Shugaban da Ya Nemi Mata Su Kashe Aurensu kan Zaben APC Ya Magantu
- Shugaban APC na jihar Yobe, Alhaji Muhammad Gadaka, ya janye kalamansa tare da ba da haƙuri game da kiran da ya yi wa mata su kashe aurensu idan sun hana su zaɓen APC
- Gadaka ya bayyana cewa ba ya nufin hakikanin kalaman da ya yi, illa dai barkwanci ne da wasa irin na al'adar mutanensa na Ngamo da 'yan kabilar Kare-Kare
- Tuba da janye kalaman nasa na zuwa ne bayan samun gagarumin martani da suka daga bakin al'umma da malaman Musulunci wadanda suka siffanta kalaman da rashin da'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Damaturu – Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, ya janye kalaman da ya yi a baya tare da neman gafarar jama'a kan zaben 2027.
Ya janye maganar ne bayan shawara da ya ba wa matan aure da su rabu da mazansu idan har sun hana su zaɓen APC a zaɓe mai zuwa.

Source: Facebook
Gadaka ya sauya matsayarsa ne ta hanyar wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 42 da Darakta Janar na Yaɗa Labarai na Gwamna Mai Mala Buni, Mamman Mohammed, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Yayin da yake jawabi a garin Nangere, Gadaka ya ƙalubalanci mata da su kashe aurensu idan mazansu ba su bar su sun zaɓi APC ba, inda har ya yi alƙawarin biyan sadaki ga duk matar da ta ɗauki wannan mataki.
Ya ce:
"Kalamai na wasa ne kawai irin na al'ada kuma ko kaɗan ba su wakiltar manufofin da nake tsaye a kansu ko kuma nufin ƙarfafa mutuwar aure tsakanin ma'aurata ba. Ina ba da haƙuri kan kalaman da na yi, kuma na janye su baki ɗaya."
An soki shugaban APC
Kalaman na sa sun haifar da fusata da gagarumin suka a tsakanin mazauna jihar, gami da malamai wadanda suka siffanta shi da neman rushe mutuncin aure a Musulunci.
Bayan fitiwar bidiyon na tuba, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun ci gaba da nuna mamaki da suka kan irin waɗannan kalamai da shugabannin siyasa ke yi a fili yayin kamfe.
Gafara da janye kalaman nasa sun sanya mutane da dama yin tambayoyi kan dalilin da zai sa gogaggen ɗan siyasa ya yi irin waɗannan kalamai marasa kyau a taron jama'a.
Ba bayanin da ya yi a bidiyon da Sulaiman Uwais Idris ya wallafa a X:
Batun nasarar APC a Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa ya yi watsi da ikirarin Peter Obi da Dr Rabiu Kwankwaso na cewa za a iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Musa ya nuna kyakkyawan kwarin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta ci gaba da riƙe karagar shugabancin ƙasa tare da lashe zaɓen gwamna da sauran muƙamai a jihar Kaduna da sauran sassan ƙasar.
Ministan ya jaddada cewa maganar rashin farin jinin jam'iyya mai mulki a Arewa ra'ayin mutane ne kawai na kashin kai, amma jam'iyya mai ci tana tsaye wajen tabbatar da nasara a zaɓe mai zuwa.
Asali: Legit.ng

