Wata Sabuwa: An Bude Wa Tinubu Kofar da Zai Iya Raba Atiku da Mataimakinsa kafin Zaben 2027
- Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi ya ce cire tallafin fetur ba tare da matakan rage radadi ba ya ƙara wa ’yan Najeriya wahala
- Tsohon ministan sufurin ya ce zai janye takararsa ta mataimakin Atiku ya yi wa Tinubu kamfe idan farashin fetur ya koma N600 kowace lita
- Amaechi ya bayyana zaben shugaban kasa na 2027 a matsayin zabi tsakanin rayuwa da mutuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya kalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan hauhawar tsadar rayuwa.
Amaechi, wanda ya rike ministan sufuri a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya soki hanyar da Shugaba Tinubu ya bi wajen cire tallafin man fetur a Najeriya.

Source: Twitter
Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Rivers, ya bayyana haka ne ranar Juma’a yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Television ranar Juma'a.

Kara karanta wannan
Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji
Abokin takarar Atiku Abubakar ya ce cire tallafin man fetur ba tare da matakan rage radadin tasirinsa ba ya kara wa ’yan Najeriya wahala da kuncin rayuwa.
Amaechi ya kalubalanci Tinubu
Ya ce zai janye daga matsayin mataimakin dan takarar ahugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar tare da yi wa Tinubu kamfe idan farashin fetur ya koma N600 kowace lita a gobe Asabar.
“Kar ku damu da ra’ayina, zan je gidan mai da kaina gobe da safe domin ku gani. Idan farashin man fetur ya sauka zuwa N600, zan yi wa Shugaba Tinubu kamfe. Idan farashin fetur ya sauka zuwa N600 gobe, zan yi wa Shugaba Tinubu kamfe.
“Idan kuna da shakku, ku zo da kyamararku da safe, zan je gidan mai in sayi fetur. Idan farashin ya sauka zuwa wannan matakin, ni Chibuike Rotimi Amaechi zan janye a matsayin mataimakin Atiku, sannan in yi wa Shugaba Tinubu kamfe idan farashin ya sauka,” in ji Amaechi.
Amaechi ya raba zaben 2027 gida 2
Ya kuma bayyana zaben shugaban kasa na 2027 a matsayin zabi tsakanin rayuwa da mutuwa, yana mai cewa ’yan Najeriya suna da zabi guda daya idan suna son ci gaba da rayuwa.
A cewarsa, “Tinubu na wakiltar zabin mutuwa.”
Kalaman na Amaechi sun zo ne yayin da jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu ke shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027, inda yake takara a karkashin ADC tare da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Source: Twitter
Atiku da Amaechi sun yi alkawarin idan suka ci zaben 2027, za su kawo wani sabon tsarin tallafin man fetur domin saukak wa yan Najeriya wahalar da suka sha sakamakon tsadar rayuwa.
Amaechi ya cika naki kan gyara Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Rotimi Amaechi ya ba da wa'adin lokacin da da zai yi murabus idan Najeriya ba ta fara samun sauyi ba bayan ADC ta hau mulki a 2027.
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce zai yi murabus idan Najeriya ba ta sauya ba cikin shekara guda na mulkin ADC bayan sun yi nasara.
Ya ce dole ne a magance matsalolin tsaro, ilimi da tattalin arziki, yana mai cewa rage cin hanci zai samar da kudaden gudanar da wadannan fannoni.
Asali: Legit.ng

