Shin da Gaske Sheikh Gumi Ya Yi Barazanar Hargitsa Najeriya kan 'Yan Bindiga? An Gano Gaskiya
- Wani bidiyo ya yi ikirarin cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi barazanar “hargitsa Najeriya” idan wani abu ya faru da ’yan bindiga
- An gudanar da sahihin bincike domin gano gaskiyar cewa ko sanannen malamin addinin Musuluncin ya yi wannan maganar
- Binciken da aka gudanar ya gano sahihiyar muryar da ke cikin bidiyon wanda aka yada na malamin addinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kaduna Najeriya - Wani bidiyo da ke yawo sosai a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi kan 'yan bindiga.
A cikin bidiyon an ce Sheikh Ahmad Gumi ya yi barazanar tada rikici a Najeriya idan aka cutar da ’yan bindiga.

Source: Facebook
Bidiyon da wani shafin Facebook mai suna @Young sunny001 ya wallafa yana amfani da tsarin raba allo, inda aka nuna hotunan Sheikh Gumi tare da wasu abubuwan gani da Deepfakeaka ɗora a kai.

Kara karanta wannan
Da gaske shugaban Majalisar dattawan Najeriya ya fice daga jamiyyar APC? An gano gaskiya
A cikin bidiyon, an ji wata murya da aka danganta da malamin tana cewa:
“Ku gwada ku gani idan wani abu ya faru da ɗan bindiga, zan hargutsa wannan ƙasa baki ɗaya.”
Ya zuwa ranar 1 ga Satumba 2026, bidiyon ya samu sama da mutane 1,000 da suka yi masa like, fiye da 1,000 da suka yada shi, da kuma sama da sharhi 150.
Wasu daga cikin masu kallon bidiyon sun yi amanna cewa maganar gaskiya ce saboda yadda Sheikh Gumi ya sha yin kalamai kan batun ’yan bindiga a baya.
Bincike ya gano cewa ikirarin ƙarya ne
Binciken da FactCheckHub ta gudanar ya tabbatar da cewa ikirarin ƙarya ne.
An gudanar da binciken hotunan bidiyon ta hanyar amfani da reverse image search domin gano ainihin inda hotunan da aka yi amfani da su suka fito.
Binciken bai gano wani sahihin faifan bidiyo ko hirar kafar watsa labarai da ta dace da muryar ko kalaman da aka ji a cikin bidiyon ba.
Haka kuma, bincike mai zurfi da aka gudanar a manyan kafafen yaɗa labarai da rumbunan bayanai bai gano wani rahoto da ke cewa Sheikh Gumi ya yi irin wannan barazana ba.
An gano cewa da ace malamin ya yi irin wannan magana mai matuƙar muhimmanci, da akwai yiwuwar manyan kafafen yaɗa labarai sun bayar da rahoto a kanta.
An gano an ƙirƙiri muryar da AI Domin tabbatar da sahihancin bidiyon, an gudanar da binciken fasaha na musamman ta amfani da manhajojin gano bidiyon bogi da aka ƙirƙira da fasahar AI.
An yi bincike kan bidiyon da aka ce na Gumi ne
Binciken da aka yi ta amfani da AI Aware’s Detection Tool ya nuna cewa bidiyon an ƙirƙire shi ne da fasahar AI.
Masu binciken sun kuma cire sautin muryar daga bidiyon, sannan suka yi amfani da Resemble AI domin bincikar sahihancinsa.
Sakamakon binciken ya nuna cewa akwai kashi 86.9 cikin 100 na tabbacin AI cewa muryar da ke cikin bidiyon ba ta ainihi ba ce.
Muryar Sheikh Gumi ce aka kwaikwaya Binciken fasaha ya tabbatar da cewa muryar da ke cikin bidiyon wani kwaikwayon murya ce da AI ta samar, wadda aka ɗora a kan hotunan bidiyon da aka gyara.
Kayan aikin binciken ya gano cewa muryar ba ta da yanayin sautin ɗan Adam na yau da kullum, musamman yayin ihu, inda aka lura da wasu alamomin sauti na na’ura.

Source: Facebook
Hukuncin binciken
An yanke hukuncin cewa ikirarin da ke cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi barazanar “hargitsa Najeriya” idan wani abu ya faru da ’yan bindiga ƙarya ne.
Binciken dijital ya tabbatar da cewa an yi amfani da muryar AI da aka kwaikwaya domin ƙirƙirar wata magana da malamin bai yi ba, sannan aka ɗora muryar a kan hotunan da aka gyara.
Matsayar Sheikh Gumi kan auren gata
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya kare amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da auren gata.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa yin hakan wani bangare ne na halastaccen kuma nagartaccen shugabanci a jihar da ke tafiyar da harkokinta bisa Shari’a.
Asali: Legit.ng

