Pantami, Tsohon IGP Adamu, da Wasu na Fuskantar Rashin Tabbas kan Takara

Pantami, Tsohon IGP Adamu, da Wasu na Fuskantar Rashin Tabbas kan Takara

  • Hukuncin Kotun Ƙoli kan wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 ya jefa takarar wasu ’yan siyasa cikin sabon yanayin rashin tabbas
  • Kotun ta tabbatar da ingancin sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2), wadanda suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu da yadda ake tantance ’yan takara
  • Wasu daga cikin wadanda ake alakanta lamarin da su sun hada da Kingsley Chinda, tsohon IGP Mohammed Abubakar Adamu da Farfesa Isa Ali Pantami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Yayin da shirye-shiryen zaben 2027 ke kara yin nisa, wani sabon hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke kan Dokar Zaɓe ta 2026 ya haifar da ce-ce-ku-ce kan makomar wasu ’yan takara.

Kotun Ƙoli ta ranar Alhamis ta amince da daukaka karar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shigar kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya soke wasu tanade-tanaden dokar.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda manyan Najeriya da iyalansu 61 suka saye kadarorin $270m a Amurka

Shehu Buba, Sheikh Pantami da IGP Adamu
Sanata Shehu Buba a tsakiyar Sheikh Isa Ali Pantami da IGP Adamu mai ritaya. Hoto: Abba Sani Pantami|Mujaddadi TV|Mohammed Abubakar Adamu
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa kotun ta dawo da sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na dokar, tana mai cewa ba su saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ba.

Abin da hukuncin kotu ya kunsa

Sashe na 77(5), 77(6) da 77(7) sun shafi rajistar mambobin jam’iyyun siyasa da ake gabatarwa ga INEC, yayin da sashe na 84(2) ya tanadi gudanar da zaben fidda gwani ta hanyar kuri’ar kai tsaye ko yarjejeniya.

Kotun Ƙoli ta kuma soke hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 16 ga Yuli, 2026, tare da dawo da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta yi watsi da karar ZLP.

A wasu shari’o’in biyu, Kotun Ƙoli ta yi watsi da karar da jam’iyyar SDP ta shigar, yayin da ta yi watsi da karar YP saboda an shigar da ita bayan wa’adin da doka ta kayyade.

Makomar IGP Adamu da Chinda

A Jihar Nasarawa, magoya bayan tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, sun musanta cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya kawo cikas ga burinsa na neman kujerar gwamna.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira

Daily Trust ta wallafa cewa Adamu ya koma jam’iyyar SDP bayan ya shiga zaben fidda gwani na APC, lamarin da ya sa wasu magoya bayan APC suka fara murnar cewa ba zai samu damar bayyana a takardar zabe ba.

Sai dai kakakinsa, Otaru Douglas, ya ce babu dalilin fargaba, yana mai cewa ana fassara hukuncin ne ba daidai ba.

A Rivers, an kuma fara alakanta hukuncin da takarar Kingsley Chinda na APC da Awaji-Inombek Dagomie Abiante na NDC.

Chinda ya lashe zaben fidda gwani na APC na gwamnan Rivers a ranar 21 ga Mayu, 2026, bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya janye daga takarar.

Sai dai tambayoyin sun taso kan lokacin da Chinda ya shiga APC da kuma ko an saka sunansa cikin rajistar mambobin jam’iyyar kafin zaben fidda gwanin.

Pantami: PDP na nazari

A Gombe kuwa, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya cancanci sake neman tikitin jam’iyyar na gwamna.

Sakataren yada labarai na PDP a Gombe, Abdulkadir Ahmed Dukku, ya ce an tantance ’yan takarar uku ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 26 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: An maka INEC kara kotu kan zaben 2027

Wasu na ganin hukuncin zai shafi takarar Pantami saboda ya shiga PDP bayan wa'adin da aka sanya ya kare, yayin da wasu ke ganin ya tsallake siradi.

Bayanin Sanata Shehu Buba

Dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a Bauchi, Sanata Shehu Buba Umar, ya yi watsi da rahotannin cewa hukuncin Kotun Ƙoli zai iya shafar cancantarsa ta neman takara a 2027.

Ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Sabo Mohammed, Sanata Buba ya ce ya bi dukkan tanade-tanaden dokar zabe da suka dace da shi.

Zaben Anambra a Najeriya
Masu kada kuri'a a filin zaben da aka yi a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya ce matsayin doka da hukuncin Kotun Ƙoli suka tabbatar, tare da ikon INEC na fitar da ka’idojin tsarin zaben 2027, sun fara aiki ne daga ranar 24 ga Satumba, 2026.

Bayanin PDP da ADC a Kwara

A Kwara, sunayen Sanata Saliu Mustapha, Kolo Jiya da Saheed Popoola na daga cikin wadanda ake tattauna makomarsu bayan hukuncin Kotun Ƙoli.

Sakataren yada labarai na PDP a jihar, Olusegun Olushola Adewara, ya ce jam’iyyar ba ta da alaka da karar da aka shigar kan INEC, kuma ba ta kalubalantar jerin ’yan takararta da hukumar ta wallafa.

Kara karanta wannan

An saki sunayen jami'an NSCDC 20 da aka dakatar kan mutuwar mutum 37 a Neja

Ya ce INEC ta riga ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar PDP, wanda yake a bude domin jama’a su duba.

Adewara ya kuma ce ikon tsayar da ’yan takara na hannun jam’iyyun siyasa ne, matukar sun bi Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe.

PDP za ta yi zabe a Gombe

A wani labarin kun ji cewa Kotun Tarayya ta soke zaben fitar da dan takarar gwamna na PDP da aka yi a baya a Jihar Gombe, inda ta ba da umarnin sake gudanar da shi.

Jam'iyyar PDP ta tantance Farfesa Isa Ali Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki, da Usman Aliyu Garry domin fafatawa a sabon zaben.

Rahotanni sun nuna cewa an kayyade ranar Talarata, 29 ga watan Satumba, 2026, domin gudanar da sake zaben a dukkan mazabun jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng