Dan Takarar Wike Kingsley Chinda, Ya Zama Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Dokoki Ta 10

Dan Takarar Wike Kingsley Chinda, Ya Zama Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Dokoki Ta 10

  • A ranar Talata, 4 ga watan Yuli ne aka gabatar da sabbin naɗe-naɗe na shugabanni daban-daban na Majalisar Dokoki ta 10
  • Shugaban Majalisar Dokokin, Tajuddeen Abbas ne ya jagoranci zaman bayan shafe makonni uku suna hutu
  • Honarabul Kingsley Chinda, ɗan majalisa daga jihar Ribas, kuma wanda Nyesom Wike ke goyon baya ne ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Honarabul Kingsley Chinda, wanda shi ne ɗan takarar da tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike ke goyon baya, ya zama shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dokoki ta 10.

Kingsley Chinda ɗan majalisa ne a jam’iyyar PDP daga jihar Ribas, da ke wakiltar mazabar Obio/Akpor a Majalisar Dokoki ta ƙasa.

Dan takarar Wike, Kingsley Chinda ya zama shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dokoki
KIngsley Chinda, dan majalisar da Wike ke goyawa baya ya zama shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dokoki. Hoto: Marvin Chinda (Mr Civil)/ Journalist KC
Asali: Facebook

Rashin jituwar Wike da shugabannin PDP da Atiku

Wike dai ya kasance ya raba gari da shugabancin jam’iyyar PDP bayan ya rasa tikitin takarar shugaban ƙasa a shekarar da ta gabata da ya yi ga Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Masu Rinjaye Bamidele

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun daga wannan lokacin ne Wike ya fara adawa da duk wani tsari, ko wani ɗan takarar da uwar jam'iyyar wato PDP, ko Atiku Abubakar suka zo da shi.

A ranar Talata ne kakakin Majalisar Dokoki, Honarabul Tajudeen Abbas, ya bayyana sabbin shugabanni na Majalisar Dokokin ta 10, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Abbas ya bayyana Julius Ihonvbere, ɗan majalisa da ke wakiltar Owan ta Gabas da Owan ta Yamma da ke jihar Edo, a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Haka nan ma ya bayyana Abdullahi Ibrahim Halims, wanda ɗan majalisa ne da ke wakiltar mazaɓun Ankpa/Omala/Olamaboro da ke jihar Kogi, a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.

Kakakin majalisar ya kuma bayyana Usman Bello Kumo, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Akko da ke jihar Gombe, a matsayin mai tsawatarwa na majalisar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sunayen Sabbin Jagororin Majalisar Wakilan Tarayya Ta 10

Sannan an sanar da Adewunmi Oriyomi Onanuga, ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓun Ikenne/Sagamu/ da Remo ta arewa a jihar Ogun, a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.

'Yan jam'iyyar NNPP da na Labour sun samu kujeru a Majalisar Dokoki ta 10

Tajuddeen Abbas bai tsaya a iya APC da PDP ba, ya garzaya har jam'iyyar NNPP, inda ya bayyana Ali Madakin Gini, wanda ke wakiltar mazaɓar Dala jihar Kano, a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Hakan nan an bayyana sunan Ali Isa na PDP matsayin mai tsawatarwa na marasa rinjaye; yayin da aka sanar da George Ebizimawo na jam’iyyar Labour a matsayin mataimakin mai tsawatarwa na marasa rinjaye.

Daga ƙarshe, Tajuddeen Abbas ya yi addu’ar Allah ya bai wa dukkan shugabannin hikima da ikon riƙe ragamar shugabancin nasu a zauren majalisar.

An samu ɓaraka a APC biyo bayan sanar da sabbin shugabannin majalisun tarayya

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan barranta da jam'iyya mai mulki, wato APC ta yi da sabbin shugabannin Majalisar Dattawa da aka sanar ranar Talata, 4 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu yayin ganawarsa da gwamnonin jam'iyyar, ya bayyana cewa babu hannu APC cikin sabbin shugabannin da aka sanar ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel