Najeriya Ta Ƙulla Alaƙa da Sojojin Amurka yayin da Ta'addanci Ya Yi Ƙamari

Najeriya Ta Ƙulla Alaƙa da Sojojin Amurka yayin da Ta'addanci Ya Yi Ƙamari

  • Najeriya da Amurka sun amince da zurfafa haɗin gwiwar soji, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da inganta tsaron yankin Tafkin Chadi
  • Ministan Tsaro Christopher Musa ya bayyana fannoni da dama na haɗin gwiwa, ciki har da horo, musayar bayanan sirri da sa ido kan iyakoki
  • Manjo Janar Matthew Brown ya ce ayyukan sojin Amurka a Najeriya na wucin gadi ne, kuma sun fi mayar da hankali kan tallafa wa hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya sake tabbatar da aniyar Najeriya na zurfafa alaƙar soji da Amurka, musamman wajen yaƙi da ta’addanci.

Janar Musa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar Manjo Janar Matthew Brown, kwamandan Rundunar Sojin Amurka ta Afirka, SETAF-AF.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya ya yi kamari: Gwamnatin Tinubu ta nemo dabarun yaki da cutar

Najeriya ta sake kulla alakar soji da Amurka
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

A wata sanarwa da Leah Katung Babatunde, mai ba ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai, ta fitar, ta ce ziyarar ta duba shirye-shiryen tsaro na haɗin gwiwa, cewar Punch.

Musabbabin hadin guiwar sojojin Amurka da Najeriya

Ta ce ziyarar ta kuma yi nufin tsara ingantaccen tsarin haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu domin cimma sakamako mai kyau a nan gaba.

Musa ya yaba wa gwamnatin Amurka saboda ci gaba da haɗin gwiwar da take yi da Najeriya, yana mai cewa ayyukan tsaro a Arewa maso Gabas sun ƙarfafa gwiwar sojoji.

Ya ce haɗin gwiwar musamman a yankin Tafkin Chadi ya taimaka matuƙa wajen inganta ayyukan sojojin Najeriya da yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci.

Domin ƙara samun nasarori, ministan ya bayyana muhimman fannoni da Najeriya ke son ƙarfafa haɗin gwiwa da Amurka a kansu.

Daga cikin su akwai horar da jami’an rundunar musamman tare, musayar bayanan sirri, ƙarfafa ƙwarewa, inganta tsaron iyakoki da taimakon yaƙi da bama-bamai.

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Sauran fannoni sun haɗa da taimakon fasahar gano da kawar da bama-bamai da kuma zamanantar da kayayyakin more rayuwar tsaro domin ƙarfafa ƙarfin cikin gida.

A nasa jawabin, Manjo Janar Brown ya taya Najeriya murnar bikin ranar samun ’yancin kai tun da wuri, tare da nuna godiya ga dogon tarihin haɗin gwiwar sojojin ƙasashen biyu.

Ya bayyana cewa alaƙar sojin Najeriya da Amurka ta ci gaba da taimakawa wajen cimma manufofin tsaro da ƙasashen biyu suke da shi.

Brown ya kuma yaba da nasarorin ayyukan yaƙi da ta’addanci da aka gudanar kan ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ISIS a Afirka, tare da yaba wa sojojin da suka shiga ayyukan.

Dangane da ayyukan sojin Amurka a yankin bayan ficewar jami’an da suka kasance cikin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Musamman da ta yi aiki a Bauchi, Brown ya yi ƙarin bayani.

Ya ce ayyukan sojin Amurka a Najeriya na wucin gadi ne, kuma an fi mayar da hankali kan ƙarfafa hukumomin tsaro da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Brown ya bayyana alaƙar Najeriya da Amurka a matsayin muhimmiyar dangantaka da aka gina kan amincewa da juna.

Kara karanta wannan

Bayan nasarar Isa Ali Pantami, PDP ta kori manyan masu masa adawa 2 a Gombe

Ya ce babban dalilin ziyararsa shi ne fahimtar abubuwan da Najeriya ke buƙata a fannin tsaro kai tsaye, domin daidaita tallafin Amurka da ƙarfafa musayar bayanan sirri.

An tura bataliyar sojoji zuwa Zamfara

An ji cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sababbin bataliyoyin soji uku a jihar Zamfara domin ƙarfafa ayyukan tsaro da gaggauta tunkarar barazanar tsaro.

Sababbin bataliyoyin sun haɗa da 12 Infantry Battalion da aka kafa a Bakura, 23 Infantry Battalion a Kaura Namoda da 28 Infantry Battalion a Anka.

Rundunar ta ce sababbin rundunonin za su faɗaɗa ayyukanta tare da inganta tsaron yankunan da aka ba su alhakin kulawa da su a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.