Baraka Ta Hargitsa Jam'iyyar NDC da Tafiyar Obi da Kwankwaso daga Fara Kamfen

Baraka Ta Hargitsa Jam'iyyar NDC da Tafiyar Obi da Kwankwaso daga Fara Kamfen

  • Kungiyar OK Movement ta ayyana nada kwamitin yakin zaben shugaban kasa ba tare da amincewar jam'iyyar NDC ba
  • Shugabannin gudanarwa na NDC sun nesanta kansu daga wannan kwamiti, yayin da OK ta ce ba ta neman amincewarsu
  • Ana ganin ‘yan Obidients da Kwankwasiyya suna makauniyar biyayya ga jagororinsu ba tare da bin wani tsarin jam’iyya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Baraka ta shiga tsakanin jam’iyyar NDC da kuma tafiyar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso wanda ta fi shahara da OK.

Daga lokacin da aka ce kungiyar OK ta fitar da sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ne aka samu sabani.

Magoya bayan OK
Wasu masoyan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a Kaduna Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rashin jituwar NDC da OK ta fito karara

Wannan ne karon farko da bangarorin biyu suka fito fili suna rigima a tsakaninsu kamar yadda Jaridar Daily Trust ta labarta yau.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a NDC kan kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso da Obi

Sakatariyar kungiyar OK a Najeriya, Saadatu Sani ta fitar da sanarwa cewa John Ughulu zai jagoranci yakin neman zaben 2027.

Dama can John Ughulu wanda shi ne shugaban kungiyar OK yana ta samun matsala da shugabannin jam’iyyar NDC na kasa.

Kungiyar magoya bayan ta dage za ta yi wa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso aikin neman zama shugaban kasa a inuwar NDC.

Shuganannin NDC sun fitar da jawabin raddi ta hannun Cleopas Moses, suna masu watsi da sanarwar nada kwamitin kamfen.

Sanata Moses wanda shi ne shugaban NDC na kasa ya ce jam’iyyar ba ta kai ga amincewa da fitar da ‘yan kwamitin yakin zabe ba.

Babu ruwan OK da sahalewar jam'iyyar NDC

Amma kungiyar OK ta zo ta bayyana cewa babu ruwanta da jam’iyyar, ba ta jiran amincewarta kafin ta fara aikin ta a zaben 2027.

Punch ta ce 'yan kungiyar magoya bayan sun bukaci a nemi afuwarsu ne saboda abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Yadda kawancen tallata Tinubu da Wike ya kafa yake neman tarwatsewa

Rahoton ya ce tun asali ana zargin ‘yan kungiyar OK ba su tafiya da jagororin jam’iyyar NDC wajen duk harkokin siyasar da suke yi.

Yayin da kungiyar ta ke cewa tana zaman kanta ne a Najeriya, ita NDC tana ganin hakan zai kawo sabani da kuma raina jam’iyya.

Su ‘yan Obidients da ‘yan Kwankwasiyya suna aikinsu gadan-gadan ne gefe guda alhali ita NDC tana aiki da tsarin shugabancin jam’iyya.

Sa-in-sar shugaban OK da jam'iyyar NDC

A lokacin da OK take ji da Darekta Janar din ta, John Ughulu, ita NDC har ta nemi a ladabta shi saboda ya saba wa ka’idojin jam’iyya.

Ughulu ya samu matsala da jam’iyyar NDC saboda rigimar zaben tsaida gwani a jihar Legas.

Manyan jam’iyyar NDC sun nemi yi wa tsarin shugabancin OK garambawul, amma ‘yan kungiyar suka yi ta yakar wannan yunkuri.

Tsohuwar rigimar shugabannin NDC da Obidients/Kwankwasiyya

Gabanin yanzu an yi ta jin rigima tsakanin su Kwankwaso da tsagin Hussaini Mai Riga da Muhammad Sabo Bakin Zuwa a Kano.

An kuma ji yadda aka yi ta kokarin zama saboda rigimar takara da Seriake Dickson wanda shi ne babban jagoran jam’iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun zo da wani tsari da zai iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027

A zaben tsaida gwani, wasu magoya bayan Obidients da Kwankwasiyya sun rasa samun takara.

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
'Yan takaran NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso gabanin taro a Kaduna Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Goyon bayan NDC ya ci kujerar hadimin Barau

Ana da labarin yadda zancen ‘Abba Must Go’ ya sa Mai ba Barau Jibrin shawara a Majalisar dattawa ya rasa kujerar da yake kai.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya tsige Umar Alhassan (King Indara), saboda adawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Barau I. Jibrin ya rabu da King Indara ganin bai tare da tazarcen Abba Kabir Yusuf. Matashin yana tallata 'dan takaran NDC a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng