Babban Goro: Ficewar Ronaldo Ta Jawo Hukumar Kwallon Kafar Portugal Ta Samu Gagarumar Matsala

Babban Goro: Ficewar Ronaldo Ta Jawo Hukumar Kwallon Kafar Portugal Ta Samu Gagarumar Matsala

  • Rahotanni sun ce shafin Instagram na Hukumar Kwallon Portugal ya yi asarar mabiya sama da miliyan ɗaya cikin sa’o’i 24 bayan Ronaldo ya bar sansanin 'yan wasan kasar
  • Ronaldo ya bar sansanin ne Portugal bayan ganawa da sabon koci Jorge Jesus da shugaban hukumar ƙwallon ƙasar kan rashin buga wasa
  • Shahararren dan wasan ya bayyana cewa barinsa sansanin ba yana nufin ya yi ritaya daga buga wa Portugal wasa a matakin ƙasa da ƙasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Lisbon, Portugal - Shafin hukumar ƙwallon Portugal ya yi asarar mabiya Hukumar Kwallon Portugal (FPF) ta yi asarar sama da mabiya a shafukan sada zumunta biyo bayan abin da ya faru da Cristiano Ronaldo.

Hukumar FPF ta rasa sama da mabiya miliyan ɗaya a Instagram cikin sa’o’i 24 bayan Cristiano Ronaldo ya bar sansanin tawagar 'yan ƙasar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi maganar hana hawa a Kano bayan kalaman bangaren Aminu Ado

Ronaldo ya bar tawagar Portugal
Cristiano Ronaldo na jawabi ga manema labarai Hoto: Cristiano Ronaldo
Source: Facebook

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa shafin Instagram na Hukumar Kwallon Portugal yana da mabiya miliyan 24.9 ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026.

Sai dai zuwa yammacin Alhamis, adadin ya ragu zuwa kusan miliyan 23.8, lamarin da ya zo bayan ficewar Ronaldo daga sansanin tawagar.

Ronaldo ya bar sansanin bayan rashin buga wasa

Ficewar Ronaldo ta zo ne a lokacin da ake ta rade-radin rashin jituwa tsakaninsa da sabon kocin Portugal, Jorge Jesus.

Ronaldo, mai shekaru 41, yana cikin ’yan wasan da aka ajiye a benci yayin da Portugal ta doke Norway ranar Lahadi, kuma bai shiga wasan ba.

Kafin wasan da Portugal za ta kara da Denmark, Jesus ya kare matakinsa na ajiye Ronaldo a benci.

Ya ce shi ne kocin ƙungiyar kuma shi ne ke yanke shawarar ’yan wasan da za su buga wasa.

“Ni ne koci, kuma na gaya wa ɗan wasan cewa ba zai fara wasan ba. Na gaya masa zan kai shi benci, kuma idan na buƙace shi na tsawon mintuna 30, zai shiga wasa,” in ji Jesus.

Kara karanta wannan

Malamar addini ta fito ta gayawa Tinubu gaskiya kan halin da ake ciki a Najeriya

Ya ƙara da cewa ya ga wasan ta wata hanya daban, don haka bai saka Ronaldo ba.

“Ba Cristiano ba, ko wani ɗan wasa, babu wanda zai canza ra’ayina a matsayina na koci. Babu shi,” in ji shi.

Ronaldo ya sanar da barin sansanin

Sa’o’i kaɗan bayan taron manema labaran kocin, Ronaldo ya sanar a kafafen sada zumunta cewa ya yanke shawarar barin sansanin tawagar Portugal.

Ya ce ya tattauna da Jesus da kuma shugaban Hukumar Kwallon Portugal kafin ya ɗauki matakin.

Ronaldo ya ce zai bayyana wa al’ummar Portugal dalilan da suka sa ya bar sansanin a wani lokaci na gaba.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu yana da cikakken kishin tawagar ƙasar, tare da bayyana cewa ficewarsa daga sansanin ba yana nufin ya yi ritaya daga buga wa Portugal wasa a matakin ƙasa da ƙasa ba.

Magoya baya sun mayar da martani

Ronaldo shi ne ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin tawagar Portugal, inda ya ci ƙwallaye 138.

Ya kasance jigo a tawagar ƙasar sama da shekaru 20, lamarin da ya sa ficewarsa daga sansanin ya jawo martani cikin gaggawa daga magoya baya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bayyana halin Tinubu da ba zai dauka ba idan ya zama shugaban kaaa

Magoya bayan sun cika shafukan sada zumunta na Hukumar Kwallon Portugal da saƙonnin goyon baya ga kyaftin ɗin tawagar.

Ronaldo ya bar tawagar Portugal
Cristiano Ronaldo a sansanin tawagar 'yan wasan Portugal Hoto: Cristiano Ronaldo
Source: Facebook

Ronaldo ya yi maganar ritaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Cristiano Ronaldo, fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, ya yi magana kan lokacin da zai yi bankwana da buga kwallo. Cristiano

Ronaldo ya bayyana cewa kakar wasa ta 2026/2027 na iya zama shekararsa ta karshe yana taka kwallon kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng