"Zan Iya Rantsewa," Tsohon Gwamna Ya Ce Bai Taba Ganin Shugaba Mai Tsari kamar Tinubu ba
- Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya ce bai taɓa ganin shugaban ƙasa mai kyakkyawan shiri ga Najeriya kamar Bola Tinubu ba
- Masari ya soki masu cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi komai ba, yana mai cewa dama irinsu ba za a taba masu daidai ba
- Ya buƙaci mata masu wa’azi su yi amfani da tasirinsu wajen dakile kalaman rarrabuwar kawuna gabanin 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Aminu Bello Masari, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, ya ce a kusan shekaru 40 da ya shafe yana harkokin siyasa, bai taɓa ganin shugaban ƙasa mai kyakkyawan tsari ga Najeriya kamar Bola Tinubu ba.
Tsohon gwamnan Katsina ya ce mutanen da ke cewa Shugaba Tinubu bai yi komai ba suna maimaita irin sukar da aka yi wa gwamnatocin baya.

Kara karanta wannan
Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta

Source: Twitter
Masari ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya bazu a ranar Talata, wanda HM Arewa, wata kafar yaɗa labarai da ke watsa labarai da Hausa, ta wallafa a Facebook.
Masari ya dora Tinubu a gaban kowa
A cikin bidiyon, Masari na magana da wasu mata a wani taron jama’a da aka ce an gudanar da shi a Kaduna a baya-bayan nan.
“Ko rantsuwa aka bani, a yan shekaruna kusan shekaru 40 da na shafe ina harkokin siyasa, ni inga shugaban ƙasa da ya zo da tsari wanda zai fitar da kasar nan daga kangi, ban gan shi ba.
Ya kawo misalin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, inda ya ce bayan Obasanjo ya kammala wa’adinsa na farko na shekaru huɗu, masu sukar gwamnati sun fara zargin nuna bambancin yanki da kabilanci.
Masari ya dauki tarihin sukar gwamnati
Masari ya ce an yi irin wannan suka ga gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, yana mai cewa ana maimaita irin wannan a ƙarƙashin Tinubu.
“Mutanen da ke cewa Bola Ahmed Tinubu bai yi komai ba, su ne mutanen da ba sa ganin darajar mutum idan yana yin abin kirki, su dama ba wanda ya taba yin daidai sai su.
“Idan muka ɗan duba tarihinmu, za mu ga cewa a shekarar 1999, bayan Obasanjo ya kammala wa’adinsa na farko na shekaru huɗu, mutanen nan sun fito da batun nuna bambancin yanki da kabilanci.
“Sun yi irin wannan abu ga Goodluck Jonathan, kuma abin da suke yi kenan a yanzu. Waɗanda ke cikinsu da har yanzu suke raye, tare da waɗanda suka raina da irin wannan tunani, su ne ke bayan wannan abu.”
- Aminu Bello Masari.

Source: Twitter
Masari ya tabo maganar addini
Masari ya ƙara da cewa wasu daga cikin masu sukar gwamnati na ƙoƙarin tayar da batun addini, kamar dai kowane addini na wata ƙabila ce kaɗai.
“Abin da ke ba ni mamaki game da mutanenmu idan suna magana kan addini shi ne, wai shi addini nan cewa aka yi Bahaushe ne? Ko cewa aka yi Bayerabe ne? Ko cewa ska yi Inyamuri ne?” ya tambaya.
Ya roƙi malamai mata masu wa’azi da su yi amfani da tasirinsu wajen hana kalaman da ke raba kan jama’a yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan
Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC
Ma'ikata sun huro wa Tinubu wuta
Kun ji cewa kungiyar NLC da kungiyoyin ma'aikatan gwamnati sun bukaci Bola Tinubu ya rage farashin fetur zuwa N500 a kowace lita sannan a maida mafi karancin albashi zuwa N500,000.
Ma'aikatan sun ba gwamnatin tarayya wa'adin zuwa Laraba, 30 ga watan Satumba, 2026, domin daukar mataki kan buqatunsu saboda tsananin halin matsin lamba.
Asali: Legit.ng
