Shugaban APC Ya Zazzagi Wike, Ya Kira Ministan Tinubu da Barazana ga Dimokuradiyya

Shugaban APC Ya Zazzagi Wike, Ya Kira Ministan Tinubu da Barazana ga Dimokuradiyya

  • Shugaban APC na jihar Imo ya fada wa Nyesom Wike ya daina rara gefe tsakanin jam’iyyu siyasa biyu
  • Cif Austin Onyedebelu ya ce dokar zabe ba ta hallata wa mutum zama ‘dan APC da PDP lokaci daya ba
  • ‘Dan siyasar ya kuma zargi Wike da kirkiro ‘Rainbow Coalition’ saboda manufarsa ta zama shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - Shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Imo, Austin Onyedebelu, ya soki Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

A makon jiya ne aka ji Cif Austin Onyedebelu ya siffanta Nyesom Wike, a matsayin babbar barazana ga tsarin dimokuradiyya Najeriya.

Bola Tinubu da Nyesom Wike
Shugaban kasa Bola Tinubu da Ministan Abuja Nyesom Wike a Aso Rock Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

APC a Imo ta soki Nyesom Wike

Austin Onyedebelu ya jaddada cewa ministan ba zai yiwu ya kasance cikin jam’iyyu biyu lokaci guda ba, a cewar wani rahoton Leadership.

Shugaban na jam’iyya mai mulki ya soki yadda Nyesom Wike yake tare da PDP kuma yake goyon bayan takar jam'iyyar APC a sama.

Kara karanta wannan

Rigima ta kara zafi: Gwamna Dauda ya tura zazzafan sako ga Wike

‘Dan siyasar ya shawarci Nyesom Wike da ya zabi jam’iyya guda, ya daina raba kafa a siyasa a lokacin da ake shirin babban zabe.

Shugaban jam'iyyar na Jihar Imo ya bayyana hakan ne yayin da yake zanta wa da manema labarai a karshen makon da ya gabata.

Wike ba zai iya zama a APC da PDP

Onyedebelu ya bayyana cewa dokar zabe ta kasa ba ta tanadi cewa mutum zai zama dan jam'iyyu biyu dabam-dabam a lokaci guda ba.

Ya fada wa ‘yan jarida cewa idan har Wike yana son yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aiki, to ya dace ya shigo cikinsu a jam'iyyar APC.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto shi yana rokon tsohon gwamnan na Rivers ya sauya-sheka.

A cewarsa, mutum ba zai iya tsayawa a tsakiyar hanya biyu yana da'awar tafiya guda daya ba, da yake bayani a kan matsayar Mista Wike.

Amfani da 'Rainbow Coalition' domin farfado da PDP

Shugaban jam'iyyar ta APC ya zargi Wike da yin amfani da gamayyarsa ta 'Rainbow Coalition' domin busa wa jam'iyyar PDP rai saboda 2031.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya jero gwamnonin jam'iyyar APC 3 da suka huro masa wutar adawa

Jam’iyyar PDP ta yi rauni musamman bayan ficewar manyan 'yan siyasa irinsu Alhaji Atiku Abubakar a shekarar bara zuwa ADC mai adawa.

Onyedebelu ya zargi ministan Abuja da amfani da gangaminsa na hadin gambizar ‘yan siyasa saboda burin sa na mulkar Najeriya.

Shugaban na APC a Imo ya jaddada matsayar gwamnonin APC dangane da wannan tafiya.

Ya ce maimakon Wike ya karbi shawarar, sai ya koma sukar shugabannin APC, musamman shugaban gwamoninta, Hope Uzodimma.

Wike.
Ministan Abuja Nyesom Wike bayan ruwa ya yi gyara a Maitaima Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Gwamnan LP yana tare da APC a sama

A baya an karanta labari cewa Gwamna Alex Otti ya goyi bayan Gwamnatin Bola Tinubu tazarce a kan karagar mulki a shekarar 2023.

Mai girma gwamnan ya dauki wannan ra’ayi ne saboda kujerar da yake kai a NEC da kuma tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta kawo.

LP tana da ‘dan takara kuma akwai masu ganin shaharar Peter Obi ta taimaki Otti a 2023 amma shi gwamnan ya nuna duk babu ruwansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng