Yadda Kawancen Tallata Tinubu da Wike Ya Kafa ke Neman Tarwatsewa
- Kawancen Rainbow da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kafa domin marawa Shugaba Bola Tinubu baya a 2027 na fuskantar kalubale bayan wasu sun nesanta kansu da tsarin
- A Rivers, bangaren jam’iyyar LP ya nuna rashin amincewa da yadda aka kafa kawancen, yana mai cewa mutanen da ke wakiltar jam’iyyar ba su da alaka da su a jihar
- Haka kuma shugabannin APC a Kudu maso Gabas sun yi watsi da abin da suka kira kawancen “Rainbow”, tare da bayyana goyon bayansu ga ‘yan takarar APC a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Kawancen Rainbow da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kafa domin marawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027 na fuskantar sabani daga wasu bangarorin siyasa.
Kawancen ya kunshi APC, PDP, LP da AA a Jihar Rivers, amma wasu ‘yan jam’iyyar LP a jihar sun ce ba a tuntube su wajen kafa tsarin ba.

Source: Twitter
LP ta nesanta kanta da Wike
Daily Trust ta wallafa cewa shugabannin LP a Rivers sun ce mutanen da kawancen ke mu’amala da su ba mambobin LP ba ne, illa dai suna da alaka da Kungiyar Kwadago.
Tsohon Mataimakin Shugaban LP na Shiyyar Kudu maso Kudu, Favour Reuben, ya ce ba ya cikin kawancen.
Reuben ya kuma yi zargin cewa dan takarar gwamna na LP da kawancen ya amince da shi dan PDP ne, ba dan jam’iyyar LP ba.
An soki tsarin kawancen
Masanin siyasa kuma mai rajin kare hakkin al’ummar Ogoni, Dr Celestine Akpobari, ya soki tsarin kawancen, yana mai cewa bai kunshi kowa ba.
Akpobari ya yi tambaya kan yadda za a kira kawancen Rainbow alhali, a cewarsa, shugabannin APC da PDP da kuma ‘yan takarar gwamna na APC, PDP da LP duk ‘yan kabilar Ikwerre ne.

Source: Twitter
Ya ce idan aka dauke mulki daga Gwamna Siminalayi Fubara wanda ya fito daga Rivers ta Kudu maso Gabas, ya kamata a ba al’ummar Ogoni damar samun mulki, kasancewar ba su taba samar da gwamna, mataimakin gwamna, Kakakin Majalisar Jiha ko Babban Alkalin Jihar ba.
'Kawancen ya mamaye Rivers'
Wani jigon APC a Rivers da ke cikin kawancen, wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce kawancen ya riga ya samu iko sosai a jihar.
Ya yi ikirarin cewa shugabannin kananan hukumomi da kansilolin gundumomi na cikin kawancen, sannan Gwamna Fubara da magoya bayansa sun koma cikin tsarin.
A nasa bangaren, tsohon Shugaban Kungiyar Matasan Ijaw ta Duniya kuma dan takarar gwamna na LP a Bayelsa a 2023, Udengs Eradiri, ya bayyana Rainbow Coalition a matsayin wata dama da za ta iya taimakawa wajen tara kuri’u ga Tinubu a 2027.
Rawar da Tinubu zai taka
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin shiga tsakani kan sabanin da ke tsakanin gwamnonin APC da Ministan Abuja, Nyesom Wike, yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Wike, wanda ke jagorantar bangare a jam’iyyar PDP yayin da yake rike da mukamin minista a gwamnatin APC, ya kasance yana tallata Rainbow Coalition a Rivers domin marawa Tinubu baya a zaben shugaban kasa na 2027.
Wike ya kuma zargi Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da takwaransa na Imo, Hope Uzodimma, da hannu wajen kalubalen siyasar da yake fuskanta, yana mai cewa adawar nasu na da alaka da yaduwar Rainbow Coalition.
Asali: Legit.ng

