VeryDarkMan Ya ba Jami’an Tsaro Hakuri bayan Jifansu da Kazamar Kalma a Taro

VeryDarkMan Ya ba Jami’an Tsaro Hakuri bayan Jifansu da Kazamar Kalma a Taro

  • Dan gwagwarmaya a Najeriya, VeryDarkMan ya nemi afuwar sojoji, ’yan sanda, jami’an kwastam da shige da fice kan kalamansa
  • Ya ce ya fahimci cewa kiran jami’an tsaro a taro ya lura bai dace ba, musamman ganin yadda suke sadaukar da rayukansu
  • Mai fafutukar ya ce kalaman nasa ba su yi adalci ga jami’an da ke yaki da Boko Haram da sauran barazanar tsaro ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan TikTok, VeryDarkMan ya nemi afuwar jami'an tsaron Najeriya gaba daya bayan fadar wasu kalamai a kansu.

A yayin taron shekara-shekara na 66 na kungiyar lauyoyi da aka gudanar a Fatakwal, Rivers, VeryDarkMan ya kira sojoji da ’yan sanda “yan bindiga”.

VeryDarkMan ya ba jami'an tsaro hakuri
Dan gwagwamaya a Najeriya VeryDarkMan. Hoto: VeryDarkMan.
Source: Instagram

VeryDarkMan ya nemi afuwar ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a Facebook ranar Juma’a, bayan ya yi tunani kan jawabin da ya gabatar a taron.

Kara karanta wannan

'Ya fi kasar Belgium fadi,' Yadda girman dajin Sambisa ke zama kalubale

VeryDarkMan ya yi nadamar kalamansa kan jami'an tsaro

Ya ce daga baya ya fahimci cewa kalaman nasa sun shafi jami’an da ke kasadar rayukansu domin kare ’yan Najeriya.

“Ba na ganin na yi wa mutane da dama adalci ba, musamman a jawabin da na ce sojoji su ne ‘unknown gunmen’, ’yan sanda su ne ‘unknown gunmen’, har ma da jami’an shige da fice da kwastam.
“Na san ainihin abin da nake ƙoƙarin faɗa, domin ina da hujjojin da za su tabbatar da ikirarina, amma ban yi wa mutane da dama adalci ba a wannan jawabin."

VeryDarkMan ya bayyana cewa sukar da yake yi ta shafi zargin cin hanci, yi wa aiki zagon ƙasa da fallasa bayanan sirri da wasu jami’ai ke aikatawa.

Sai dai ya amince cewa yadda ya bayyana batun ya zama kamar yana zargin dukkan jami’an tsaro, abin da zai iya rage darajar sadaukarwarsu.

“A wancan jawabin ban yi wa mutane adalci ba, musamman sojojin da ke cikin dazuzzuka suna yaƙi da Boko Haram domin kare ƙasarmu, kare rayukanmu da kuma kare iyalanmu.”

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

- VeryDarkMan

VeryDarkMan ya yi nadamar kalamansa kan jami'an tsaro
Dan TikTok da ke kokarin ganin an yaki zalunci a Najeriya, VeryDarkMan. Hoto: VeryDarkMan.
Source: Instagram

Manufar VeryDarkMan kan kalaman da ya yi

Ya ce manufarsa ita ce shugabannin hukumomin tsaro su mai da hankali kan wasu jami’an da ake zargi da yi wa abokan aikinsu da ƙasa zagon ƙasa.

Daga bisani, mai fafutukar ya nemi afuwar Babban Hafsan Tsaron Najeriya da sauran hukumomin tsaro, tare da roƙon a isar da saƙonsa ga jami’an da ke wurare masu haɗari.

Ya kuma nemi afuwar ’yan sanda, kwastam da jami’an shige da fice, da kuma iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu yayin da suke yi wa ƙasa hidima.

Duk da haka, VeryDarkMan ya ce zargin wasu jami’an da aikata ba daidai ba bai kamata ya shafe gudunmawar jami’an da ke ci gaba da yi wa ƙasa hidima ba.

Sai dai duk da neman afuwar, VeryDarkMan ya ce zai ci gaba da magana kan jami’an da yake zargi da yi wa aiki zagon ƙasa da fallasa bayanai ga ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Janar Musa ya ce Najeriya ta yi galaba kan 'yan ta'adda, ya gabatar da dalili

VeryDarkMan ya kalubalanci yan sanda

An ji cewa VeryDarkMan ya ce ba zai mika wa ’yan sanda hujjojin zargin da ya yi cewa jami’an tsaro na taimakawa wajen sace mutane da ayyukan ’yan bindiga ba.

’Yan sandan Najeriya sun gayyaci VeryDarkMan domin ya bayyana hujjojin zargin cewa wasu jami’ai na taimaka wa masu garkuwa da mutane.

Duk da sukar hukumomin tsaro, VeryDarkMan ya ce ya kamata gwamnati ta inganta jin daɗin ’yan sanda domin ƙarfafa tsaron ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.