Abba Ya Tona Asirin Abin da Kwankwaso Ya Tura Shi Ya Fadawa Tinubu kan Shiga APC

Abba Ya Tona Asirin Abin da Kwankwaso Ya Tura Shi Ya Fadawa Tinubu kan Shiga APC

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya tura shi wajen Shugaba Bola Tinubu domin yin alƙawarin komawa APC
  • Abba ya bayyana cewa Kwankwaso ya nemi ya yi rantsuwa da Alƙur’ani kan cika alƙawarin idan ya yi nasara a shari’ar zaɓen gwamna ta 2023
  • Gwamnan ya ce bai ɗauki komawarsa APC a matsayin cin amanar Kwankwaso ba, domin a ganinsa shi ya cika alƙawarin da tsohon ubangidansa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana yadda tsohon ubangidan siyasarsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya sa shi yin rantsuwar cewa za su koma jam’iyyar APC bayan zaɓen gwamna na 2023.

Abba ya ce sun yi yarjejeniya da Shugaba Bola Tinubu cewa idan bai tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano ba, za su koma jam’iyyar APC bayan samun nasara.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso
Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso a lokacin da suke NNPP. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamnan ya cewa BBC Hausa Kwankwaso ne ya jagoranci wannan yarjejeniya, amma daga baya ya yi watsi da ita, lamarin da ya ce ya sa shi ganin cewa komawarsa APC ba cin amana ba ce.

Abba Kabir ya je wajen Tinubu

Abba Kabir ya ce bayan zaɓen 2023 ne suka gana da Shugaba Bola Tinubu, inda suka tattauna batun shari’ar zaɓen gwamnan Kano.

A cewarsa, sun roƙi shugaban ƙasar kada ya tsoma baki a shari’ar da ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da ya samu.

Ya ce Kwankwaso ne ya tura shi wajen Tinubu domin ya tabbatar masa da alƙawarin komawa APC idan aka samu nasara.

Abba ya bayyana cewa Kwankwaso ya kuma nemi ya yi rantsuwa da Alƙur’ani domin tabbatar da gaskiyar alƙawarin.

Abba ya soki Kwankwaso

Gwamnan ya ce ya je wajen Tinubu ya tabbatar masa da alƙawarin, inda ya ƙara da cewa Kwankwaso ya sha ganawa da shugaban ƙasar kan batun komawa APC.

Kara karanta wannan

Dattawa sun shiga magana, ana ta tir da sakin auren gwamna Abba a jihar Kano

Ya kuma ce tsohon ubangidan siyasarsa ya sha tura tawagogi domin tattauna shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki.

A cewar Abba, yarjejeniyar ta ƙunshi komawar Kwankwaso da shi da kuma magoya bayansu APC bayan samun nasara a shari’ar zaɓen gwamna.

Sanata Kwankwaso da Bola Tinubu
Rabiu Musa Kwankwaso da Bola Tinubu a Aso Villa. Hoto; Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sai dai ya ce daga baya Kwankwaso ya sauya matsayarsa kan shiga APC, duk da cewa shi ne ya sa aka yi alƙawarin.

A bayanin da ya yi, Gwamnan Kano ya ce bai ɗauki matakin komawarsa APC a matsayin butulci ko cin amanar Kwankwaso ba.

NDC ta kafa kwaitin kamfen

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NDC ta ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta na babban zaɓen 2027 a jihar Kano, inda ta yi alƙawarin bai wa ƙananan hukumomi cikakken ’yanci.

An gudanar da taron a ƙaramar hukumar Gezawa, inda ya samu halartar dimbin magoya baya, shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki daga sassan jihar.

Ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce idan aka zaɓe su, za su tabbatar da cewa kudin ƙananan hukumomi na zuwa kai tsaye garesu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng