Wata Sabuwa: Ana So Tinubu Ya Hakura da Shiga Takarar Zaben 2027

Wata Sabuwa: Ana So Tinubu Ya Hakura da Shiga Takarar Zaben 2027

  • Jam’iyyar APM ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya janye daga takarar shugaban kasa ta 2027 tare da goyon bayan dan takararta,Seyi Makinde
  • APM ta zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen samar da shugabanci mai inganci, tare da sukar manufofinta kan tattalin arziki da tsaro
  • Jam’iyyar ta kuma soki rashin halartar Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APM ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2027 tare da mara wa dan takararta, Gwamnan Oyo Seyi Makinde, baya.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Abubakar Yusuf, ya fitar ranar Juma’a, inda ta zargi gwamnatin Tinubu da rashin samar da shugabanci mai inganci.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 7 sun hada kai domin kifar da Tinubu a 2027

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya a lokacin da ya karbi shaidar lashe zaben fitar da gwani na APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

APM na so Tinubu ya janye takara

The Cable ta rahoto cewa Abubakar Yusuf ya ce APM ta yi imanin cewa Tinubu bai nuna cikakken karfin jagorancin da ake bukata wajen tafiyar da Najeriya ba.

Ya zargi Shugaban da mika wasu ayyukan gwamnati ga wasu mutane da ba zababbun jami’ai ba, ciki har da ’yan uwa da masu taimaka masa.

Yusuf ya kuma soki rashin halartar Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilci Najeriya tare da gabatar da jawabin kasar.

Jam’iyyar ta soki Tinubu kan tsaro

APM ta kuma ce rashin halartar Shugaban Ƙasa a wasu tarurrukan shugabannin duniya na rage damar Najeriya na bayyana muradunta a matakin kasa da kasa.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa Tinubu bai kai ziyara kai tsaye ga wasu al’ummomin da hare-haren ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka shafa ba.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

Yusuf ya ce:

“Shugaba Tinubu bai taba nuna kudurin da karfin jagoranci daga gaba a matsalolin tsaro ba. A duk lokacin da aka kai hari, fadar shugaban kasa kan fitar da sanarwa, ta ba da umarni ko ta aika da tawaga maimakon Shugaban ya kai ziyara kai tsaye.”

APM ta soki manufofin tattalin arziki

Jam’iyyar ta kuma soki manufofin gwamnatin Tinubu da suka hada da cire tallafin man fetur, sauye-sauyen haraji da karbar basussukan kasashen waje.

Yusuf ya ce wadannan manufofi sun taimaka wajen kara tsadar rayuwa tare da janyo wasu kamfanoni su rufe ko su fice daga Najeriya.

Gwamna Seyi Makinde
Dan takarar APM, Seyi Makinde. Hoto: Oyo State Government
Source: Facebook

Ya kuma yi zargin cewa bashin Najeriya ya kai N159.28trn, yana mai cewa ba a ga yadda aka yi amfani da dukkan kudin da aka karba ba.

Jam’iyyar ta bukaci Tinubu ya sake duba kudurinsa na neman wa’adi na biyu, ya janye takararsa tare da goyon bayan Makinde.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Korafin Buba Galadima kan 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa jigon jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya ce Allah da Shugaba Bola Tinubu ne kadai suka san abin da zai faru a zaben shugaban kasa na 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya tattauna kan shirye-shiryen NDC da tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Ya kuma nuna shakku kan gudanar da zaben cikin ’yanci da adalci, yana mai cewa wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar kasar sun jawo damuwa a tsakanin ’yan adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng