Jagoran NDC Ya Yi Kus Kus da Obi da Kwankwaso Suna Shirin Fara Kamfen

Jagoran NDC Ya Yi Kus Kus da Obi da Kwankwaso Suna Shirin Fara Kamfen

  • Jogoran NDC a Najeriya, Sanata Henry Seriake Dickson ya bukaci mambobin jam'iyyar su haɗa kai domin samun nasara a zaben 2027
  • Dickson ya yi kiran ne bayan ganawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Tsohon gwamnan Bayelsa ya ce jam'iyyar na shirin ƙaddamar da kwamitin yakin neman zabe domin tunkarar zaben shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jigon jam'iyyar Nigeria NDC, Sanata Henry Seriake Dickson, ya yi kira ga mambobin jam'iyyar su haɗa kai domin tabbatar da nasarar 'yan takararta a zaben 2027.

Dickson, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, ya yi wannan kira ne bayan tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, da wanda zai masa mataimaki, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai

Shugabannin NDC a Najeriya
Henry Dickson da jagororin NDC a Najeriya. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce tattaunawar ta shafi makomar jam'iyyar da kuma wasu muhimman batutuwan da suka shafi Najeriya.

Ganawar Dickson da Obi/Kwankwaso

Dickson ya ce ya gana da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso tare da shugaban jam'iyyar na kasa da sauran shugabanninta, domin ci gaba da tattaunawa kan shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.

A cewarsa, shugabannin jam'iyyar sun gudanar da ganawa sau biyu cikin kwanaki biyu domin tattaunawa tare da kammala wasu muhimman shawarwari.

Ya ce ana yin hakan ne musamman yayin da jam'iyyar ke ci gaba da shirye-shiryen ƙaddamar da kwamitin yakin neman zabenta kafin babban zaben 2027.

Dickson ya bukaci hadin kai

Sanata Dickson ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, masu neman takara da sauran mambobin jam'iyyar da su manta da sabani tare da hada kai.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Danjuma Goje ya raba gardama kan batun ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya

Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wajen taron siyasa. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Getty Images

Ya ce a wannan lokaci mai muhimmanci, wajibi ne kowa ya bayar da gudunmawarsa domin tabbatar da nasarar 'yan takarar jam'iyyar daga mataki na kasa har zuwa sauran mukamai.

Vanguard ta rahoto shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa:

"A wannan lokaci mai muhimmanci, ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, masu neman takara da mambobin babbar jam'iyyarmu da su hada kai, su dunkule wuri guda domin samun nasarar 'yan takararmu a dukkan matakai."

Peter Obi ya hada ai da Kwankwaso domin shiga zaben shugaban kasa na 2027 da niyyar yin nasara a kan Bola Tinubu na APC da Atiku Abubakar na ADC da sauran 'yan takara.

APC an son mamaye kujerun Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba za ta mika ko kujera daya ga jam'iyyun adawa a Kano a zaben 2027 ba.

Kara karanta wannan

'A bar yan Najeriya su yanke hukunci': Bashir Ahmad ya kalubalanci Kwankwaso

Dan majalisar ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya yi da shugabannin APC da wakilan rumfunan zabe daga kananan hukumomin Kiru da Bebeji.

Jibrin Kofa ya ce APC na da yakinin cewa za ta ci gaba da rike kujerar shugaban kasa tare da lashe dukkan kujerun da ake takara a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng