Sauki Ya Zo: NNPCL Ya Kawo Tsarin Sayen Fetur da Arha a Fadin Najeriya
- NNPC ta fara bayar da rangwamen N66 ga kwastomomin da ke amfani da NNPC Fuel App wajen sayen fetur a gidajen mai na kamfanin
- Tallafin farashin ya fara aiki ranar 1 ga Oktoba kuma zai ci gaba har zuwa ranar 7 ga Oktoban shekarar 2027
- Kamfanin ya bukaci masu ababen hawa da sauran kwastomomi su ci gaba da amfani da manhajar domin cin gajiyar rangwamen kafin lokacin ya ƙare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kamfanin Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya sanar da rangwamen N66 ga kwastomomin da ke amfani da manhajar NNPC Fuel App a gidajen man kamfanin da ke faɗin Najeriya.
Kamfanin ya ce rangwamen ya fara aiki ne ranar 1 ga Oktoba, kuma zai ci gaba har zuwa ranar 7 ga Oktoban 2026.

Source: Facebook
Kamfanin NNPCL ya bayyana rangwamen ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, 2 ga watan Oktoban 2026.
A cewar NNPCL, rangwamen na daga cikin shirye-shiryen da aka gudanar a wannan lokaci, inda aka buƙaci kwastomomi su yi amfani da manhajar wajen sayen fetur da gudanar da mu’amaloli a gidajen man kamfanin.
NNPCL ya bukaci kwastomomi su amfana
A cikin sanarwar, kamfanin NNPCL ya bukaci kwastomomi a faɗin ƙasar su yi amfani da damar.
A cewar sanarwar:
"Shirin rangwamen N66 yana gudana, kuma an riga an fara ganin farin ciki a gidajen manmu da ke faɗin ƙasar."
“A duk faɗin Najeriya, kwastomominmu suna cin gajiyar wannan dama, kuma har yanzu akwai lokaci da ku ma za ku amfana.”
An fara samun masu cin gajiyar rangwamen
NNPCL ya ce wasu kwastomomi sun riga sun fara cin gajiyar rangwamen tun ranar farko da aka fara shirin.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Kamfanin ya ce an gudanar da wasu ayyuka da suka shafi tallafin a gidajen man sa daban-daban a faɗin ƙasar a ranar farko.
Ya kuma ƙarfafa gwiwar masu ababen hawa da sauran kwastomomi da su ci gaba da amfani da NNPC Fuel App a duk tsawon lokacin da tallafin zai kasance.
Za a ci gaba da wallafa bayanan shirin
Kamfanin ya ƙara da cewa zai ci gaba da raba hotuna da bayanai daga gidajen man sa daban-daban domin nuna yadda shirin ke gudana.
“Ku ci gaba da shan mai, ku ci gaba da gudanar da mu’amalolinku, sannan ku ci gaba da bibiyar shafukanmu.” In ji sanarwar.
Kamfanin ya kuma yi kira ga kwastomomi da su yi amfani da damar rangwamen kafin shirin ya ƙare ranar 7 ga Oktoba.
Rangwamen N66 yana samuwa ne ga kwastomomin da suka yi amfani da NNPC Fuel App yayin da shirin ke gudana.

Source: Facebook
Kamfanin NNPCL ya samu riba
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin NNPCL ya ce ya samu ribar Naira tiriliyan 7.2 bayan cire haraji a shekarar 2025.
Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ya ce ribar ta samu ne daga kudaden shiga da kamfanin ya samar, wadanda suka kai Naira tiriliyan 34.5 as shekarar.
Asali: Legit.ng
