Majiyoyi Sun Tsaida Lokacin da Ake Sa Ran Tinubu Zai dawo Najeriya daga Turai

Majiyoyi Sun Tsaida Lokacin da Ake Sa Ran Tinubu Zai dawo Najeriya daga Turai

  • Mai girma Bola AHmed Tinubu zai dawo Najeriya ranar Lahadi bayan hutun kwanaki fiye da 20 a ketare
  • Ya bar kasar tun 30 ga Agusta 2026, kusan kwanaki 28 da suka wuce rabon da ya shiga ofis a Aso Rock
  • Rashin dawowarsa ya jawo tambayoyi kan tanadin Kundin Tsarin Mulki tunda babu shugaban rikon kwarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - An fara magana cewa Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya bayan hutun kwana da kwanaki da ya yi a kasashen waje.

Shugaban kasar ya tafi nahiyar Turai inda yake hutawa gabanin babban zaben da za a shiga a farkon shekara mai zuwa.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ranar Lahadi Bola Tinubu zai dawo Najeriya

Majiyoyi da ke da masaniya kan shirinsa sun bayyana wa jaridar TheCable cewa ranar Lahadi shugaban zai dawo gida.

An ce majiyoyin fadar shugaban kasar sun ce Tinubu zai koma Legas, ana sa ran zai shafe kusan mako guda a garinsa.

Kara karanta wannan

Duk da yana jam’iyyar adawa, gwamna ya fadi abin da ya sa zai goyi bayan Tinubu

Daga nan ne kuma zai wuce birnin tarayya Abuja a farkon watan Oktoba domin cigaba da aiki a ofishinsa a fadar Aso Rock Villa.

A lokutan bikin sallah, an saba ganin tsohon gwamnan na Legas ya kara kwanaki bayan an gama hutu kafin ya koma bakin aiki.

Tinubu ya bar Najeriya tun watan Agusta

Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa Landan ranar 30 ga watan Agusta kuma har ya zarce adadin kwanakin da ya dauka.

Fadar shugaban kasar ta ce ya tafi ne hutun aiki na makonni uku, daga baya kuma aka ce ya tsawaita hutun da yake yi.

A ranar 21 ga Satumba, fadar shugaban ƙasar ta sanar da cewa Tinubu ya kara wasu kwanaki da ba a bayyana adadinsu ba.

Bayan ya shafe kusan mako guda a Birtaniya, ya zarce zuwa Paris na kasar Faransa, kasar da ya saba zuwa tun ba yau ba.

Tafiyar na daga cikin hutun shekara da yake yi, wannan yana cikin dokokin aiki a Najeriya.

Babu sanarwar tafiyar shugaban kasa a hukumance

Yanzu majiyar ta ce Mai girma shugaban kasazai dawo Najeriya a karshen mako, kenan ya shafe kwanaki 28 a waje.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 7 sun hada kai domin kifar da Tinubu a 2027

Fadar ta kuma ce shugaban na ci gaba da tuntubar jami'an gwamnati a Najeriya domin jin yadda abubuwa suke tafiya.

Ta ce Tinubu yana kuma ci gaba da jagorantar harkokin gwamnati duk da kasancewarsa a can kasashen waje.

Rashin samun shugaban rikon kwarya ya jawo magana

Sai dai rashin Tinubu a Najeriya ya haifar da muhawara kan kundin tsarin mulki musamman ganin bai bada mulki ba.

Wasu suna ganin kasancewarsa a kasashen waje fiye da kwanaki 21 ya ci karo da doka, kuma ya kamata a dauki.

Musamman saboda ba a bayyana cewa ya mika ikon shugabanci ga Mataimakinsa wato Sanata Kashim Shettima ba.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a bakin aiki Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

'Yan majalisa sun fara maganar a koma aiki

Ana da labari cewa a ranar Laraba, wasu 'yan Majalisar Wakilai sun nemi Majalisar Tarayya ta dawo daga hutunta.

Sun ce hakan zai ba ta damar bincika ko Bola Tinubu ya bi tanadin kundin tsarin mulki wajen tafiya hutu a Agusta.

Kungiyar SDG ta ce ya kamata Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai su bayyana gask

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng