Abdulaziz Yari Ya Sake Tara Malamai 1,500 a Zamfara duk da Sace Wasu a Baya
- Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya karɓi baƙuncin malaman addinin Musulunci 1,500 a garin Talata Mafara
- Yari ya ce sun yi addu’ar samun zaman lafiya a Zamfara da kuma yi wa Gwamna Dauda Lawal addu’a yayin shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓe
- Sanatan ya kuma gana da mataimakin sufeto-janar na ’yan sanda, AIG Ahmed Musa, domin tattauna matsalar tsaro a Zamfara da jihohin Sokoto da Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari ya karɓi baƙuncin malaman addinin Musulunci 1,500 a garin Talata Mafara da ke jihar Zamfara.
Yari, wanda ya taɓa zama gwamnan jihar, ya ce malaman sun taru ne domin yin addu’ar samun zaman lafiya da kuma yi wa Gwamna Dauda Lawal addu’a yayin shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya je Maiduguri, ya fito da abubuwa 3 da za su sa 'yan Arewa su nemi canji a 2027

Source: Facebook
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Sanatan ya kuma bayyana cewa ya gana da mataimakin sufeto-janar na ’yan sanda, AIG Ahmed Musa, domin tattauna matsalar tsaro a Zamfara da jihohin Sokoto da Kebbi.
Yari ya gana da malamai 1,500
Sanata Yari ya ce ya karɓi baƙuncin malaman addinin Musulunci 1,500 daga sassa daban-daban na Zamfara a Talata Mafara.
Ya bayyana cewa sun yi addu’o’i domin samun zaman lafiya a jihar, tare da yi wa Gwamna Dauda Lawal addu’a a shirye-shiryen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa.
Sanatan ya gode wa malaman bisa amsa gayyatarsa da kuma halartar taron yi wa dan takarar APC kuma gwamnan jihar Zamfara addu'a.
Maganar Yari kan tsaro
A wani ɓangare na ziyarar tasa, Sanata Yari ya gana da AIG Ahmed Musa na shiyya ta 10 ta rundunar ’yan sandan Najeriya.
Rahoto ya nuna cewa ya ce sun tattauna batutuwan tsaro da suka shafi jihar Zamfara da jihohin makwabtanta na Sokoto da Kebbi.
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Source: Original
Dauda Lawal ya raba babura
A wani rahoto da aka fitar ranar 22 ga Nuwamba, 2026, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon babura 1,000, adaidaita sahu 100, motocin Hijet 40 da ƙananan motocin ɗaukar kaya masu ƙafa uku 40 a Gusau.
Gwamnatin jihar ta ce rabon wani ɓangare ne na shirin tallafa wa jama’a ta hannun Hukumar Rage Talauci ta Jihar Zamfara (ZAPA), domin taimaka wa mutane da ƙungiyoyi su bunƙasa sana’o’insu, samar da ayyukan yi da dogaro da kai.
Dalilin shigar Abba APC
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito da bayanai game da dalilin shigar shi jam'iyyar APC mai mulki duk da Rabiu Kwankwaso bai so hakan ba.
A wata hira da aka yi da shi, Abba ya ce Kwankwaso ya tura shi wajen shugaba Bola Tinubu ya masa alkawarin zai koma APC idan ya yi nasara a kotu.
Bayan INEC ta sanar da Abba ya lashe zaben 2023, abokin hamayyarsa, Nasiru Gawuna ya kalubalanci nasarar a kotu, inda hakan ya haifar wa Abba fargaba.
Asali: Legit.ng
