‘Yan Siyasa 12 da Aka Taba Samu da Yi wa ‘Yan Adawa Barazana Lokacin Zabe

‘Yan Siyasa 12 da Aka Taba Samu da Yi wa ‘Yan Adawa Barazana Lokacin Zabe

Abuja - A shekarar nan ana neman dawo da siyasar barazana, inda za a ji masu rike da mulki suna yin munanan kalamai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Daga 'yan jam'iyya, gwamnoni, ‘yan majalisa zuwa shugabannin kananan hukumomi, an saba jin ‘yan siyasa suna neman tada hankali.

Rahoton nan ya bibiyi tarihi, ya tuno da ‘yan siyasar da aka taba ji sun bari giyar mulki ya ja su a kan aboka hamayyarsu daga 2015 zuwa yau.

Shema
Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema da Shugaban kasa Goodluck Jonathan kafin zaben 2015 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

‘Yan siyasar da kalamansu suka nemi jawo rikici

1. Muhammad Gadaka

Kwanan nan aka ji shugaban APC na reshen Yobe, Muhammad Gadaka yana kira ga mata su bokarewa mazajensu wajen zaben jam’iyyarsu.

An rahoto cewa Alhaji Gadaka ya fada wa matan su nemi saki idan masu gidansu suka hana su zaben APC, yake cewa bayan nan shi zai aure su.

Kara karanta wannan

"Ka nemi afuwa ko ka yi murabus," An taso gwamnan APC kan kalaman da ya yi

Da ya ji matin lamba da surutun jama’a, ‘dan siyasar ya yi maza ya nemi afuwar mutane.

2. Sainna Buba

A wani taron siyasa a Satumban 2026, Sainna Buba wanda ke rike da kujerar kwamishina a gwamnatin jihar Borno ya yi barazanar karya yatsun ‘yan adawa.

Leadership ta ce Kwamishinan na matasa da yaki da talauci ya janye kalaman da ya yi, ya ce bai kamata al’umma su yi amfani da zahirin maganganunsa ba.

3. Danjuma Shekwolo

Shi Danjuma Shekwolo ya dauko ta da zafi, domin ya yi barazanar za su kori duk wanda bai goyon bayan APC a karamar hukumar Kuje a birnin Abuja.

Da surutun jama’a ya yi, shugaban karamar hukumar ya yi kokarin wanke kan shi a cewar rahoton Arise. Lamarin ya kai 'yan sanda sun fara binciken su.

4. Francis Nwifuru

Mai girma gwamna Francis Nwifuru ya yi wa shugabannin kananan hukumomin Ebonyi kashedi za su iya rasa kujerunsu idan APC ta kunyata.

Mun rahoto Gwamna Francis Nwifuru yana cewa duk shugaban karamar hukumar da ya bari APC ta fadi zabe, ya yi ta kujerarsa bayan zaben 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

Kalamansa ba da 'yan adawa suke ba, amma ya saba doka kuma ya nuna yadda siyasa ta rufe ido.

5. Francis Fadahunsi

Gabanin zaben gwamna da aka yi a watan Agustan 2026, an ji yadda Francis Fadahunsi ya fito yana barazana ga rayukan ‘yan jam’iyyar Accord a Osun.

An zargi sanatan Gabashin Osun da bada umarnin a kashe ‘yan adawar APC, amma ya kare kan shi da cewa an fassara kalaman na shi ne ba daidai ba.

6. Yahaya Bello

A tsakiyar shekarar nan Sahara Reporters ta rahoto Yahaya Bello yana cewa za su casa mutanen da ya kira abokan gabarsu a siyasar Kogi ta tsakiya.

Tsohon gwamnan bai ambanci sunan kowa ba, amma yi maganganu masu hadari yayin da ake murnar Tijani Lubabatu Ozavize ta zama lauya.

7. Monday Okpebholo

Wani gwamna a Najeriya a wannan bakin jeri shi ne Monday Okpebholo wanda ya yi wa Peter Obi gargadi game da shigowa jihar Edo ba da izininsa ba.

A kan haka BBC ta rahoto Femi Falana yana cewa maganar da gwamnan Edo ya yi ta ci karo da sashe na 33 da ta ba kowane ‘dan kasa damar yawo.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga shirye shiryen dinke barakar da ta bijiro wa jam’iyyar a jihohi

8. Nyesom Wike

Lokacin da za a yi takarar 2023, Nyesom Wike ya fito ya yi kalaman da ake ganin suna da hadari a Najeriya da ta ke karkashin tsarin damukaradiyya.

Idan aka dogara da rahoton Vanguard, za a ji yadda tsohon gwamnan Rivers ya kira wasu ‘yan siyasa kusan 30, yake cewa ana neman su ruwa a jallo.

9. Abdulmajid Danbilki Kwamanda

Abdulmajid Danbilki Kwamanda sai da ya shiga hannun DSS a 2024 lokacin da aka zarge shi da tada wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf hatsaniya.

Fitaccen ‘dan siyasar ya zargi Rabiu Kwankwaso a lokacin da yin kutun-kutun na ganin Muhammadu Sanusi II ya dawo kan ragamar sarkin Kano.

10. Adamu Aliyu Kibiya

Da ake tsoron Abba Kabir Yusuf zai iya rasa mulkin Kano a sakamakon hukuncin kotun karar zabe, Adamu Aliyu Kibiya ya fito ya yi baram-barama.

Da jin Adamu Aliyu Kibiya ya aika wa alkaklan kotun korafin zabe da barazanar kisa, wannan ya sa Gwamnan Kano ya yi maza ya tsige shi a 2023.

Kara karanta wannan

Shin da gaske Sheikh Gumi ya yi barazanar hargitsa Najeriya kan 'yan bindiga? An gano gaskiya

'Yan siyasa da kalamansu suka zama matasala a baya

11. Mukhtar Ramalan Yero

Mai girma Mukhtar Ramalan Yero ya yi maganganu marasa dadin ji kafin a yi zaben gwamnan Kaduna a 2015 lokacin da zai gwabza da Nasir El-Rufai.

The Guardian ta ce Ramalan ya yi wa magoya bayan APC da ‘dan takaransu barazanar hana shi shiga Kaduna ko ya rusa gidajensa ko ya hana shi motsi a jihar.

12. Ibrahim Shehu Shema

Gwamna Ibrahim Shehu Shema yana sahun wadanda ake zargi sun nemi tada rigima da suka hango jam’iyyar APC za ta iya kifar da su a zaben 2015.

Gwamnan Katsina ya kamanta ‘yan adawa da kyankyasai a gida ya kuma zuga mutane su kashe su kamar kwari a gidajensu, labarin ya zo a Vanguard.

Wike.
Nyesom Wike a taron siyasar PDP a shekarun baya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Majalisar shari'a ta yi zancen El-Rufai

Rahoto ya zo cewa Majalisar shari’a ta ce dole a yi wa Nasir El-Rufai adalci a shari’arsa da ICPC da DSS da ake yi a kotu dabam-dabam.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

A wani jawabi da ta fitar ta hannun Nafiu Baba Ahmad, ta ce ya kamata a yi wa tsohon gwamnan Kaduna adalci kamar kowane 'dan kasa.

Sakataren Majalisar Shari’a ta SCSN ya bayyana damuwa kan tsare Nasir El-Rufai da ake yi har gobe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng