Wike Ya Ture Manyan APC Gefe wajen yi wa Tinubu Muhimmin Aiki a 2027

Wike Ya Ture Manyan APC Gefe wajen yi wa Tinubu Muhimmin Aiki a 2027

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce zai kaddamar da tawagar yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a Abuja da Rivers
  • Wike ya bayyana cewa shi da magoya bayan Tinubu daga bangarorin siyasa daban-daban sun shirya fara gangamin neman kuri'u a zaben 2027
  • Ministan ya kuma ce ayyukan raya kasa da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa a Abuja za su taimaka wajen samun goyon bayan jama'a a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da cewa zai kaddamar da tawagar yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Abuja da jihar Rivers, tare da jagorantar tawagar da kansa.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Chikuku, wata al'umma da ke kan hanyar Kuje-Gwagwalada, Abuja, bayan duba aikin fadada hanyar Kuje-Gwagwalada.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana so Tinubu ya hakura da shiga takarar zaben 2027

Nyesom Wike da Bola Tinubu
Nyesom Wike tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Lere Olayinka
Source: Twitter

Wike zai jagoranci gangamin Tinubu

Vanguard ta rahoto cewa Wike ya ce jam'iyyu daban-daban na shirya kansu domin tunkarar zaben 2027, yayin da magoya bayan Tinubu daga bangarorin siyasa daban-daban suka kammala shirye-shiryensu.

Ya ce nan ba da jimawa ba zai kaddamar da tawagar yakin neman zaben Tinubu a Abuja da Rivers, kuma shi ne zai jagorance ta.

Wike ya ce:

"APC mai mulki, a ganina, tana hada kanta domin fara gangamin yakin neman zabe mai karfi. Mu da muke goyon bayan Shugaban Ƙasa daga bangarorin siyasa daban-daban, mun shirya tsarinmu domin fara aiki gaba daya.
"Nan ba da jimawa ba zan kaddamar da tawagar yakin neman zaben Tinubu a Abuja da Rivers, kuma ni zan jagorance ta. Dukkan bangarorin APC sun shirya, Shugaban Ƙasa ya shirya, mu ma mun shirya."

Magana kan ayyukan Tinubu

Ministan ya yi magana kan masu sukar gwamnatin da abokan hamayyarta, yana mai cewa ayyukan raya kasa da ake gani a Abuja za su taimaka wajen samun goyon bayan jama'a.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 7 sun hada kai domin kifar da Tinubu a 2027

Wike ya ce mutane suna farin ciki da ayyukan da ake gudanarwa, yana mai cewa hakan zai jawowa Tinubu kuri'u a lokacin zabe.

Rahoton NAN ya nuna cewa ya ce,

"Mutane suna farin ciki, kuma ban san wanda zai tsaya takarar Shugaban Ƙasa ya sha gabansa ba a wannan zaben. Wannan shi ne mulki, kuma abin da jama'a suke bukata ke nan. Hakan zai jawo mana kuri'u."

Wike ya kuma ce ayyukan samar da abubuwan more rayuwa da gwamnatin Tinubu ke yi za su taimaka wajen samun goyon baya ga 'yan takarar APC a Abuja, ciki har da Sanata Philip Aduda da 'yan takarar kujerun Majalisar Wakilai biyu na Abuja.

Nyesom Wike da Bola Tinubu
Nyesom Wike na gaisawa da shugaban kasa Bola Tinubu. Hoto: Lere Olayinka
Source: Twitter

APC ta soki Atiku kan zaben 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta gargadi 'yan Najeriya kan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, wanda ke neman takarar Shugaban Ƙasa a 2027 karkashin ADC.

Mai magana da yawun APC na kasa, Felix Morka, ya zargi Atiku da alaka da wasu batutuwan cin hanci da rashawa, ciki har da batun aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da badakalar Siemens.

APC ta kuma soki alkawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa hakan na iya shafar kudin ajiyar kasar waje, yayin da ta danganta tsofaffin kalaman tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo kan Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng