Abba Ya Ba Ilmin Kano Muhimmanci a 2027 a Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 1.1

Abba Ya Ba Ilmin Kano Muhimmanci a 2027 a Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 1.1

  • Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin jihar Kano na shekarar 2027, ya ware 63% ga ayyukan raya kasa
  • Naira biliyan 413.55 (37%) na kasafin kudin badin ne kawai zai tafi ga kudin da ake kashewa a harkokin yau da kullum
  • Gwamnan Kano ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta cimma sama da 90% na manufofin da ta tsara za ta yi a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika wa Majalisar dokoki kundin kasafin kudi na shekarar 2027 da za a shiga.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya kai kasafin kudin gaban ‘yan majalisa su duba ana saura wata daya da rabi shekarar nan ta kare.

Abba.
Abba Kabir Yusuf a Majalisar dokokin jihar Kano Hoto: @babarh
Source: Twitter

Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin N1.1tr

Labarin da aka samu daga shafin VON ya ce bangaren ilmi ya fi kowane samun kaso a kasafin kudin domin an ware masa 28% a 2027.

Kara karanta wannan

'Maganar yunwa fa ruruta ta ake yi': Jigon APC ya magantu kan halin kunci

A kasafin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar an fahimci gwamnatinsa za ta cigaba da ba ilmi da makarantu muhimmanci sosai.

Gwamnan ya fada wa majalisa za iyi kokari wajen inganta rayuwar al’umma a shekarar da za a shiga.

Ya ce:

“Kasafin kudin zai kara karfafa nasarorin da aka samu a bangaren ilimi, tare da ci gaba da sauye-sauyen da ake yi domin inganta sakamakon karatun dalibai a faɗin jihar.”

Nasarorin da Abba ya samu a jihar Kano

Da yake magana a majalisa, gwamnan ya jero nasarorin da gwamnatinsa ta samu a shekarar musamman wajen daukar malama aiki.

Ya tuna wa ‘yan Majalisar dokokin yadda ya dauki malamai 4, 900 aikin din-din sannan aka ba malamai 3, 688 a karkashin shirin BESDA.

Abba ya ce gwamnatin jihar ta biya wa dalibai fiye da 150, 000 kudin jarrabawowin NECO, NBAIS da NABTEB duk a cikin shekarar bana.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka tallafa wa Tinubu yana tafiya a wurin taro ya dauki hankali, Sowore ya yi magana

Bayan nan an rahoto shi yana cewa sun sauke nauyin bashin da yake kan makarantun kwana kuma an gyara wuraren karatun dalibai.

Gwamnan ya kara da cewa Kano ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko idan ana zancen samun nasarar a jarabawar NECO har a bana.

Yadda Abba zai kashe kudin Kanawa a 2027

Dangane da tsarin kasafin kudin baki ɗaya, gwamnan ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 693.47 da za a kashe wajen ayyukan raya kasa.

Haka zalika Naira biliyan 413.55, wato 37% kadai za su tafi wajen yin ayyukan yau da kullum.

“Ware kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin ga ayyukan raya kasa na nuna kudurin gwamnatinsa na fadada ababen more rayuwa, bunkasa kwarewar al’umma da kuma inganta zuba jari da zai iya haifar da ci gaban tattalin arziki.”

- Abba Kabir Yusuf

Vanguard ta ce gwamnatin jihar na hasashen samun biliyan 692.64 a 2027, tana cewa ta cin ma 90% na manufofin da ta tsara wa Kanawa.

Naira biliyan 142.84 zai fito daga kuɗin shiga da jihar ke samarwa (IGR), sai kuma Naira biliyan 549.80 daga asusun tarayya a kason wata-wata.

Kara karanta wannan

An ɗauki bidiyon jagoran jam'iyyar su Kwankwaso ya tuɓe kaya ya shiga kogi

Gwamna ya sha alwashin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da baitul-mali yayin da ya bar majalisa ta duba kundin kasafin.

Idan ‘yan majalisa sun gama aiki a kai, ana sa ran kasafin zai fara aiki a farkon shekarar mai zuwa.

Gwamnan Kano ya ji dadin ceto shugaban APC

An samu labarin kubutar da wani shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano da ya shafe kwanaki kusan 70 a hannun masu garkuwa da mutane.

Salisu Muhammad Kosawa ya yi amfani da Facebook ya fitar da jawabin Kwamishinan labarai bayan an ceto shugaban na APC a yankin Rogo.

Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Kano ya ce sun yi nasarar kwato Abdullahi Alasan Belo ta hanyar amfani da dabarun aiki na musamman.

Hotunan Abba yana gabatar da kasafin kudin 2027 a majalisa daga shafin hadiminsa a X, Abdullahi Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng