Gwamnati Ta Kirkiro Sabuwar Hukuma da Nufin Share Hawayen Al'umma a Jihar Kano

Gwamnati Ta Kirkiro Sabuwar Hukuma da Nufin Share Hawayen Al'umma a Jihar Kano

  • Gwamnatin Kano ta kafa hukumar KASSTOWA domin inganta samar da ruwan sha a yankunan karkara da kananan birane
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Injiniya Sani Bala Danbatta a matsayin mukaddashin shugaban hukumar
  • Kwamishinan albarkatun ruwa ya ce za a hanzarta ayyukan samar da ruwan sha a fadin jihar Kano domin share hawayen jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kano ta kafa sabuwar hukuma domin karfafa samar da ruwa da inganta hanyoyin samun tsaftataccen ruwan sha a kananan birane da yankunan karkara a fadin jihar.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabur Yusuf a fadar gwamnatinsa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamnatin Kano ta kafa sabuwar hukuma

Leadership ta rahoto cewa Hashim ya sanar da hakan ne bayan kaddamar da Hukumar Samar da Ruwa a Kananan Garuruwa ta Jihar Kano (KASSTOWA), wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kafawa.

Kara karanta wannan

Bayan faɗuwar ɗanyen mai a duniya, FCCPC ta waiwayo kan farashin fetur a Najeriya

Hashim ya bayyana cewa an nada Injiniya Sani Bala Danbatta a matsayin mukaddashin shugaban hukumar, yayin da aka nada Aminu Mamman Yaro a matsayin mukaddashin mataimakinsa, tare da wasu daraktoci.

Ya ce an kafa hukumar ne domin inganta samar da ruwan sha a al'ummomin da ba sa samun isasshen ruwa, ta hanyar inganta yadda ake tafiyar da tsare-tsaren samar da ruwa na shiyyoyi.

Aikin da aka dora wa hukumar

A cewar kwamishinan, an umarci sabuwar tawagar gudanarwar hukumar da ta gaggauta aiwatar da ayyukan da ake kai tare da ci gaba da ayyukan samar da ruwa domin inganta samun tsaftataccen ruwan sha.

"An kafa hukumar ne domin karfafa ayyukan samar da ruwa a kananan birane da yankunan karkara ta hanyar ingantaccen tafiyar da tsare-tsaren samar da ruwa na shiyyoyi.
"Na umurci sabuwar tawagar gudanarwa da ta gaggauta ayyukan da aka fara tare da tabbatar da ci gaba da ayyukan samar da ruwa a shiyyoyin Kano," in ji shi.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027: Gwamna Radda ya runtuma kora a gwamnatinsa

An samar da motocin aiki ga hukumar

Hashim ya kuma bayyana cewa an mika wa hukumar sababbin motocin aiki masu tambari domin saukaka gudanar da ayyukanta da kuma inganta zirga-zirgar ma'aikatanta yayin gudanar da ayyukan da suka shafi kai ziyara a wurare daban-daban.

Ya sake jaddada kudirin gwamnatin Abba Gida-gida na farfado da bangaren samar da ruwa, fadada kayayyakin more rayuwa da ake amfani da su wajen samar da ruwa, da kuma tabbatar da cewa al'ummar Kano sun samu tsaftataccen ruwan sha.

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf yana jawabi a taron Majalisar zartarwa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Kwamishinan ya ce:

"A karkashin jagoranci! mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, babban abin da muka sa a gaba shi ne farfado da bangaren samar da ruwa, fadada kayayyakin more rayuwar samar da ruwa da tabbatar da adalci wajen bai wa al'ummar Jihar Kano damar samun tsaftataccen ruwa."

Gwamna Abba ya fara raba tallafin N50,000

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin tallafin N50,000 duk wata ga mata 5,200 a faɗin Jihar Kano.

Gwamna Abba ya buƙaci waɗanda za su amfana su yi amfani da kuɗin wajen kafa sana’o’i da faɗaɗa kasuwancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262