Wakilan Tinubu Sun Je Gidan Dahiru Bauchi, Sun Gargadi 'Yan Arewa kan 2027
- Darakta Janar na Kwamitin Kamfen din APC, Abdul’aziz Yari, ya gargadi ’yan Arewa kan matsa lamba cewa dole ne shugabancin Najeriya ya koma yankin a 2027
- Da suka je gidan Sheikh Dahiru Bauchi, Yari ya ce dagewa kan cewa sai ɗan Arewa ne zai mulki Najeriya na iya yin illa ga haɗin kan ƙasar da kuma ƙarfafa rabuwar kai
- Ya yi wannan magana ne yayin da tawagar kwamitin ke ci gaba da tuntubar manyan masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar gabanin harkokin siyasa da aka saka a gaba a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Abdul’aziz Yari, ya yi magana kan batun inda shugabancin Najeriya zai fito a zaɓukan da ke tafe.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC
Yari ya gargadi ’yan Arewa da kada su dage cewa dole ne shugabancin ƙasar ya koma yankin Arewa a babban zaɓen da ke tafe.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa Yari ya ce irin wannan matsaya na iya kawo cikas ga haɗin kan Najeriya idan aka mayar da shugabanci a matsayin abin da dole sai wani yanki ne ya mallake shi.
Gargadin Yari ga 'yan Arewa
Yari ya yi magana ne a ranar Lahadi yayin da yake magana da wasu fitattun malaman addinin Musulunci a gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ke Jihar Bauchi.
Sanata Yari ya ce idan aka dage cewa babu wanda zai mulki Najeriya sai ɗan Arewa, hakan zai iya raba ’yan ƙasar.
Ya ce ya kamata a riƙa bai wa shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar damar jagoranci domin tabbatar da haɗin kai da daidaito.
“Idan muka ce babu wanda zai mulki Najeriya sai ɗan Arewa, mun raba kanmu ne.
“Yana da muhimmanci mu kasance tare a matsayin ƙasa mai haɗin kai, domin shugabanni su riƙa fitowa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Kara karanta wannan
Kwankwaso da Obi sun zo da wani tsari da zai iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027
“A Najeriya, mun fara gano yadda za mu kiyaye haɗin kanmu da daidaito, wato shugabanci ya riƙa zuwa daga sassa daban-daban na ƙasar.
“Idan aka zaɓi shugaban ƙasa daga Arewa, sai a zaɓi wani shugaban ƙasa daga Kudu. Wannan shi ne mafita ga bambancin da ke tsakaninmu.”
'Tinubu na son Dahiru Bauchi'
Da yake magana a wajen taron, ɗan takarar gwamnan Bauchi na APC, Mohammed Abubakar, ya tunatar da malaman cewa Shugaba Bola Tinubu na ƙaunar marigayi Sheikh Dahiru Bauchi.

Source: Facebook
Muhammad Abubakar ya tuna cewa Tinubu ya je Bauchi domin jajantawa mabiyan marigayi malamin addinin bayan rasuwarsa.
Ya yi kira ga mazauna Bauchi da su sake zaɓar Tinubu tare da mara wa APC baya a dukkan matakai a babban zaɓen da ke tafe.
Tsohon gwamnan ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka yi fice wajen bayar da shawarwari da jagoranci a Jihar Bauchi.
Ga bidiyon bayanin Sanata Yari da Bashir Ahmad ya wallafa a X:
Waye na gaban goshin Tinubu?
A wani labarin, kun ji cewa mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya zama ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa masu tasiri a ƙasar.
Hakan ya fara bayyana ne tun bayan rawar da ya taka a matsayin wanda aka sanya na ɗan lokaci a matsayin abokin takarar Tinubu a shirye-shiryen zaɓen 2023.
Binciken manema labarai ya nuna cewa ya kasance ɗaya daga cikin ’yan siyasar da ke da kusanci da shugaban ƙasa a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng
