Tinubu Ya Roki 'Yan Najeriya Alfarma a 2027, Ya Fadi Dalilin Neman Tazarce

Tinubu Ya Roki 'Yan Najeriya Alfarma a 2027, Ya Fadi Dalilin Neman Tazarce

  • Yayin da jama'a ke korafi, shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na gyara kurakuran da gwamnatocin baya suka bari ba su gyara ba
  • Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su kara bai wa gwamnatinsa dama domin ta kammala ayyukan da ta fara, yana mai cewa zaman lafiya na dawowa
  • Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, yayin addu’a ta musamman da aka gudanar a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin gyara kurakuran da aka tara a karkashin gwamnatocin da suka gabata, yana mai cewa ya kamata a kara ba ta dama domin kammala ayyukan da ta fara.

Kara karanta wannan

Majiyoyi sun tsaida lokacin da ake sa ran Tinubu zai dawo Najeriya daga Turai

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, yayin wata addu’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Kasa da ke Abuja domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maganar kan zaman lafiya

The Cable ta rahoto shugaban ya ce zaman lafiya da ci gaba suna fara dawowa kasar, yana mai cewa Najeriya ta kai matsayin da ba za a sake kallonta a matsayin kasa mai tasowa ba bayan shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

Ya ce tafiyar Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai ta kunshi nasarori da kalubale, amma ya gode wa Allah da ya ba kasar damar kai wa wannan muhimmiyar rana.

Tinubu ya ce:

“Sakon da nake isarwa ga kasar nan a madadin Shugaban Ƙasa, Shugaban Majalisar Dattawa da dukkan mambobin Majalisar Ƙasa shi ne kada ‘yan kasa su yanke kauna.
“Zaman lafiya na dawowa kasar nan. Ci gaba na dawowa kasar nan. Al’amura za su inganta yayin da muke ci gaba da tafiya a cikin tsarin dimokuradiyya.”

Kara karanta wannan

Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

Batun gyara kurakuran baya

Tinubu ya ce ‘yan Najeriya su mai da hankali kan alkiblar gwamnatin da ke mulki a yanzu, musamman kokarin gyara kurakuran da suka taru daga gwamnatocin baya.

Ya ce akwai abubuwan da kasar ta rasa a baya da kuma damammakin da ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba, yana mai cewa gwamnatin yanzu na kokarin gyara wadannan kura-kurai.

Tajudeen Abbas
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas na bayani a wajen taro. Hoto: Tajudeen Abbas
Source: Twitter

Shugaban ya ce:

“Ina son in bayyana karara cewa Najeriya tana kan hanya madaidaiciya, akwai haske a gaba, kuma ‘yan Najeriya sun kammala yin sadaukarwar da ake bukata domin kasar ta sake zama babbar kasa.”

Ya ce:

“Ya kamata mu kara bai wa wannan gwamnati dama domin ta dawo ta kammala aikin alherin da ta fara.”

Shirin kayar da Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, na jagorantar wasu ‘yan siyasa 7 domin kokarin kayar da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

N500,000: Gwamnatin Najeriya ta shirya tattaunawa kan karin albashi

Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi ranar Alhamis, inda ya tattauna kan dabarun ‘yan adawa wajen kalubalantar Shugaban Ƙasa.

Ya ce a bangaren doka ba zai yiwu jam’iyyun adawa su hada kai su fitar da dan takara guda daya a katin zabe domin kalubalantar Tinubu ba, yana mai cewa lokaci ya wuce na irin wannan tsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng