Kano: Wuta Ta Taso a NDC, Shugaban Jam'iyya Ya Jefi Kwankwaso da Zargin Kama Karya

Kano: Wuta Ta Taso a NDC, Shugaban Jam'iyya Ya Jefi Kwankwaso da Zargin Kama Karya

  • Muhammad Rabiu Bakin Zuwo ya yi bayanin abubuwan da suka rika faruwa a cikin jam’iyyarsu ta NDC
  • Shugaban jam’iyyar ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da murkushe su da hana mutanensa samun takara
  • Bakin Zuwo ya ce jagoran na Kwankwsiyya ya dage sai ya raba shi Usaini Mai Riga daga mukamansu a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Muhammad Rabiu B/Zuwo wanda shi ne shugaban NDC na shiyyar Arewa maso yamma ya yi maganganu da suka tada kura.

‘Dan siyasar ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da kokarin ganin bayan shi duk da yadda suka rungume shi lokacin da ya rabu da ADC.

Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi a taron NDC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Rabiu Bakin Zuwa ya fallasa Rabiu Kwankwaso

Gidan rediyon Express Kano ta rahoto Muhammad Rabiu Bakin Zuwo yana bayanin tuggun da aka shirya wa shi da Usaini Isah Mai Riga.

Kara karanta wannan

Sai bango ya tsage: Yadda APC ke ta yi wa Kwankwaso illa sakamakon rikicin NDC a Kano

Bayan karbar Rabiu Musa Kwankwaso cikin NDC, ya yi ikirarin tsohon gwamnan ya huro wuta yana son a tsige wadannan mutane biyu.

Muhammad Rabiu Bakin Zuwo ya ce ana kokarin raba sa da shugabancinsa a jam’iyyar NDC, amma lamari zai juye da mujiya.

“Rabiu Musa Kwankwaso bayan ya shigo jam’iyya ya ce dukkanmu a kore mu, daga ni har su Mai Riga. Yankina gaba daya ya ce a bar masa.
Shugaban jam’iyya ya ce wannan ba zai yiwu ba, kai (Kwankwaso) dai ku shigo da mutanenka, wanda ya ce ba za a yi masa wannan ba.”
Su kuma mutanen jam’iyya suka ce ba za mu kori mutanensa saboda ka shiga ba, komai alfarmar ka, komai jama’anka, amma za a ba ka kowane irin mukamai.

- Muhammad Rabiu Bakin Zuwo

Saura kiris a sallama wa Kwankwaso a NDC

Rabiu Bakin Zuwo ya yi ikirarin Kwankwaso ya dage a tsige Mai Riga, shi kuma ya ki yarda tunda shugaban na Kano bai yi wani laifi ba.

Domin a zauna lafiya ya ce shi zai hakura da kujerarsa ta shugaban ADC a ba Usaini Mai Riga an raba shi da shugabancin reshen Kano.

Kara karanta wannan

2027: Jigon APC ya yi zargin Kwankwaso na da dan takarar shugaban kasa ba Obi ba

A karshe dai ya ce an yarda ba za a taba shugabannin ba, amma bayan nan Kwankwaso ya dawo da maganar har aka samu sabani a jihar.

Wannan lamari a cewar Bakin Zuwo ne ya kai har an fara duba yiwuwar a dakatar da Sanata Kwankwaso ko a kore shi daga jam’iyyar NDC.

Yadda aka yi rabon mukamai a jam'iyyar NDC

Haka aka lallaba har Kwankwasiyya ta samu 60% na kujerun NDC yayin da tsofaffin ‘yan jam’iyya suka rike 40%, kuma ana yin biyayya.

Da aka zo zancen ‘yan takara, ‘dan siyasar ya ce Kwankwaso ya bukaci su kyale sa shi kadai ya fito da wadanda za su rike wa NDC tuta.

B/Zuwo ya ce duk da suna da 40% na mukaman jam’iyya, Sanata Kwankwaso ya ce ko mutum daya ba zai ba takara daga bangarensu ba.

Tsofaffin ‘yan jam’iyya sun bukaci ‘dan takara daya a Majalisar dokoki da biyar a Majalisar tarayya amma abin ya ki yiwuwa a NDC.

Akwai kura a NDC a Kano har yanzu

A hirarsa, ya ce ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar NDC ya hana su takara ko daya.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan da suka ki barin jam'iyyar PDP har yau duk da rikicin cikin gida

Bakin Zuwo ya kuma ce nan gaba zai fitar da sunayen asalin wadanda za su yi wa jam’iyyarsu ta ADC takara a jihar Kano a zabe mai zuwa.

A halin yanzu, NDC ta kafa kwamiti da zai biniki Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo domin ana zargin ba shi da cikakkun takardun karatu.

Kyautar Abba a Kano ta jawo magana

Labarin nan ya ce wasu mazauna jihar Kano sun nuna rashin jin daɗinsu kan matakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na raba filaye 1,540 dakudi ga masoyansa.

Mazauna jihar sun bayyana cewa dukiyar gwamnati mallakin al'umma ce baki ɗaya, don haka bai dace a fifita wani ɓangare ko ƙungiyar siyasa a kansu ba.

Haka zalika, shugaban jam'iyyar ADC na jihar ya zargi cewa an yi rabon ne domin jan hankalin shugabannin rumfunan zaɓe gabannin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng