Tinubu Ya Yi Magana da Ɗansa Seyi Ya Samu Babbar Sarauta a Kebbi

Tinubu Ya Yi Magana da Ɗansa Seyi Ya Samu Babbar Sarauta a Kebbi

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya ɗansa Seyi murnar samun sarautar Dan Zaki Gwandu daga hannun Sarkin Gwandu a jihar Kebbi
  • Sarkin Gwandu ya naɗa Seyi Tinubu sarautar ne a fadarsa da ke Birnin Kebbi ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026
  • Tinubu ya bukaci ɗansa da ya yi amfani da sarautar wajen ƙara himma kan ayyukan jinƙai, haɗin kai da ci gaban matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya ɗansa, Seyi Tinubu, murnar samun sarautar gargajiya ta Dan Zaki Gwandu da Sarkin Gwandu da ke jihar Kebbi ya naɗa masa.

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashar ne ya ba Seyi sarautar a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a wani biki da aka gudanar a tsohuwar fadar Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

"An ci amanata"; Tsohon gwamna ya koka bayan gama wahala da PDP

An ba Seyi Tinubu babbar sarauta a Kebbi
Shugaba Bola Tinubu da ɗansa Seyi Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Kebbi Radio.
Source: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa wannan shi ne karon farko da masarautar ta ba wani mutum irin wannan sarauta a tarihinta, cewar Punch.

Abin da Tinubu ya ce kan sarautar ɗansa

Shugaba Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda wata masarauta mai daɗaɗɗen tarihi ta karrama ɗansa, inda ya kuma gode wa Sarkin Gwandu da majalisar masarautarsa bisa wannan karamci.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce sarautar ta wuce matsayin karramawa ga mutum guda.

Ya bayyana cewa hakan na nuna irin kyakkyawar alaƙa, mutunta juna da haɗin kan da ke tsakanin al'ummomi daban-daban a Najeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ƙoƙarin Seyi wajen tallafa wa matasa, bunƙasa al'umma da ƙarfafa musu gwiwa ta hanyar ƙungiyar City Boy Movement da sauran shirye-shiryensa.

Tinubu ya ce:

"A matsayina na uba, ina farin cikin ganin ɗana ya samu karramawa daga wata cibiyar gargajiya mai irin wannan tarihi mai daraja.

Kara karanta wannan

Sarakunan Yarbawa a jihohin Arewa 19 sun dauki babban alkawari ga Tinubu

"Amma ina kuma tunatar da shi cewa duk wata karramawa tana zuwa da nauyi. Sarautar Dan Zaki Gwandu tana ɗauke da darajojin jarumtaka, jagoranci da hidimtawa al'umma. Ina kira gare shi da ya yi aiki da waɗannan ƙa'idoji, ya kasance mai tawali'u tare da ci gaba da sadaukar da kansa wajen kyautata rayuwar jama'a."

Shawarar da Tinubu ya ba ɗansa

Shugaban ƙasar ya shawarci Seyi da kada ya ɗauki sabuwar sarautar a matsayin abin alfahari kawai, sai dai ya mayar da ita wata dama ta ƙara jajircewa wajen taimakon matasa da samar da zaman lafiya.

Ya kuma bayyana cewa sarakunan gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen kare tarihi, al'adu da haɗin kan ƙasa.

Tinubu ya yi wa ɗansa fatan samun hikima, tawali'u da ƙarfin hali wajen sauke nauyin da ke tattare da sabuwar sarautar.

An ba yar Tinubu sarauta

An ji cewa Sarkin Daura ya karrama Folashade Tinubu-Ojo, ’yar Shugaba Tinubu, saboda gudunmawarta wajen ci gaban al’umma da mata baki daya.

Sarkin Daura ya kuma nada Minista Hannatu Musa Musawa sarautar Mairamar Kasar Hausa, yayin bikin Hawan Magajiya da aka gudanar a fadar masarautar.

Bikin ya samu halartar Gwamna Dikko Umaru Radda da manyan jami’an gwamnati, sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya daban-daban daga sassa daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.