"Ka Nemi Afuwa ko Ka Yi Murabus," An Taso Gwamnan APC kan Kalaman da Ya Yi
- Kalaman da Gwamna Francis Nwifuru ya yi lokacin rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi na ci gaba da tayar da kura a Ebonyi
- Jam'iyyar PDP ta nuna damuwa kan kalaman gwamnan, inda ta yi kira da ya fito ya nemi afuwa ko kuma ya yi murabus daga mukaminsa
- PDP ta bayyana kalaman gwamnan a matsayin masu tunzura jama’a kuma masu iya haddasa tashin hankali na siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi, Nigeria - Jam’iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta bukaci Gwamna Francis Nwifuru ya gaggauta janye kalaman da ya yi kan ’yan adawa a jihar, tare da neman afuwa ba tare da wani sharadi ba.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci gwamnan na APC da ya nemi afuwa ko kuma ya yi murabus daga mukaminsa.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce jam’iyyar ta bayyana kalaman gwamnan a matsayin masu tunzura jama’a kuma masu iya haddasa tashin hankali na siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Kalaman da gwamnan Ebonyi ya yi
Fushin PDP ya samo asali ne daga kalaman da Gwamna Nwifuru ya yi ranar Talata yayin rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu a Abakaliki.
Yayin da yake mayar da martani kan zargin cewa mambobi da magoya bayan APC mai mulki suna muzgunawa tare da tsoratar da masu sukarsa, Nwifuru ya gargadi ’yan adawa.
Ya ce:
“’Yan adawa suna zargin yan APC na muzgunawa tare da tsoratar da su. Suna nan za su ga barazana ta gaskiya a lokacin da ya dace,” in ji gwamnan.
Gwamna Nwifuru ya kuma umarci shugabannin kananan hukumomin da aka rantsar da su su tabbatar APC ta mamaye harkokin siyasa a matakin kasa gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya ware gwamnonin Arewa, ya fadi matsalan da za su fuskanta a zaben 2027
“Kada ku bari ’yan adawa su yi nasara a 2027. Duk shugaban karamar hukumar da ya kasa lashe karamar hukumarsa za a tsige shi daga mukaminsa.”
PDP ta bukaci Nwifuru ya nemi afuwa
Da yake magana a wani shirin rediyo kai tsaye ranar Juma’a, sakataren yada labaran PDP a jihar Ebonyi, Darlington Peter-Onwe, ya bukaci gwamnan ya dauki alhakin kalamansa.
Ya ce kalaman sun riga sun haddasa karuwar nuna kiyayya ga mambobin jam’iyyun adawa da kuma ’yan jarida a jihar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Ya ce:
“Ya kamata gwamnan ya nemi afuwar mutanen Ebonyi ko kuma ya yi murabus. Dole ne ya janye kalaman ko ya sauka daga mukaminsa saboda ya saba wa muhimman manufofi da ka’idojin tafiyar da gwamnati.”

Source: Twitter
Peter-Onwe ya ce sashe na 14 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa babban nauyin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A cewarsa:
“Ta hanyar yin irin wadannan kalamai, shi ne yanzu yake nuna alamun tashin hankali.”
Yan daba sun farmaki taron PDP
A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari kan 'yan jaridar a jihar Ebonyi yayin taron siyasa.
Majiyoyi suka ce an kuma kai hari kan mambobin jam'iyyar PDP yayin wani taron sauya sheka da aka gudanar a Idembia, karamar hukumar Ezza ta Kudu.
Rahotanni sun ce akalla magoya bayan PDP 20 sun gamu da hari, takwas sun jikkata, yayin da aka lalata motoci, kujeru, rumfuna da sauran kayayyaki.
Asali: Legit.ng

