Kwana Ya Kare: An Yi Jana'izar Tsohon Gwamnan da Allah Ya Yi Wa Rasuwa

Kwana Ya Kare: An Yi Jana'izar Tsohon Gwamnan da Allah Ya Yi Wa Rasuwa

  • An yi jana'iza tare da birne tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris a makabartar Gudu da ke Apo a birnin tarayya Abuja
  • Idan baku manta ha Ibrahim Idris ya rasu yana da shekaru 77 bayan fama da rashin lafiya a kasar Birtaniya
  • Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo da tsoffin gwamnoni Yahaya Bello da Idris Wada sun halarci jana’izar marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An yi jana’izar tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, a makabartar Gudu da ke Apo, Abuja, bayan an dawo da gawarsa Najeriya daga Birtaniya.

Marigayi Ibrahim Idris ya rasu yana da shekaru 77 a Birtaniya ranar Lahadi da ta gabata bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Ibrahim Idris.
Gwamna Ahmed Ododo, Yahaya Bello d wasu manyan mutane a wurin jana'izar tsohon gwamnan Kogi, Ibrahim idris Hoto: Umar Habib Muhd
Source: Facebook

Manyan mutane sun halarci jana'iza

Tashar Channels tv ta ruwaito cewa mutanen da suka halarci jana’izar sun haɗa da Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo; tsoffin gwamnoni Yahaya Bello da Idris Wada; ’yan gidan marigayin, jami’an gwamnati, abokan siyasa da sauran su.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 61, an ceto shugaban ƙaramar hukumar da ya fada tarkon yan bindiga

Ibrahim Idris ya zama gwamnan Jihar Kogi a shekarar 2003, sannan ya ci gaba da riƙe mukamin har zuwa watan Janairu 2012.

Ya koma kan kujerar gwamna bayan ya sake lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a watan Maris na 2008, bayan ƙalubalantar sakamakon zaɓen shekarar 2007 a kotu.

Idris Wada ne ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar a watan Janairu 2012.

Gwamnatin Kogi ta karrama Ibrahim Idris

Bayan rasuwar Ibrahim Idris ranar Lahadi, Gwamna Ododo ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki domin girmama tsohon gwamnan.

Ododo ya kuma bayar da umarnin sauke tutocin Najeriya da na Jihar Kogi zuwa rabi a dukkanin ofisoshin gwamnati da sauran wuraren gwamnati da aka ware a jihar.

Gwamna Ododo ya sanar cewa za a yi wa marigayin jana’izar girmamawa, inda Gwamnatin Jihar Kogi za ta ɗauki nauyin kuɗaɗen jana’izar da shirye-shiryenta.

A cikin wasiƙar ta’aziyya da ya aika wa iyalan Idris, Ododo ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Jihar Kogi da Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi alhini da Allah ya yi wa tsohon shugaban hukumar alhazai rasuwa

Ya ce tsohon gwamnan ya sadaukar da wani muhimmin ɓangare na rayuwarsa wajen hidimar jama’a.

Gwamnan ya ce gwamnatin Idris ta aiwatar da matakan inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman fannoni, lamarin da ya taimaka wajen ci gaba da bunƙasar hukumomin jihar.

Ibrahim Idris.
Tsohon gwamnan jihar Kogi da ya rasu, Marigayi Ibrahim Idris Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Tarihin rayuwar Ibrahim Idris

An haifi Ibrahim Idris a shekarar 1949 a Idah, Jihar Kogi. Ya fara karatun firamare a Onitsha, Jihar Anambra, kafin ya kammala karatunsa na firamare a Kano.

Daga bisani ya halarci King’s Commercial College da ke Buguma, Jihar Rivers, sannan ya samu digirin farko a fannin Shari’a daga Jami’ar Abuja.

Kafin ya shiga siyasa, Idris ɗan kasuwa ne, kuma ya kafa Ibro Trading Company wadda ke da harkokin gine-gine, kera kayan ɗaki da harkokin otal.

Tinubu ya aika sakon ta'aziyya

Kun ji cewa Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris

Tinubu ya yaba da gudunmawar tsohon gwamnan wajen ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya da kuma shekarun da ya shafe yana yana hidima

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262