ADC Ta Shiga Shirye Shiryen Dinke Barakar da Ta Bijiro wa Jam’iyyar a Jihohi
- Sanata Tunde Ogbeha ne ke shugabantar kwamitin sulhun da aka kafa ya warware rikicin cikin gidan ADC a fadin kasa
- Shugaban jam'iyyar na kasa, David Mark, ya ce kwamitin sasanta masu neman takara, shugabanni, da sauran ‘ya ‘ya
- ADC ta yi kira ga wadanda suka yi nasara a zaben gwani da kada su wulakanta wadanda ba a tsaida takara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar ADC ta gargadi ‘ya ‘yanta game da yin duk abubuwan da za su kawo rabuwar kai gabanin babban zaben 2027.
ADC ta yi kashedi game da yin kalamai da za su iya hura wutar rigima ko kuma a kai kara a kotu ko a yi wa jam’iyya makarkashiya.

Source: Facebook
David Mark ya rantsar da kwamitin sulhu a ADC
Shugaban ADC na kasa, David Mark ya yi wannan jan hankali a sakatariyar jam’iyyar a Abuja kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba
Sanata David Mark ya yi wannan bayani da yake rantsar da ‘yan kwamitin sasanci da kawo zaman lafiya na kasa a jam’iyyar ADC.
Shugaban jam’iyyar a Najeriya ya bukaci ‘yan kwamitin su tattauna da fusatattun masu neman takara da sauran ‘ya ‘yan da suka yi fushi.
Kwamitin sulhu zai yi aikin sasanta rigimar gida
Ana so a yi zama da duk wasu masu ruwa da tsaki da abubuwa ba su yi masu dadi ba wajen zaben tsaida gwani domin a samu mafita.
Daga wannan zama ne David Mark yake so a gano wuraren da suke yi wa ‘yan jam’iyya ciwo na hakika domin dinke baraka.
Kwamitin zai yi kokarin hana ‘yan jam’iyyar ADC yin kalaman da za su jawo rikici ko sabani da juna ko ma har a shigar da kara a kotu.
Duk da doka ta ba ‘yan jam’iyya damar shigar da kara a kotu, Mark ya ce idan za a iya yin sulhu a cikin gida, gara a fara yin hakan.

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi: Yan adawa sun fara ɗaukar matsayan da za ta iya kayar da Tinubu a zaben 2027
Wadanda ADC ta nada su shugabanci kwamitin sulhu
Jam’iyyar hammayar za ta dage wajen ganin an jawo wadanda suka rasa tikiti a karkashin kwamitin da Tunde Ogbeha yake jagoranta.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Oserheimen Osunbor shi ne mataimakin shugaban kwamitin da ya sha alwashin zai yi aiki da gaskiya.
Daily Trust ta rahoto tsohon shugaban majalisar dattawan yana bayanin yadda ya kamata kowane ‘dan APC ya zama limamin sulhu.
Ganin an kusa shiga zabe, ADC tana so ta gujewa siyasar ramuwar gayya ko ta zagon-kasa, take cewa ‘yan jam’iyyar sun zama daya.
Kwarewa da magoya baya da kuma karfin wadanda aka doke a zaben tsaida gwani zai yi wa jam’iyyar ADC amfani a babban zabe.
Ga wadanda aka ba tuta kuwa, shugaban ADC na kasa ya fada masu cewa nauyi aka ba su, kuma kar su manta abokan karawarsu.
Matsalar da NDC ta samu lokacin rajista
An ji cewa jam'iyyar NDC ta zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da hana ta lambar sirrin na daura sunayen 'yan takararta.

Kara karanta wannan
Jita jitar Opay da shahararrun labaran bogi da suka rika yawo makon jiya a Najeriya
Jinkirin ya faru ne sakamakon samun umarnin Kotun Tarayya da ke Lokoja wanda ya ba da damar soke rajistar jam'iyyar ana cikin shirye-shirye.
Mai magana da yawun NDC, Osa Director, ya jaddada cewa jam'iyyar za ta koma INEC da kuma kotu domin dakatar da aiwatar da hukuncin.
Hotunan rantsar da kwamitin daga shafin ADC a X:
Asali: Legit.ng