2027: Kwankwaso Ya Yi Maganar Canza ‘Yan Takara da 'Fitinar' Sha'aban Sharada a NDC

2027: Kwankwaso Ya Yi Maganar Canza ‘Yan Takara da 'Fitinar' Sha'aban Sharada a NDC

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya zauna da wasu masu ruwa da tsaki a tafiyar Kwankwasiyya a makon nan a garin Kano
  • ‘Dan takaran mataimakin shugaban kasar ya musanta cewa NDC ta sauya ‘yan takaranta duk da ana fama da shari'a
  • Kwankwaso ya yi fatali da maganganun da ake ji cewa irinsu Sha’aban Sharadan za su yi masu takara a zaben badi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo zancen wasu ‘yan takaran majalisa na jam’iyyar NDC a jihar Kano da ake cewa an canza su.

‘Dan takaran mataimakin shugaban kasar na ADC a 2027 yana maida martani ne da aka ji su Sha’aban Sharada sun yi kara a kotu.

Kwankwaso
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Miusa Kwankwaso cikin masoyansa a Kano Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Rabiu Kwankwaso ya zauna da masu ruwa da tsaki

Tashar Express ta rahoto Rabiu Musa Kwankwaso yana nuna ba su san wane ne Hon. Sha’aban Sharada ba a cikin tafiyar NDC.

Kara karanta wannan

"Zan iya rantsewa," Tsohon gwamna ya ce bai taba ganin shugaba kai tsari kamar Tinubu ba

Madugun na Kwankwasiyya ya zargi tsohon ‘dan majalisar da kasancewa ‘dan APC wadanda suke neman kawo masu fitina a kotu.

An rahoto cewa Hon. Sharada ya shigar da kara a asirce a kotu, yana so a tsaida shi a matsayin ‘dan takaran jam’iyyar NDC a 2027.

Shararren ‘dan siyasar yana son sake zama mai wakiltar Birnin Kano a Majalisar wakilan tarayya.

An shiga rudani a Kano domin mutane suna ganin cewa Hon. Yusuf Kofar Mata aka ba tuta ya wakilci mutanen birni a majalisa.

Daily Nigerian ta ce tsohon hadimin shugaban kasar bai shiga neman takara ba kuma bai saye fam a NDC ba, amma yanzu yake son tikiti.

Sharada ya nemi takarar zama sanatan Kano ta tsakiya a APC amma bai dace ba, sai ya dawo wajen shugabannin NDC yana neman tuta.

Kwankwaso ya karyata zancen canza 'yan takara

Kara karanta wannan

Atiku ya 'tona wayau' da Tinubu yake shirin yi game da tallafin fetur

Rabiu Kwankwaso ya ce Kwankwasiyya ba ta canza ‘yan takaranta na jam’iyyar NDC a 2027 ba, har yanzu ba ta san da wani sauyi ba.

Da yake bayani a Kano, Kwankwaso ya gargadi mutanensa game da tado fitinar siyasa, ya ce su ba su tsoka rikici ana zaune kalau.

Ya ce 'yan takaransu tara suke da kara a kotu, kuma hadiminsa ya daura bidiyo a Facebook yana cewa sun dauki matakan da suka dace.

Tsohon gwamnan ya gargadi wadanda suke zuwa wajen wasu ‘yan siyasa dabam da tunanin su za su yi wa NDC takara a jihar Kano.

Gargadin da Kwankwaso ya yi wa mabiya

An ji shi ya ce:

“Ina so in fada maku cewa, yan takararmu na farko da muka tsayar, Kwankwaso ita na sani, ni su na sani.
Kuma ba mu canza ba, kuma ku ma, duk wanda ya shiga ya je wajen wani dan takara ba wanda muka fitar da shi ba, shi ma ya shiga cikin fitina wanda kuma ko a dade, ko a jima, shi ma za mu hadu da shi.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Madugun ya fada wa mabiyan nasa cewa shi ba ya yin gaba sannan ya yi baya ko da ya yi kuskure.

Kwankwaso ya kuma yi bayanin farin jinin jam’iyyar NDC, yake cewa a kullum cikin karbar ‘yan siyasa ake yi a kananan hukumomin Kano.

Ya kare da kira ga mabiya da su dage wajen tallata takarar jam’iyyar adawa ta NDC domin su sake ganain bayan gwamnati mai-ci a jihar.

Bidiyon bayanin Kwankwaso a shafin hadiminsa a Facebok, Saifullahi Hassan.

Baraka a yakin zaben Obi/Kwankwaso

An rahoto maku cewa Jabir Ibrahim Yaro ya ce ba a tuntube shi ko aka nemi izininsa kafin saka sunansa cikin kwamitin kamfen 2027 ba.

‘Dan siyasar ya yi watsi da duk wata magana da ke nuna cewa shi mamba ne a kwamiti kamfen Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso

Mallam Jabir ya ce har yanzu yana biyayya ga babban jagoransa Peter obi, kamar yadda ya fada a wata sanarwa a dandalin X a makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng