Lissafin Yadda Jam’iyyun APC da Accord Suka Yi Bindiga da Naira biliyan 100 a Zaben Osun

Lissafin Yadda Jam’iyyun APC da Accord Suka Yi Bindiga da Naira biliyan 100 a Zaben Osun

  • Bincike ya nuna APC da Accord sun kashe sama da ₦100bn wajen siyan kuri'u, biyan jami'ai da sauran harkokin zabe a Osun
  • Tsabar kudi sama da Naira biliyan 100 da jam'iyyun APC da Accord suka kashe a zaben gwamnan Osun ya karya dokar zabe
  • Kungiyar Yiaga Africa ta yi kiraye-kiraye na gaggawa ga hukumomi da su gurfanar da jam'iyyun gaba da kotu saboda saba wa ka’idoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Osun - Jam’iyyar APC da kuma Accord da ta tsaida Ademola Adeleke a zaben gwamnan Osun sun kashe sama da N10bn a takara.

An batar da makudan kudin ne wajen kayan kamfe, sayen kuri’un jama’a, sallamar wakilan jam’iyya da biyan jami’an tsaro da na zabe.

Zaben Osun
Gwamna Ademola Adeleke tare da magoya baya a zaben Osun Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

Osun: Jam'iyyun APC, Accord sun kashe N100bn

Wani bincike da jaridar Punch ta yi ya nuna yadda aka kashe wannan kudi a rumfunan zabe 3, 763 da ke mazabu 332 da ke a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

Nesa ba kusa ba, wannan kudi ya kere N3bn da aka ware cewa kowane ‘dan takara zai iya kashe wa wajen neman zabe gwamna a zabe.

Wakilan jam'iyyu sun samu kudi a zaben Osun

Wakilan da suka tsaya wa APC a rumfar zabe a Osun sun tashi da N100, 000 yayin da jam’iyyar Accord ta iya biya nata wakilan N20, 000.

Ita jam’iyyar ADC da ‘dan takaranta ya zo na uku a zaben, ta ba wakilanta N30, 000.

Sauran jam’iyyu na NDC, NNPP, APM da APGA da ae zargin jam’iyyar Accord ta shigar da su cikin zaben suma sun samu N20, 000.

Hakan yana nufin a karshe jam’iyyar Accord mai-ci a Osun ita ma ta kashe N100, 000 a duk rumfa a fadin kananan hukumomi 30 na jihar

Idan aka buga lissafin, za a ga wadannan jam’iyyu biyu sun kashe kusan N752m tun a nan.

Wakilan APC wajen tattara sakamakon zabe a kowace mazaba sun samu N120, 000. Ana hasashen su ma sun ci N39.84m wajen zaben.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

Irin kudin da kashe wa jami'an tsaro

Jami’ai daga rundunar ‘yan sanda da NSCDC da na FRSC sun ci N100, 000 da N80, 000 daga hannun APC da Accord a duk wata rumfa.

Haka zalika ma’aikatan tsaron sun samu karin wata N50, 000 daga gwamnatin jiha. Gwamnati da jam’iyya mai-ci sun kashe N865m a nan.

Duk wani babban ‘dan sanda ya samu N2m daga hannun APC, saboda haka ake tunanin jam’iyyar hamayyar ta kashe sama da N60m.

An saye kuri'un fiye da Naira biliyan 30

Wajen sayen kuri’u kuwa, an rahoto cewa APC ta ware N40, 000 ga duk mai zabe. Hakan ya sa kananan hukumomi suka ga biliyoyi.

Shugabannin APC a kananan hukumomi sun samu daga N100m har zuwa N500m domin sayen kuri’un mutane kamar 150 a duk rumfar zabe.

A wannan bangare kawai ana zargin N22.578bn ya fito daga hannun jam’iyyar APC. Akwai wata N1.1289bn da aka kashe dabam a nan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Osun ya yi wuf ya karyata ADC da ta ce sun hada kai a doke APC

A duk inda ake zabe, wasu ‘yan jam’iyyar adawar sun ce APC ta tanadi mutane 30 da za su jawo hankalin jama’a, an ba kowa N10, 000.

Su ma Accord ba a bar su a baya ba, ana zargin sun kashe N20, 000 domin su saye kuri’u kimanin 150 a duk rumfar da ake kada kuri’a.

Ban da N11.289bn da Accord ta kashe na sayen kuri’u, lissafin ya nuna ta kashe irin abin da APC ta batar a kan masu cefanen kuri’a.

Adeleke_01
Gwamna Ademola Adeleke tare da magoya baya a zaben Osun Hoto: @OyebamijiBola/@AAdeleke_01
Source: Twitter

Kira da aka kama shugabannin APC da Accord

A karshe dai jam’iyyar Accord ta yi barin abin da ba zai gaza N40bn. Ana zargin APC ta kashe tsakanin N60bn zuwa N110bn a zaben jihar.

Wannan ya sa shugaban kungiyar Yiaga Africa, Samson Itodo, ya yi kira da a kama shugabannin jam’iyyun nan saboda karya dokokin zabe.

Samson Itodo ya yi tir da yadda aka yi kaca-kaca da dokar zabe, yana mai kuma sukar sayen kuri’un mutane da aka rika yi a zaben gwamnan.

A duk lissafin nan, ba a yi maganar N150, 000 da N300, 000 da aka biya malaman zabe ba.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru ya ba 'yan Najeriya shawarar abin da za su koya daga zaben gwamnan Osun

Yayan gwamnan Osun ya yi azumin zabe

A labaran zaben Osun, an ji yadda APC ta sa mahaifin Davido ya koma yin azumi a duk mako saboda 'danuwansa ya zarce a kan mulki.

Duk dukiyar Dr Adedeji Adeleke, a karshe sai da ya rungumi Ubangiji domin ganin kaninsa, Ademola Adeleke ya cigaba da mulkin Osun har 2030.

Attajirin ya zargi tsohon gwamnan jihar Osun wanda yanzu yake minista, Adegboyega Oyetola, da kokarin yin duk mai yiwuwa wajen yakar Accord.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng