2027: Alƙawurran da Sheikh Pantami Ya Dauka a tsakiyar Dandazon Mutane a Gombe

2027: Alƙawurran da Sheikh Pantami Ya Dauka a tsakiyar Dandazon Mutane a Gombe

  • Dan takarar gwamnan Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi alkawarin yaki da talauci da samar da ayyukan yi idan aka zabe shi a 2027
  • Tsohon Ministan sadarwa ya ce zai tallafa wa matasa, mata, manoma, ’yan kasuwa da ’yan kwangilar cikin gida
  • Sheikh Pantami ya yi alkawarin kare dukiyar jihar Gombe daga almundahana da almubazzaranci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - 'Dan takarar gwamnan Jihar Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi alkawarin yaki da talauci, samar da ayyukan yi da tallafa wa matasa, mata, manoma, ’yan kasuwa da ’yan kwangilar cikin gida idan aka zabe shi a 2027.

Pantami ya yi wannan alkawari ne a ranar Laraba, jim kadan bayan karbar tutar takarar gwamna ta PDP daga hannun shugaban jam'iyyar na kasa, Abdurrahman Muhammad.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ke sa mata a mota ya masu bidiyo tsirara

Pantami.
Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami tare da dumbin al'umma da suka tarbe shi Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa aln mika tutar ne a wani gangami da aka gudanar a Gombe domin gabatar da shi a hukumance a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben gwamna mai zuwa.

Jawabin Pantami ga mutanen Gombe

Da yake jawabi ga magoya bayan PDP da masu ruwa da tsaki, Pantami ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga jin dadin al'ummar jihar, musamman ta fuskar samar da ayyukan yi, karfafa tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a.

"Insha Allah, za mu yunwa da izinin Allah, za mu yaki talauci, mu samar da ayyukan yi, sannan mu tallafa wa matasa da iyaye mata," in ji shi.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani ya kuma yi alkawarin bude hanyoyin samun ci gaban tattalin arziki ga manoma, ’yan kasuwa da ’yan kwangila.

Ya ce gwamnatinsa za ta ba ’yan kwangilar cikin gida ayyukan kwangila tare da tallafa wa harkokin kasuwanci domin su bunkasa.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya saka ranar shiga Gombe don fara kamfen da gaske

Ya bayyana cewa muradun al'ummar Gombe ne za su jagoranci manufofin gwamnatinsa, inda ya ce manoma za su samu tallafin gwamnati, yayin da za a taimaka wa ’yan kasuwa wajen fadada kasuwancinsu.

Ya yi alkawarin kare dukiyar Gombe

Pantami ya kuma yi alkawarin kare dukiyar al'umma daga almubazzaranci da rashin kyakkyawan tafiyar da ita, yana mai jaddada cewa arzikin jihar ya kamata ya amfani al'ummarta baki daya, ba wasu tsiraru masu gata kadai ba.

"Arzikin Gombe ba ganima ba ne. Dukiyar Gombe ta al'ummar Jihar Gombe ce. Ba za a yi almubazzaranci da ita ba," in ji shi.

Ya kara da cewa ya kamata a rika tafiyar da dukiyar jihar cikin gaskiya da rikon amana, tare da amfani da ita wajen inganta rayuwar al'ummar jihar.

Pantami.
Dan takarar gwamnan jihar Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

PDP ta kori jiga-jigai a Gombe

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta kori manyan jiga-jiganta biyu a jihar Gombe, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki da Hon. Usman Aliyu Garry.

Ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan sakamakon binciken kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar da kuma nazarin rahoton da hukumomin da abin ya shafa na jam'iyyar suka yi.

Sanarwar ta bayyana cewa laifukan da ake zargin mutanen biyu da aikatawa sun faɗa ƙarƙashin sashe na 58(1)(a), (b), (h) da (j) na kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017 da aka yi wa kwaskwarima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262