Sanata Barau Jibrin Ya Tsige Hadimi saboda Adawa da Tazarcen Gwamna Abba a Kano

Sanata Barau Jibrin Ya Tsige Hadimi saboda Adawa da Tazarcen Gwamna Abba a Kano

  • Barau I. Jibrin ya tsige Umar Alhassan (King Indara) daga mukaminsa na Mataimaki na Musamman kan Al'amurran Majalisa
  • Sanatan ya yi waje da shi ne sakamakon wallafa kalamai masu taken "Abba Must Go" da ya yi a Facebook duk da yana ‘dan APC
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi kira ga mutanen Kano da su dangwala jam'iyyar APC daga sama har kasa a zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Mataimakin shugaban Majalisar dattawa a Najeriya, Barau I. Jibrin ya kori wani daga cikin masu ba shi shawara a aikinsa.

Sanata Barau Ibrahim Jibrin ya kori Umar Alhassan wanda aka fi sani da King Indara daga aiki a sanadiyyar wani rubutunsa.

Barau Jibrin
Sanata Barau Jibrin a gidansa, King Indara a tsakiya da Abba Kabir Yusuf wajen taro a Kano Hoto: Barau I. Jibrin/King Indara/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Barau Jibrin ya sanar da korar King Indara

Mataimakin shugaban Majalisar dattawa ya fitar da sanarwa a shafin Facebook, ya tabbatar da raba jiha da Umar Alhassan.

Kara karanta wannan

ICC ta saki yadda minista ya nemi yaudarar Buhari a ci $200m a aikin Mambilla

Hon. Shittu Madaki Kunchi ya fitar da sanarwa a madadin Barau Jibrin, ya shaida wa al’umma an kori King Indara daga aiki.

Shittu Madaki Kunchi shi ne Mai taimaka wa Barau Jibrin a harkokin yada labaraida hulda da jama'a.

Barau I. Jibrin ya zargi King Indara da yin kalamai da rashin da’a da ladabi ga Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sanata Barau yana tare da APC 100%

Hadimin ya rika yin rubutu da teken ‘Abba Must Go’, da nufin dole a ga bayan gwamntin Abba Yusuf ta APC a jihar Kano.

Shittu Kunchi ya yi amfani da damar wajen fada wa jama’a cewa Barau Jibrin yana so a zabi APC daga sama har kasa a 2027.

Jibrin wanda da farko ya nuna sha’awar neman takarar gwamnan Kano ya hakura da burin ganin Abba ya dawo jam’iyyar APC.

Sanatan na Kano ta Arewa yana goyon bayan Abba ya zarce a kan karaga har zuwa 2031.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya cire Atiku cikin wadanda ya kamata su nemi shugaban kasa

King Indara ya bar matsayinsa a Majalisar tarayya

Da wannan sanarwa aka sallami Umar Alhassan, ya bar kujerarsa ta Mataimaki na musamman a harkokin majalisa (SLA).

Daily Trust ta ce Indara ya yi fice kuma yana da farin jini a Tik Tok, ya fito shafin Facebook yana cewa Kano ta Kwankwaso ce.

Duk da cewa yana nuna goyon baya ga Sanata Rabiu Kwankwaso, matashin ya ce har yanzu yana nan a jam’iyyar APC mai mulki.

Bayanin ya ce matakin ya fara aiki daga ranar Juma’a, 18 ga watan Satumba 2026 duk da sai a safiyar Asabar aka ga sanarwar.

'Yan APC masu adawa da Abba a Kano

Akwai ‘yan APC kamar Abdulmajid Dinbilki Kwamanda wanda har yanzu sun ki karbar Abba a matsayin ‘dan takaransu a 2027.

Abdulmajid Dinbilki Kwamanda yana cikin manyan masu goyon takarar Barau, duk sanatan bai tare da wannan matsaya da ya dauka.

A yau matashin ya yi amfani da shafin Facebook yana murnar gama aikin SLA lafiya, ya ce shi ne wanda tafiyar Abba Must Go ta fara ci.

Kara karanta wannan

Bamanga Tukur: Tarihi da rayuwar shugaban jam’iyyar PDP na kusan karshe a mulki

Obi/Kwankwaso sun kafa kwamitin yakin zaben 2027

An rahoto Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun bayyana kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa mai mutum kusan 60.

Tsohon shugaban NNPP a Kano, Hashim Dungurawa da Sabo Gashuwa suna cikin mutane 59 sun samu shiga kwamitin kamfen na NDC.

An nada John Ughulu a matsayin Darakta-Janar (DG) na kwamitin yakin neman zaben, yayin da Saadatu Sani ta zama Sakatariya ta Kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng