Dan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya Ya Tafi Amurka, Ya Shiga Zanga Zanga kan Falasdinawa

Dan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya Ya Tafi Amurka, Ya Shiga Zanga Zanga kan Falasdinawa

  • Omoyele Sowore ya shiga zanga-zangar neman kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da nuna goyon baya ga Falasɗinawa a New York da ke Amurka
  • Sowore, wanda ke neman zama shugaban Najeriya a 2027, ya ce ya shiga zanga-zangar ne domin neman adalci ga Falasɗinawa
  • Fitaccen dan gwagwarmayaj ya yi Allah-wadai da abin da ya kira kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

New York - Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 kuma mai fafutukar kare dimokuraɗiyya, ya shiga zanga-zangar da aka gudanar a New York ta kasar Amurka.

Sowore ya shiga zanga-zangara nendomin neman kawo ƙarshen yaƙin Gaza da nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Sowore.
Fitaccen dan gwagwarmaya kuma dan takarar shugaban kasa a 2027, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Sowore, wanda ya wallafa wani bidiyo na kansa yana cikin masu zanga-zangar a shafin Facebook, ya ce an gudanar da zanga-zangar ne domin neman adalci ga Falasɗinawa da kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Hamas.

Kara karanta wannan

"Yanzu ne lokacin": Atiku ya sake aika sako ga 'yan Najeriya kan Shugaba Tinubu

Omoyele Sowore ya yi Allah-wadai

Sowore ya ce:

“Eh, yau a New York na shiga zanga-zangar ceto Falasdinawa (Free Palestine). Babu adalci, babu zaman lafiya! A ’yantar da Falasɗinu!
“Na yi Allah-wadai da kisan kiyashin da ƙasar Isra’ila ke yi a Gaza. Na shiga zanga-zangar ne domin bayyana cewa ’yan Najeriya suna tsayawa kan adalci da haƙƙin ɗan Adam ga Falasɗinawa.”

An gudanar da zanga-zangar ne a birnin New York na Amurka, inda ɗaruruwan masu zanga-zanga suka taru a kusa da zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a lokacin da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya isa birnin.

Mutanen da suka halarci zanga-zanga

Ƙungiyar Jewish Voice for Peace ta ce ɗaruruwan Yahudawa, Falasɗinawa, Iraniyawa da Lebanon da ke New York sun shiga wata babbar zanga-zangar adawa da yaƙi a ranar 24 ga Satumba.

Sowore, wanda shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters, ya shafe shekaru da dama yana shiga zanga-zangar tituna da fafutukar siyasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

APC ta fito da sabon gargadi game da zaben Atiku a 2027

Fafutukarsa ta fara tun lokacin da yake jami’a, lokacin da ya shiga zanga-zangar ɗalibai a Jami’ar Legas, daga bisani aka kore shi daga jami’ar, kamar yadda ya bayyana a wata hira da aka yi da shi a 2026.

Sowore.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Ya kuma bayyana cewa an kama shi sau da dama tare da samun saɓani da gwamnatoci daban-daban saboda fafutukarsa.

Ya samu karɓuwa sosai a matakin ƙasa musamman bayan ƙaddamar da zanga-zangar #RevolutionNow a 2019, wata fafutuka da ta nemi a samu sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki tare da ƙarin riƙon amana daga gwamnati.

Sowore ya yi wa yan Najeriya alkawari

Kun ji cewa dan takarar AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba.

Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba, yana mai cewa zama shugaban ƙasa ba zai shafi aurensa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262