INEC Ta Yi Matsaya kan Hukuncin Kotu da Ya Rusa Takarar Atiku a 2027

INEC Ta Yi Matsaya kan Hukuncin Kotu da Ya Rusa Takarar Atiku a 2027

  • INEC ta ce ba za ta ɗauki mataki kan rikicin shugabancin ADC ba har sai ta karɓi kwafin hukuncin kotun da aka tantance
  • Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna, ya ce sashen shari’ar hukumar zai nazarci hukuncin tare da ba da shawarar matakin da ya dace
  • ADC ta ƙi amincewa da hukuncin kotu, ta ɗaukaka ƙara tare da neman dakatar da aiwatar da shi har sai an yanke hukunci kan ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce tana jiran samun sahihin kwafin hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC, kafin ta yanke shawarar matakin da za ta ɗauka.

Hukumar ta bayyana cewa sashen shari’arta zai nazarci hukuncin tare da ba ta shawarar matakan da suka dace bayan ta karɓi takardar.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Kotu ta yi hukunci kan takardar murabus din Nafiu Bala daga ADC

INEC ta yi magana kan hukuncin rusa takarar Atiku
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce kwamishinan INEC na ƙasa, kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe da yaɗa bayanai na hukumar, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026.

Ya yi magana ne yayin wani taron tattaunawa ta yanar gizo da gidauniyar PUNCH Media Foundation ta shirya.

Dalilin da ya sa INEC ba ta ɗauki mataki ba

Haruna ya bayyana cewa INEC ba za ta iya ɗaukar mataki kan hukuncin ba tare da ta fara samun sahihin kwafinsa tare da nazarinsa ba.

Ya ce hukumar ta fara ƙoƙarin samo takardar, amma dole ne ta bi ƙa’idojin gudanarwa da kotu ta tanada wajen bayar da irin wannan takarda.

A kalamansa, hukumar ba za ta iya gaggawa fiye da tsarin kotu ba, amma tana yin abin da ya rataya a wuyanta domin samun takardar.

"Ba za mu iya gaggauta kotu ba, amma muna yin namu ɓangaren. Muna da cikakken sashen shari’a. Da zarar irin waɗannan hukunce-hukuncen sun fito, ma’aikatan sashen kan je kotu domin duba rajistar shari’o’i da neman samun kwafinsu. Amma kotuna ma suna da nasu matakai.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Tsohon abokin takarar Buhari ya bayyana dalilin kin karbar tayin mukamin da Tinubu ya yi masa

Kwamishinan ya ƙara da cewa samun sahihin kwafin hukuncin kotu yawanci yana ɗaukar kusan mako guda.

Yadda INEC za ta yanke shawara

Haruna ya ce da zarar hukumar ta samu takardar, sashen da ke kula da shari’o’in da aka shigar zai nazarci hukuncin, sannan ya ba wani kwamiti shawara.

Ya bayyana cewa kwamishinan INEC na ƙasa ne ke jagorantar kwamitin, wanda shi ma zai gabatar da shawarwarinsa ga hukumar domin yanke hukunci na ƙarshe.

“Da zarar mun same shi, za mu bi tsarin kwamitoci. Sashen da ke kula da shari’o’i zai nazarci hukuncin, sannan ya ba da shawara. Akwai wani kwamiti da kwamishinoni na ƙasa ke jagoranta. Su kuma za su ba hukumar shawara, daga nan hukumar za ta yanke shawarar matakin da za ta ɗauka.” In ji shi.

Ya jaddada cewa INEC ba za ta yanke wata shawara kan rikicin ba har sai ta karɓi sahihin kwafin hukuncin.

A cewarsa, “A yanzu, har sai mun karɓi sahihin kwafin hukuncin, babu wani abu da za mu iya yi a kan lamarin.”

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya sake taso Atiku a gaba duk da nasara a kotu

Yadda rikicin shugabancin ADC ya fara

Rikicin shugabancin ADC ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke ranar 5 ga Nuwamba.

Kotun ta soke shugabancin jam’iyyar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ke jagoranta.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya shigar yana ƙalubalantar fitowar shugabancin da Mark ke jagoranta.

Matakin kotun ya kuma shafi tsarin shugabancin ADC yayin da ake shirin babban zaɓen 2027, ciki har da tsarin da ya shafi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Sai dai ADC ta ƙi amincewa da hukuncin, inda ta ɗaukaka ƙara tare da neman kotu ta dakatar da aiwatar da shi.

Jam’iyyar ta nemi hakan ne domin hana INEC ɗaukar wasu matakai sakamakon hukuncin har sai an kammala sauraron ƙarar da ta shigar.

Abin da INEC ta ce kan takarar Atiku
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

INEC ta shigar da korafi gaban kotu

Kara karanta wannan

Kurunkus: Matakin da INEC za ta dauka kan rusa takarar Atiku a 2027

A wani labarin kuma, kun​ ji cewa hukumar INEC, ƙarƙashin shugabanta, Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ta shigar da ƙorafi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

INEC ta nemi soke sammacin da ya umarci hukumar ta fitar da takardun da suka shafi takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen gwamnan jihar Legas na 1999 da kuma zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng