Muhimman Abubuwan Sani 11 kan Jihar Osun yayin da Ake Gudanar da Zaben Gwamna
- Zaben gwamnan Osun na ranar Asabar, 15 ga Agusta, ya zo yayin da jam’iyyun siyasa ke kammala yakin neman zabensu, lamarin da ya kara zafafa siyasar jihar
- Fafatawar ta fi karkata ne tsakanin ‘yan takara uku, yayin da wasu jam’iyyu da ‘yan siyasa suka janye burinsu domin mara wa manyan ‘yan takarar baya, musamman Bola Oyebamiji na APC
- Osun na da kananan hukumomi 30 da mazabu 3,763, yayin da zaben na Asabar zai kasance karo na takwas da aka gudanar na gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Zaben gwamnan jihar Osun ya zo, yayin da ake samun karuwar zafin siyasa a fadin jihar gabanin zaben da za a gudanar a ranar Asabar, 15 ga Agusta.
Zaben zai kasance karo na biyu cikin zabukan gwamnonin jihohin da ake gudanarwa ba tare da bin tsarin babban zabe ba a Najeriya a bana, bayan jihar Ekiti ta gudanar da nata a watan Yuni.

Source: Original
Legit Hausa ta yi duba kan wasu muhimman abubuwan sani dangane da jihar Osun da ke yankin Kudu maso Yamma.
Abubuwan sani kan jihar Osun
Fafatawar ta fi zafi ne tsakanin ‘yan takara uku, yayin da wasu jam’iyyu da masu ruwa da tsaki a siyasa suka ajiye burinsu tare da goyon bayan manyan ‘yan takarar, musamman Bola Oyebamiji na All Progressives Congress (APC).
Ga wasu muhimman abubuwan sani kan jihar Osun:
1. Yadda aka kafa jihar Osun
An kafa jihar Osun ne a ranar 27 ga Agusta, 1991, a lokacin mulkin soja na Ibrahim Babangida. An cire ta daga jihar Oyo a wani babban aikin samar da sababbin jihohi da Najeriya ta gudanar, cewar rahoton Premium Times.
A wannan shekarar, adadin jihohin Najeriya ya karu daga 21 zuwa 30, bayan gwamnatin soja ta kirkiro sababbin jihohi tara.
Sauran jihohin da aka kirkira a lokacin sun hada da Abia, Anambra, Delta, Enugu, Jigawa, Kebbi da Yobe.
Osogbo, wani muhimmin birnin kasuwanci, shi ne babban birnin jihar Osun.
2. Sunan jihar da taken ta
Taken jihar a hukumance shi ne “Land of Virtue”, wato “Ƙasar Nagarta”.
Ana kuma yawan kiran Osun da “Jihar Ruwan Rai”, saboda kogin Osun da jihar ta samo sunanta daga gare shi.
3. Gwamnan da ke mulkin Osun
Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord ne ke mulkin jihar a yanzu. An rantsar da shi a ranar 27 ga Nuwamba, 2022, bayan ya doke Gboyega Oyetola, wanda yake kan kujerar gwamna a lokacin, a zaben da aka fafata sosai.

Source: Facebook
Adeleke ya lashe zaben 2022 ne a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma yanzu yana neman wa’adin mulki na biyu a zaben ranar Asabar a matsayin dan takarar jam’iyyar Accord.
4. Kananan hukumomi da rumfunan zabe
Jihar Osun na da kananan hukumomi 30 da aka raba zuwa yankunan sanata uku: Osun ta Gabas, Osun ta Tsakiya da Osun ta Yamma.
Haka kuma, jihar wadda ke a yankin Kudu maso Yammacin Najetiya na da rumfunan zabe 3,763 da ke cikin mazabu 332.
5. Gwamnan farko na Osun
Gwamnan farko na jihar shi ne Leo Ajiborisha, wani kanal na sojoji. Ya jagoranci jihar daga watan Agusta, 1991 zuwa watan Janairu, 1992, kafin ya mika mulki ga gwamnan farko da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.
6. Zababben gwamnan Osun na farko
Isiaka Adeleke shi ne gwamnan Osun na farko da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya. Ya yi mulki daga 1992 zuwa 1993.
Ya kasance daga ahalin Adeleke mai tasiri a siyasa, sannan shi ne babban yayan Ademola Adeleke, gwamnan jihar na yanzu.
7. Wurin ibadar Osun-Osogbo
Osun na daga cikin jihohin Najeriya da ke da wuraren tarihi da duniya ta amince da su, ciki har da Osun-Osogbo Sacred Grove, daya daga cikin wuraren tarihi guda biyu na Najeriya da UNESCO ta ayyana a matsayin wuraren tarihi na duniya.
Hukumar UNESCO ta amince da wurin a shekarar 2005, musamman sakamakon kokarin Susanne Wenger, mai zane dan asalin Austria da Najeriya, cewar The Punch.
Gandun dajin yana gefen kogin Osun, a wajen birnin Osogbo. A cikinsa akwai wuraren bauta, sassaka-sassaka da sauran ayyukan fasaha da aka kebe domin girmama Osun, ubangijiyar kogi, da sauran abubuwan bautar gargajiyar Yarbawa.
8. Ile-Ife da tarihin Yarbawa
Ile-Ife da ke jihar Osun na daga cikin wuraren da kabilar Yarbawa ke dauka a matsayin tushen wayewarsu da kuma wurin da aka fara samuwar bil’adama.
Birnin shi ne masarautar Ooni na Ife, daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya a kasar Yarbawa. Wasu daga cikin rukunin Yarbawan da ke jihar Osun sun hada da Ife, Ijesa da Igbomina.
9. Arzikin ma’adinan Osun
Jihar Osun na da arzikin ma’adinai daban-daban, daga cassiterite, columbite da tourmaline zuwa marble, musamman zinariya.
An gano zinariya a jihar a shekarar 1945, amma ba a fara hakar ta ba sai a cikin shekarun 1980.
10. Sana’o’in Osogbo
Birnin Osogbo da ke zaman babban birnin jihar, ya dade yana da masana’antar kere-kere da saka tufafi.
Daga cikin sana’o’in da aka fi sani akwai kera tufafin rini na gargajiya, wato adire, tare da sarrafa abinci da wasu kananan masana’antu.
11. Lokutan da aka gudanar da zabe a Osun

Kara karanta wannan
Gwamnan APC ya ƙaƙaba harajin N150m kan Bola Tinubu da wasu yan takara a zaben 2027
Zaben gwamnan da za a gudanar a ranar Asabar zai kasance karo na takwas da jihar Osun ta gudanar na zaben gwamna.
'Yan takara 2 sun janye a zaben Osun
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan takara guda biyu a zaben gwamnan jihar Osun sun hakura sun janye.
Yan takara biyu, Adebayo Simon Adewale na APM da Adedamola Adebayo na PDP, sun janye daga takarar tare da goyon bayan Gwamna Ademola Adeleke.
Asali: Legit.ng



