Tsohon Minista Ya Musanta Cewa Hukuncin Kotun Koli Ya Taba Takarar Pantami
- Solomon Dalung ya ce Kotun Koli ba ta soke takarar Isa Pantami, M. Adamu ko wani dan takara kai tsaye ba
- Dole ne a gabatar da kara kan zaben tsaida gwani cikin wa’adin kwanaki 14 da kundin tsarin mulki ya tanada
- INEC ba za ta iya soke takarar wani ɗan takara bisa fassarar hukuncin Kotun Koli kawai ba a cewar Dalung
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Solomon Dalung ya tofa albarkacin bakinsa game da hukuncin Kotun koli da ake cewa ya rusa takarar wasu ‘yan siyasa.
Kotun koli ta ba INEC gaskiya a shari’ar dokar zabe, ta haramta wa ‘yan siyasa neman takara a jam’iyyu biyu a lokaci guda.

Source: Facebook
Sharhin Solomon Dalung kan hukuncin Kotun Koli
Solomon Dalung wanda masanin shari’a ne ya yi magana a shafin Facebook, inda ya yi karin haske game da hukuncin babbar kotun.

Kara karanta wannan
Magu: Bukola Saraki ya samu abin magana da kotu ta wanke shi a sabaninsa da Buhari
Wasu suna ganin Isa Ali Pantami, Mohammed Abubakar Adamu da Kingsley Chinda ba su iya takara ba bayan nasarar INEC a kotu.
Solomon Dalung ya bukaci mutane su kwantar da hankalinsu, ba dole hukuncin na nufin ‘yan siyasar sun rasa damar zama gwamnoni.
"Kotun koli ta tabbatar da ingancin wasu sassan dokar zabe, tabbas.
"Amma Kotun kolin ba ta yi zama a game da Pantami, Adamu ko wasu daidaikun ‘yan takara ba. Ba ta ayyana sunayensu cewa an cire su daga takara ba.
"Ba ta yi hukunci game da lamarin zaben tsaida gwanin jam’iyyu, rajistar ‘ya ‘yansu ko tsaida ‘yan takara."
- Solomon Dalung
Tsohon ministan ya cigaba da cewa ayyana doka dabam, sannan kuma amfani da ita a kan wani mai neman takara a zabe abu ne dabam.
Dalung ya ce a wannan gaba ne yake ganin akwai kuskure a fassarar da wasu suke yi.

Kara karanta wannan
Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba
Ya ce:
"INEC ba kotu ba ce. INEC kawai ba za ta iya karanto hukuncin Kotun koli sai ta fara soke takarar wasu ita kadai ba."
‘Dan siyasar ya jefa wa masu wadannan maganganu tambayoyi na ilmin shari’a.
Wane ne yake da hurumin kalubalantar wata takara?
Ina aka shigar da kara kafin shiga zabe?
An shigar da karar a lokacin da aka ware
- In ji tsohon ministan

Source: Facebook
Inda Pantami zai iya tsallakewa
A rubutun, ya kawo batun sashe na 285(9) na kundin tsarin mulki wanda ya ce dole a shigar da karar shiga takara cikin kwanaki 14.
Yake cewa kotu ta ba wasa da wannan wa’adi, babban ‘dan siyasar ya ce alkalai ba za su karbi karar da aka kai a wajen lokacin ba.
Ko da su Pantami sun canza sheka, ya ce ba za a iya hana su takara ba muddin ba a yi karar shi a kotu kafin wa’adin nan ya kure ba.
An soke zaben da ya kawo Pantami
An ji labari Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaben fitar da gwani na dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a Jihar Gombe.
Wannan hukunci ya shafi takarar Farfesa Isa Ali Pantami bayan Usman Aliyu Garry ya shigar da karan kalubalantar sahihancin zaben.
Kotun ta umarci jam'iyyar PDP da ta sake gudanar da sabon zaben tsaida gwani bisa ka'idojin jam'iyya da dokoki kuma za a yi hakan.
Asali: Legit.ng
