Kano: Bayan DSS Ta Cafke Dan Bilki, Kotu Ta Dauki Mataki Kan Zargin Cin Zarafin Kwankwaso

Kano: Bayan DSS Ta Cafke Dan Bilki, Kotu Ta Dauki Mataki Kan Zargin Cin Zarafin Kwankwaso

  • Yayin da ruguntsumin siyasa ke kara kamari a Kano, kotu ta dauki mataki kan fitaccen dan siyasa, Dan Bilki Kwamanda
  • Kotun Majistare a jihar ta ba da umarnin tsare Kwamanda kan zargin cin zarafi ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso
  • Daga bisani ya bukaci neman beli, yayin da kotun ta dage ci gaba da sauraran karar har ranar 29 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Kotun Majistare da ke Kano ta tsare Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda kan kalaman batanci ga Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kotun ta tsare fitaccen dan siyasar ce kan kalaman nasa wadanda suka kasance barazana ga tsohon gwamnan da kuma neman ta da husuma a jihar.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon hadimin Buhari ya bayyana abun da dinkewar Kwankwaso da Ganduje ke nufi ga PDP

Kotu ta dauki mataki kan Dan Bilki Kwamanda bayan neman ta da husuma
Kotu ta tsare Dan Bilki Kwamanda a gidan kaso. Hoto: DSS.
Asali: Twitter

Wane mataki kotun ta dauka kan Kwamanda?

Yayin aka bukaci neman beli, kotun ta dage ci gaba da sauraran karar har ranar 29 ga watan Janairu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan daukar wannan mataki kuwa, kotun ta ba da umarnin tsare shi a gidan kaso har zuwa ranar ci gaba da shari’ar.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar DSS ta cafke dan siyasar kan zargin neman ta da zaune tsaye a jihar.

Mene dalilin DSS na kama Kwamanda a Kano?

Wani daga cikin jam'ian DSS a jihar ya bayyana cewa sun cafke Kwamanda ne bayan samun faifan bidiyo da ya yi wanda ya ja hankalinsu.

Ya ce bayan cafke shi sun mika shi ga jami'an 'yan sanda yayin da su kuma suka gurfanar da shi a gaban kotu inda suka dauki mataki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Plateau ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24, bayanai sun fito

Har ila yau, bayan mika shi ga kotun Majistare ne ta ba da umarnin tsare shi a gidan kaso har ranar 29 ga watan Janairu.

Dan Bilki Kwamanda ya yi ci zarafin Kwankwaso

Kun ji cewa fitaccen dan a siyasar Kano, Dan Bilki Kwamanda, ya ce nan ba da jimawa ba za su kawo karshen siyasar Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kwamanda ya ce yayi mamakin yadda har Tinubu ya tsorata da Kwankwaso, wanda a cewar sa shi Sanatan matsoraci ne wanda bai kamata aji tsoronshi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel