Rikici Ya Danno cikin Kungiyar Goyon Bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027
- Rikicin cikin gida ya ɓarke a ƙungiyar OK Movement mai goyon bayan takarar tsohon gwamna Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso a 2027
- Bangarori daban-daban da ke ikirarin shugabancin ƙungiyar sun fara musayar zarge-zarge a bainar jama'a duk da rokon da Peter Obi ya yi
- Masu ruwa da tsaki sun ce rikicin na cikin gida ne kuma ba zai hana shirye-shiryen zaɓen 2027 ba, kamar yadda Legit ta samu labari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rikici ya kunno kai a cikin OK Movement, ƙungiyar da aka kafa domin tattara magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Matsalar ta fara ne bayan wata sanarwa da Jackie Wayas ta fitar, inda ta bayyana kanta a matsayin jagorar ƙungiyar ta ƙasa, tana sanar da naɗin tsohon shugaban IPAC, Peter Ameh, a matsayin Darakta Janar na ƙasa.

Kara karanta wannan
INEC ta cire sunayen ƴan takara, an cire sunan Jonathan, Goje da manyan ƴan siyasa

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Wayas ta ce kwamitin gudanarwar ƙungiyar ne ya amince da naɗin saboda gogewar Ameh a siyasa da kuma jajircewarsa wajen ciyar da manufofin ƙungiyar gaba.
Rikici ya kunno cikin ƙungiyar Obi, Kwankwaso
Sai dai cikin sa'o'i kaɗan bayan sanarwar, wasu mambobin ƙungiyar suka fara tuhumar Wayas na bayyana kanta a matsayin jagorar ƙungiyar, lamarin da ya haifar da sabon rikici.
Tsohon Kakakin ƙungiyar, Justin Ijeh, ya amince cewa akwai sabani, amma ya ce ya kamata a warware shi cikin gida ba tare da an samu gagarumar matsala ba.
Ya ce:
"Ya dace mu warware irin waɗannan matsaloli a bayan fage. Babban burinmu shi ne mu yi nasara a zaɓe."
Ya ƙara da cewa:
"Sabani abu ne da ke faruwa a siyasa, amma bai kamata a fito da shi gaban jama'a ba."
Ana son warware matsalar tafiyar Obi, Kwankwaso
Ijeh ya kuma bayyana cewa ya dakatar da kansa daga matsayin kakakin ƙungiyar har sai an sasanta rikicin, yana mai cewa rikicin ya ta'azzara ne bayan mutane biyu sun fara ikirarin matsayin Darakta Janar.
Sai dai Darakta Janar na OK Movement, John Ughulu, ya ce tuni an cire Justin Ijeh daga mukaminsa.

Source: Facebook
A cewarsa:
"An sallami Justin tun da daɗewa. Ya koma wani ɓangaren daban."
Ughulu ya ce an kafa OK Movement ne domin faɗaɗa goyon bayan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba tare da rusa sauran ƙungiyoyin magoya bayansu ba.
Ya ce:
"Obi ya roƙe ni ya ce, 'John, don Allah kada ka je kafafen yaɗa labarai, kada ka yi magana.'"
Haka kuma, Ughulu ya zargi Jackie Wayas da wasu mambobi da ƙoƙarin ƙwace jagorancin ƙungiyar, yana mai cewa ya taɓa samun sabani da ita kan yadda za a tara kuɗin gudanar da ayyukan ƙungiyar.
A gefe guda kuma, wasu rahotanni a shafukan sada zumunta sun yi ikirarin cewa an sauke Yunusa Tanko daga matsayin Mai Kula da Ƙungiyar Obidient Movement Worldwide kan zargin rashin gaskiya wajen harkokin kuɗi, amma ya musanta zargin.
Ya ce:
"Ba gaskiya ba ne. Ni ma ba ni da asusun ƙungiyar balle a ce akwai batun kuɗi da ya shafe ni."
Ibrahim Muhammad, shugaban Obidient Movement na jihar Kano ya tabbatar wa Legit cewa wannan matsala ce ta cikin gida.
Ya ce:
"Hakikanin gaskiya zan iya cewa rikici a OK movement ba zai iya haifar da matsala ba saboda rikici ne na cikin gida."
"A wannan tafiya ta mu, ko OK movement ko Obidient akwai kyakkyawan shugabanci, kyakkyawan fahimta da kyakkyawan alaƙa ko da wani rikici ya taso, In Sha Allahu mu kan hanyoyin da ya dace a yi maganin matsalolin da ya dace a lokacin da ya dace."
NDC ta soki gwamnatin Kano
A baya mun kawo labarin cewa jam'iyyar NDC ta zargi gwamnatin Kano da karɓar diyyar Hausawa da aka yi wa kisan gilla a Uromi da ke jihar Edo sannan ta yi shiru game da biyan iyalan wadannan mutane hakkinsu.
Jam'iyyar ta ce tana da hujjoji masu ƙarfi kan zargin da ta ke yi na cewa gwamnatin Kano ta hana kudin Ta kuma yi zargin cewa akwai wasu kudin da aka tara na tallafawa wadanda iftila'i ya shafa a Kano, amma shiru.
Mai magana da yawun NDC a Kano, Yusuf Fasaha ya ce gwamnatin ta gaza taimakon mazauna jihar, sannan ta gaza kare kanta daga wadannan manyan zarge-zarge da aka yi na rike hakkin jama'a.
Asali: Legit.ng

