'Dole Ku Kawo Yankunanku ga APC': Gwamna Ya Yi Barazana ga Ciyamomi

'Dole Ku Kawo Yankunanku ga APC': Gwamna Ya Yi Barazana ga Ciyamomi

  • Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya umarci sababbin shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar APC ta lashe yankunansu
  • Nwifuru ya ce ba barazana yake yi wa jam’iyyun adawa ba, sai dai ya tabbatar da cewa APC za ta yi nasara a dukkan zaɓukan jihar
  • Gwamnan ya kuma bukaci shugabannin su sasanta da abokan hamayyarsu, yayin da ya nemi a ba mata da matasa damar samun naɗin mukaman gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ba sababbin shugabannin ƙananan hukumomin jihar kan zaben 2027.

Nwifuru ya umarci ciyamomin da aka rantsar da su su tabbatar APC ta lashe yankunansu a babban zaɓen 2027.

Gwamna ya yi barazana ga ciyamomi kan zaben 2027
Gwamna Francis Nwifuru yana jawabi a Abakaliki na Ebonyi. Hoto: Hon. Francis Nwifuru.
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin rantsar da su bayan zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar 22 ga Agusta 2026, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan da ake zargi da shirya wa Tinubu juyin mulki ya fita a APC

Barazanar da Gwamna Nwifuru ya yi

Ya ce duk shugaban ƙaramar hukumar da ya gaza tabbatar da nasarar APC a yankinsa a zaɓen 2027 za a cire shi daga mukaminsa.

Nwifuru ya bayyana cewa umarnin nasa ba barazana ba ce ga jam’iyyun adawa, sai dai nuna jajircewarsa wajen kare APC da tabbatar da nasararta.

A zaɓen, APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 13 da kuma kujerun kansiloli 171 da aka fafata a jihar.

Nwifuru ya ce yayin da aka fara yakin neman zaɓen kujerun Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ana sa ran shugabannin za su tattara goyon bayan jama’a domin APC.

Ya ce:

“Ba za mu bar ko kujera ɗaya ga wata jam’iyyar siyasa ba. Za mu lashe kashi 100 cikin 100 na babban zaɓe. Ku je ku gaya wa ‘yan adawarmu cewa babu wanda ke yi musu barazana.”
An gargadi ciyamomi game da zaben 2027
Taswirar jihar Ebonyi da aka gudanar da zaɓen kananan hukumomi. Hoto: Legit.
Source: Original

Alfaharin da Gwamna Nwifuru ya yi kan zaɓe

Nwifuru ya ce an fara yakin neman zaɓe kuma APC ba za ta yi wa abokan hamayya barazana ba, sai dai za ta kayar da su a rumfunan zaɓe.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ce"; Kwamishina ya yi barazanar guntile 'yan yatsun masu adawa da APC

Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk shugaban ƙaramar hukumar da ya gaza kawo nasara wa APC a yankinsa zai fuskanci cirewa daga mukaminsa.

Ya ce:

“Yanzu mun fara yakin neman zaɓe. Ba barazana muke yi muku ba; za mu kayar da ku a rumfunan zaɓe. Babu wanda ke yi muku barazana. Mu ‘yan siyasa ne. Dole ne mu yi wa jam’iyyarmu magana kuma mu tabbatar da nasarar jam’iyyarmu.
“Idan muka yi nasara, kuma kun san za mu yi nasara, za mu cire duk shugaban ƙaramar hukumar da bai lashe ƙaramar hukumarsa ba. Hakan ne kawai.”

Sai dai ya umarce su da su tattauna da abokan hamayyarsu tare da sasanta da mutanen da suka fafata da su a zaɓen ƙananan hukumomi, cewar Daily Post.

Gwamnan ya kuma shawarci shugabannin da kada su ɗauki abokan gabansa a matsayin abokan gaba, yana mai cewa ba lallai ne abokin gabansa ya zama nasu abokin gaba ba.

Dan minista ya zama ciyaman a Ebonyi

An ji cewa Osborn Nweze Umahi, ɗan Ministan Ayyuka David Umahi mai shekaru 28, ya zama zababben shugaban ƙaramar hukuma.

Kara karanta wannan

Daraktan yakin neman zaben Tinubu, Abdulaziz Yari ya yi magana kan dawo da tallafin fetur

Umahi ya yi takarar kujerar shugaban Ohaozara ƙarƙashin APC, inda ya yi alkawarin fifita gaskiya, ingantaccen aiki da samar da ci gaba.

Bayan nasararsa, Umahi ya sha alwashin barin albashi da alawus ɗinsa gaba ɗaya, tare da mai da hankali kan ci gaban matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.