Auren Bogi Ya Jawo wa Wani Mutum Matsala a Jihar Kano, Hisbah Ta Cafke Shi
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Sunusi Sabi’u Zakariyya bisa zargin aurar da budurwa Zainab ba tare da bin ka’ida ba
- Budurwar ta ce ta baro Birnin Kebbi zuwa Kano ne bayan mahaifinta ya shirya tilasta mata auren wani mutum
- Wanda ake zargin ya ce ya nemi wasu mutane ta hannun abokinsa domin su zama waliyyan auren, inda aka daura shi da sadaki naira 70,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani matashi bisa zargin kulla aure ta hanyar da bai dace ba lamarin da ya jawo maganganu a jihar.
An cafke matashin ne mai suna mai suna Sunusi Sabi’u Zakariyya da ya auri budurwar da ake kira Zainab bayan ta tsere daga Kebbi zuwa jihar Kano.

Kara karanta wannan
"Na ƙara gane rayuwa," Sanata ya ɗauko muhimman darussa a zaman da ya yi a gidan yari

Source: Facebook
An cafke wani da ya yi auren bogi
Kwamandan Hisbah na karamar hukumar Kano Municipal, Malam Hamidan Tanko Alasaka, ne ya bayyana kamen yayin da yake bayani kan binciken da hukumar ta gudanar game da lamarin, cewar Daily Trust.
A cewar rahotanni, Zainab ta shaida wa masu bincike cewa ta baro Birnin Kebbi ne bayan samun labarin cewa mahaifinta na shirin tilasta mata yin auren da ba ta so.
Ta bayyana cewa ta fara sanin Sunusi ne ta hanyar tattaunawa ta waya bayan ta gudu daga gidan iyayenta.
Yadda aka gudanar da auren a Kano
A nasa bayanin, Sunusi ya ce Zainab ta shafe kusan watanni biyu tana zaune a gidan yayarsa, amma iyayenta ba su yi wani kokari na gano inda take ba.
Matashin, wanda rahoton ya bayyana cewa yana da aure, ya ce ya tuntubi wasu mutane ta hannun wani abokinsa domin su wakilce shi a matsayin waliyyan auren.
Ya bayyana cewa an gudanar da daurin auren ne tare da sanya sadaki Naira 70,000 wanda hukumar ta ce ya saba ka'ida duba da sharudan da ake da su kafin daurin aure.
Hukumar Hisbah ta fara bincike kan lamarin
Kwamandan hukumar Hisbah ya ce hukumar ta fara samun bayanin lamarin ne bayan wasu mazauna yankin sun kai rahoton cewa an gudanar da auren a cikin wani shago.
Ya ce jami’an hukumar sun kama mutanen da ake zargi da hannu a lamarin domin gudanar da bincike.
A cewarsa, bayan kammala binciken farko, hukumar za ta mika wadanda aka kama zuwa hedikwatarta domin daukar matakin da ya dace.
An hana mata talla a Katsina
A wani labarin, mun ba ku labarin cewa Hisbah ta Katsina ta kawo wata doka domin hana ’yan mata yin tallace-tallace da daddare daga karfe 10:00 na dare a fadin jihar.
Kwamandan hukumar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ya ce matakin na da nufin kare ’yan mata daga cin zarafi musamman wanda ke faruwa da dare.
Hisbah ta kuma yi gargadi kan sake bude gidajen karuwai, tallata magungunan gargajiya da kalaman batsa da sauran wurare da ake aikta badala.
Asali: Legit.ng
