Kwankwaso Zai Yi Bikon Mai Dakin Abba da Ta Bar Gidan Gwamnatin Jihar Kano

Kwankwaso Zai Yi Bikon Mai Dakin Abba da Ta Bar Gidan Gwamnatin Jihar Kano

  • Musa Iliyasu Kwankwaso ya nuna zai je su yi bikin Zainab Musa Kwankwaso da yanzu ta bar gidan Gwamnan jihar Kano
  • Tsohon kwamishinan bai da ra’ayin cewa Mai girma Abba Kabir Yusuf ya saki matar shi a wajen taro da aka yi a kwanaki
  • Alhaji Musa Kwankwaso yana sa rai aurensu zai dawo kuma idan zabe ya zo za su dankara jam’iyyar NDC da kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Tsohon kwamishina a gwamnatin jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso shi ma ya yi magana game da zancen auren gwamna.

An samu sabani tsakanin Abba Kabir Yusuf da matarsa ta biyu, Zainab Musa Kwankwaso hara bin ya kai ta kwashe kaya daga cikin gidansa.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Zainab Musa Kwankwaso Hoto: @Dawisu
Source: Twitter

Musa Kwankwaso zai dawo da auren Gwamnan Kano

A hirar Musa Iliyasu Kwankwaso da DCL Hausa, ya nuna a shirye yake da ya yi kokari wajen ganin an dawo da igiyar wannan aure tamau.

Kara karanta wannan

Abba ya yi wa Kwankwaso tonon silili kan shiga APC da zuwa wajen Tinubu

‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa babu wanda ya sa shi wannan aiki, ya ce ba gwamna ne ya aike shi ba, shi ne kawai yake ganin dacewar hakan.

Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya roki tsohon gwamnan Kano kuma uba wajen matar da ya yi hakuri a janye karar da aka kai wa kotu a Abuja.

An ji yana mai rokon Rabiu Musa Kwankwaso a hakura da maganar kotu tunda dai wannan baiwar Allah tamkar diya kuma kanwa ce a wurinsu.

Babban jagoran na APC ya nemi Zainab Musa Kwankwaso ta koma dakin mijinta a cigaba da aure.

Musa Kwankwaso suna harin ganin bayan NDC

Bayan nan kuma ya ce sai a shiga fagen siyasa inda za su doke Aminu Abdussalam da kuma ‘dan tsohon gwamna wato Mustapha Kwankwaso.

Kwankwaso ya kuma nuna APC ta ci burin ganin bayan ‘dan takaran NDC a Madobi, ya ce Abba Kabir Kan tsaida kanin Kwankwaso daga yankin.

Kara karanta wannan

Abin da ya fi ba Abba Kabir haushi kan rigimarsa da matarsa, Zainab Kwankwaso

Tsohon kwamishina ya ce gwamna bai saki matarsa ba

A game da kalaman da gwamna ya yi a wurin taro kuwa, Sarkin Yakin Karayen ya ce abin da Abba ya fada ba su nufin ya tsinka igiyar aurensa.

“Ba saki ba ne, ai gwamna bai saka ba. Saki shi ne ka ce ‘ni wane (ka fadi sunanka), ka ce na saki wance.”

- Musa Ilyasu Kwankwaso

Ya kuma kara da kalubale

“Ka kawo mani bidiyo ko audio (sauti) inda gwamna ya yi irin wannan”

Abba Kabir ya yi wa Kwankwaso butulci?

A tattaunawar da aka yi da shi, ‘dan siyasar ya kuma wanke Abba daga zargin butulci saboda ana ganin ya raba jiha da tsohon mai gidansa a siyasa.

Mataimakin darektan yakin neman zaben na APC a Kano ta tsakiya ya ce ba haka abin yake ba.

Ya ce idan haka ne za a kira Jagoran Kwankwasiyya butulu domin ya bijire wa Sanata Hamisu Musa da Musa Gwadabe duk da su ne iyayen gidansa.

Kara karanta wannan

Dattawa sun shiga magana, ana ta tir da sakin auren gwamna Abba a jihar Kano

Kwankwaso
Jagora a APC ta Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Dattijon Arewa ya soki Gwamna Abba

An ji cewa babba a Arewa, Hakeem Baba Ahmed wanda ya yi aiki da gwamnatoci da-dama yana da shawara ga Abba Kabir Yusuf.

Dattijon ya ce abin da Gwamnan Kano ya yi na tsinka igiyar aurensa a bainar jama'a ba daidai ba ne, kuma bai dace da Musulunci ba.

Ban da lamarin auren Abba Kabir Yusu, Dr. Hakeem Baba Ahmed ya yi tir da ihu da wasu suka fito suka yi wa Bola Tinubu a masallaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng