Tinubu Ya Kwantar da Hankulan 'Yan Najeriya, Ya Fadi Shirinsa kan Kawo Karshen Rashin Tsaro

Tinubu Ya Kwantar da Hankulan 'Yan Najeriya, Ya Fadi Shirinsa kan Kawo Karshen Rashin Tsaro

  • Tinubu ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru domin shawo kan matsalolin tsaro, tare da ƙarfafa rundunar ’yan sanda da sojojin ƙasa
  • Shugaban ƙasar ya bukaci ’yan Najeriya su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar kai rahoton motsin da ake zargi a yankunansu
  • Ya kuma yi alkawarin rage farashin abinci da bunƙasa noma ta hanyar amfani da injinan zamani wajen aikin gona

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya idan aka sake zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tinubu ya sake daukarwa 'yan Najeriya alkawarin da ya gaza cikawa

Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Najeriya
Mai girma Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wane alkawari Tinubu ya yi kan rashin tsaro?

Shugaban ƙasar ya amince cewa har yanzu Najeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro, amma ya buƙaci ’yan ƙasa su taimaka wa jami’an tsaro wajen kare al’ummominsu, cewar rahoton tashar TheCable.

Ya bukaci jama’a su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko aikin da suke zargi a yankunansu, domin hakan zai taimaka wa hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

“Ina tabbatar muku cewa muna aiki tukuru domin ganin Najeriya ta kasance cikin aminci, kuma ana kula da jami’an tsaronmu yadda ya kamata, ba tare da la’akari da inda suka fito ba.
“Za mu yi nasara kan rashin tsaro. Mun fuskanci yaƙe-yaƙe da dama. Za mu kayar da maƙiyanmu; maƙiyan haɗin kan ƙasa, maƙiyan zaman lafiya da kwanciyar hankali, da maƙiyan fata. Ina tabbatar muku cewa muna aiki kan hakan.
“Muna ƙarfafa rundunar ’yan sanda da sojojin ƙasa. A yanzu muna biyan su albashi mafi kyau.” In ji shi.

Kara karanta wannan

"Karya suke yi": Tinubu ya sake magana kan dawo da tallafin man fetur

Ya gabatar da kundin manufofin APC

A yayin gangamin, Tinubu ya gabatar da kundin manufofin yaƙin neman zaɓen APC mai taken “From Reforms to Prosperity”, wato daga sauye-sauyen tattalin arziki zuwa wadata.

Kundin ya ƙunshi bayanan abubuwan da gwamnatinsa ta ce ta cimma, da kuma shirye-shiryenta a fannonin gine-ginen ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma da tsaro.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa kundin zai zama jagora wajen ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki, faɗaɗa damar samun ci gaba da kuma samar da wadata ga al’umma baki ɗaya, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Ya yi alƙawarin kammala shirye-shirye da ayyukan da aka fara, yana mai cewa manufofin gwamnatinsa sun fara haifar da sakamako a sassa daban-daban na ƙasar.

Tinubu ya yi alƙawarin rage farashin abinci

Shugaban ƙasar ya kuma yi alƙawarin rage farashin kayan abinci tare da ƙara yawan amfanin gona, musamman ta hanyar bunƙasa noman zamani da amfani da injina.

Ya ce Jihar Jigawa da sauran jihohin Najeriya suna da filayen noma masu yawa da za a iya amfani da su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shettima ya yi wa Atiku shagube a wurin kamfen

A cewarsa, inganta amfani da waɗannan filaye zai taimaka wajen ƙara yawan abincin da ake nomawa, tabbatar da wadatar abinci a ƙasar da kuma bunƙasa tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da take ganin za su inganta rayuwar ’yan Najeriya, idan ta samu damar ci gaba da mulki bayan zaɓen 2027.

Tinubu ya ce zai magance rashin tsaro
Kashim Shettima, Bola Tinubu tare da matansu a wajen yakin neman zaben APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sakon Tinubu ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ƙalubalanci ’yan Najeriya da su yi wa gwamnatinsa hukunci​ bisa tarihin ayyukanta da abubuwan da ta cimma, maimakon alkawuran siyasa.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta wuce matakin furucin siyasa, inda ta kafa tsarin kariya na doka ga ma’aikatan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng