Masoya Kwankwaso da Obi Sun Yi Riga Malam Masallaci, Sun Fara Shirin Kamfen

Masoya Kwankwaso da Obi Sun Yi Riga Malam Masallaci, Sun Fara Shirin Kamfen

  • A yayin da ake samun masu sha'awara tsayawa takara a jam'iyyar hamayya ta ADC, an ƙaddamar da Obi-Kwankwaso Movement domin tallata takarar jagororin
  • Wasu jiga-jigan jam'iyya kamar Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi sun nuna sha'awar neman takara a jam'iyyar, inda aka fara batun maslaha
  • Sai dai tun kafin a kai ga batun maslaha ko zaben fitar da gwani an samar da kungiyar da ke nuna sha'warar tallata takarar Obi da Kwankwaso gabanin 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wata sabuwar ƙungiyar siyasa mai suna Obi-Kwankwaso Movement (OK Movement) ta kaddamar da tsarin shugabanci na ƙasa da jihohi.

An kafa wannan kungiya ne duk da cewa jam'iyyar ADC ba ta fitar da 'dan takarar da zai wakilce ta a zaben shugaban kasa na 2027 mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Gabanin 2027, ADC ta fada wa Tinubu maganar da za ta jefa masa tsoron 'yan adawa

An samar da kungiyar tallata manufar Obi da Kwankwaso
Tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa kungiyar, an kafa ta ne domin hada kan 'yan kasa a tunkari matsalolin da suka addabi Najeriya.

Masoya Obi da Kwankwaso sun hade

Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran kungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya fitar a Abuja ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026, ƙungiyar ta ce wannan ya wuce batun siyasa.

OK Movement ta kara da cewa wannan wani sabon yunƙuri ne na sake gina ƙasa bisa tsari mai ɗorewa da gaskiya domin a samu ci gaban da ake da muradi. Sanarwar ta ce:

“Al’ummarmu na fuskantar matsanancin talauci, tsadar rayuwa da rashin tsaro. A irin wannan lokaci, OK Movement ta fito da sabuwar mafita ta haɗin kai da gyara tsarin ƙasa.”

Ta ƙara da cewa ƙungiyar ta fahimci irin wahalar da ‘yan Najeriya ke ciki, daga manoma zuwa ‘yan kasuwa, inda ta bayyana kanta a matsayin hasken da zai jagoranci fitar da kasa daga duhu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: "Kwankwaso ya amince ya zama abokin takarar Peter Obi"

Kungiyar Kwankwaso-Obi ta watsar da kabilanci

OK Movement ta jaddada cewa manufarta ita ce tabbatar da cewa Najeriya za ta inganta ta kowace fuska, tana mai cewa, tafiyar Kwankwaso da Obi tsari ne na aiki mai ma’ana.

Ƙungiyar ta yi watsi da siyasar kabilanci, addini da yanki, tana mai cewa waɗannan abubuwa sun dade suna raba kan ‘yan ƙasa.

Kungiyar ta shirya bude rassanta a jihohin Najeriya
Sanata Rabiu Musa Kwanwkaso tare da Peter Obi a yayin tarbar tsohon jagoran NNPP zuwa ADC a Kano Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Muna gina ƙasa wacce adalci za ta tabbata a cikinta, inda arziki zai amfani kowa, kuma inda shugabanci ke kawo zaman lafiya da ci gaba.”

OK Movement ta kuma bayyana cewa za ta fara buɗe rassanta a jihohin ƙasar nan cikin makonni masu zuwa, tare da gayyatar duk wanda ke son ganin sabuwar Najeriya mai inganci da shiga cikin tafiyar.

Kwankwaso zai yi takara da Obi

A baya, mun wallafa cewa wani na kusa da Peter Obi ya bayyana cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya amince ya zama abokin takarar tsohon gwamnan Anambran a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari wata fitacciyar jami'a a Arewa? Gaskiya ta bayyana

Ibrahim Abdulkarim ya tabbatar da cewa an riga an tsara taron haɗin gwiwa tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da kuma Obidients gabanin babban zabe da ke jan hankalin kasa.

Kwankwaso ya taba cewa zai karɓi muƙamin mataimakin shugaban ƙasa na Peter Obi, muddin aka samar da amana, duk da ya girmi Obi a siyasance domin a hada kai wajen fitar da APC a mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng