Faɗa da Hadimin Gwamna Ya Jawo Matsala, an 'Hana' Limami Sallar Juma'a
- Ana fargabar rundunar ’yan sanda ta hana Limamin Masallacin Juma’a na Owerri Imam Murtala Dahiru halartar sallar Juma’a
- Hakan ya biyo bayan wata takarda da Alhaji Yusuf Sambo ya kai wa ’yan sanda, yana ikirarin ya cire Imam Dahiru daga mukaminsa
- Majalisar Malamai da Limamai ta Enugu ta ce haramcin ya sabawa kundin tsarin mulki, inda ta bukaci a kare ’yancin ibada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Rundunar ’yan sandan Najeriya a Jihar Enugu ta hana Babban Limamin Masallacin Juma’a na Owerri, Murtala Dahiru, da wasu shugabannin Musulmi halartar sallar Juma’a.
Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Enugu ta ce matakin ya samo asali ne daga takardar korafi da Alhaji Yusuf Sambo ya kai wa ’yan sanda.

Source: Original
Sambo, wanda ake takaddama kan shugabancinsa na Sarkin Hausawan Enugu, yana kuma rike da mukamin mai taimaka wa Gwamna Peter Mbah kan ayyuka na musamman, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta
An soki yan sanda kan hana sallar Juma'a
Majalisar ta ce Sambo ya yi ikirarin cewa ya cire Imam Dahiru daga mukaminsa, amma ta ce ba shi da ikon yin hakan.
A cewar majalisar, ita ce ta nada Imam Dahiru, don haka ita ce kadai ke da ikon cire shi daga mukamin Babban Limamin masallacin.
An ce an kama malaman a ranar 30 ga Satumba, 2026, bayan sun fito daga ofishin DSS da ke Enugu, inda suka je kai takarda ga Kwamishinan ’Yan Sanda.
Majalisar ta ce DSS ta ki karbar takardar, inda ta umarce su da su kai ta ga ’yan sanda. Jim kadan bayan sun fito, ’yan sanda suka kama su.
An kai malaman sashen SIB na hedikwatar ’yan sanda da ke Enugu, inda aka nuna musu takardar korafin da Sambo ya rubuta kan lamarin.
Majalisar ta ce duk da bayanin cewa rikicin na cikin harkokin addini da na farar hula ne, ’yan sanda sun tilasta musu sanya hannu kan wata yarjejeniya.
A cikin yarjejeniyar, an bukaci malaman da sauran Musulmi su daina halartar sallar Juma’a a Masallacin Owerri Road Central har sai Sambo ya nada wani Babban Limami.

Source: Twitter
Kungiya ta yi korafi kan lamarin
Kungiyar Civil Rights Realisation and Advancement Network ta kai korafi ga Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, a madadin majalisar, cewar New Nigeria.
Shugaban kungiyar, Olu Omotayo, ya bayyana matakin ’yan sandan a matsayin wanda ya sabawa doka da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Takardar ta ce ’yan sanda sun wuce iyakokin ikonsu ta hanyar hana wasu shugabannin Musulmi halartar sallar Juma’a ba tare da umarnin kotu ba.
Majalisar ta kuma ce yarjejeniyar da aka tilasta wa malaman rubutawa ta hana su halartar sallar Juma’a, kuma hakan ya sabawa doka da kundin tsarin mulki.
Malaman sun bayyana cewa ’yancin gudanar da ibada na cikin hakkokin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ’yan kasa.
Sun bukaci Kwamishinan ’Yan Sandan Enugu ya janye dokar nan take, tare da barin Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.
Majalisar ta jaddada cewa batun rikicin na farar hula da na addini ne, ba batun aikata laifi ba, sannan ta nemi gaggawar shiga tsakani.
Ta kuma yi kira da a hana lamarin haifar da rikicin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da bin doka a jihar Enugu, cewar Sahara Reporters.
Majalisar ta ce tana Allah wadai da kama da tsare ’yan kasar, tare da bukatar a janye dokar da ta hana Musulmin halartar sallar Juma’a daga ranar 2 ga Oktoba, 2026.
A wata takarda da aka aika wa Kwamishinan ’Yan Sanda, majalisar ta tambayi ko Sambo, wanda ba mamba ba ne a cikinta, yana da ikon cire Babban Limami da kansa.
Ta kuma tambayi ko Sambo yana da ikon neman a kama Limamin a Sashen Binciken Manyan Laifuka domin a cire shi daga mukaminsa yayin da yake tsare.
Majalisar ta ce ’yan sanda ba su da ikon kama Limami idan babu wani laifi da ake zarginsa da aikatawa, tana zargin cewa batun na da nasaba da siyasa.
Ta dage cewa Imam Murtala Dahiru ne halastaccen Babban Limamin Masallacin Juma’a na Owerri Road Central, tare da kira ga Sambo da magoya bayansa su janye korafin.
Yan bindiga sun hana sallar Juma'a
An ji cewa matsalar tsaro na kara jefa rayuwar mutane cikin hadari a wasu sassan jihar Katsina duk da ana cikin watan azumin Ramadan.
Rahoto daga yankunan Musawa, Kankara da Malumfashi ya nuna cewa akalla kauyuka 10 ba su samu damar fita sallar Juma'a da ta gabata ba.
Mazauna yankin sun roki gwamnati da ta kawo masu dauki, suna mai cewa an ci gaba da kai masu hare-hare duk da sulhun da aka yi.
Asali: Legit.ng


