Duk da Yana Jam’iyyar Adawa, Gwamna Ya Fadi Abin da Ya Sa Zai Goyi Bayan Tinubu
- Alex Otti na jihar Abia ya nuna ba zai yaki tazarcen gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa ba
- Ra’ayinsa kenan a matsayinsa na gwamna da kuma mamban kwamitin tattalin arziki na kasa wato NEC
- Gwamnan Abia ya ce wasu tsare-tsaren Tinubu kamar cire tallafin man fetur sun yi daidai da ra'ayinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abia - Bisa dukkan alamu Gwamnan jihar Abia, Alex Otti yana goyon bayan takarar Bola Ahmed Tinubu ne a 2027.
Gwamna Alex Otti ya bayyana cewa yana tare da Bola Tinubu a zaben badi ne a matsayinsa na ‘dan kwamitin NEC.

Source: Facebook
Ra'ayin Alex Otti a matsayin mamba a NEC
Mai girma gwamnan ya yi wannan bayani a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin Arise a ranar Alhamis dinnan.
Akwai majalisar NEC da ke sa ido a kan harkokin tattalin arziki a karkashin jagorancin Mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba
A tsarin mulkin Najeriya, wasu gwamnonin jihohi suna cikin ‘ya ‘yan wannan majalisa.
Gwamnan Abia yana cikin wadanda ake rufe kofar NEC da su a dauki matakan da suka taba tattalin arzikin Najeriya.
Alex Otti zai bi bayan Bola Tinubu?
Alex Otti ya nuna akwai kyakkyawar fahimta tsakanin jam’iyyar LP da ta kawo shi a ofis da kuma APC mai mulki.
Gwamnan ya ce bai samu kan shi a matsayin da zai yaki takarar shugaba Tinubu ba, ya ce yin hakan zai tarwatsa al’amura.
“Yana aiki ne yadda ka fada. Ban matsayin da zan kalubalanci takarar shi.”
- Alex Otti
Otti ya ce akwai bambanci tsakanin goyon bayan gwamnatin Tinubu ya zarce da kuma goyon bayan ‘dan takaran LP a 2027.
Gwamnan Abia ya yi watsi da 'dan takaran LP
Punch ta ce an fara tambayar shi ko yana tare da takarar Tinubu, sai ya amsa da cewa suna da ‘dan takaransu a jam’iyyar LP.
Da aka nemi jin ko Tinubu ne wannan ‘dan takara, sai ya yi watsi da wannan batu.
A nan ‘dan jaridar ya nace, ya sake tambayar ko yana y, zai marasa baya a kan ADC, NDC, LP da sauran ‘yan adawa.
Otti ya masa da cewa:
Me ku ke so in fada? In ce ban goyon bayan shi?”
Gwamnan bai yaki da tazarcen shugaba Tinubu
Mista Otti wanda ake ganin farin jinin Peter Obi ya taimake shi a zaben 2023 ce Mai girma Tinubu yana da damar tsaya wa takara.
Yake cewa kuma ya zama wajibi ya bi bayan APC a zaben shugaban kasa, ya kuma ce bai yin fito na fito da shugaba Tinubu.
Ko a lokutan da ya saba masa, ya ce ya yi ne saboda gwamnati ta gyara ba don ya yi adawa da mai girma shugaban kasa ba.
Otti ya yi na'am da cire tallafin fetur
A hirar ya bada misali da yadda ra’ayinsa ya zo daya da na Tinubu, daga ciki akwai kan batun janye tallafin fetur da aka yi.
Ya soki masu ikirarin dawo da tsarin, yana ganin ba za ta yiwu a cigaba da kashe makudan kudin saboda fetur ya yi sauki ba.

Source: Facebook
Takarar Atiku ta ci karo da abin kunya
Ana da labari cewa Kingsley Moghalu ya ki karbar mukami a kwamitin tallar Atiku Abubakar saboda ba a tuntube shi ba tun farko.
Masanin tattalin arzikin kuma tsohon mataimakin gwamna a CBN ya ce ya bar siyasar jam'iyya, don haka ba zai yi wa ADC kamfe ba
Farfesa Moghalu ya samu kan shi a kwamitin tsara manufofin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ba tare da ya san an yi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

