Amaechi Ya Zargi Shugaban Kasa Tinubu da Hannu a Mutuwar Mahafiyarsa
- Rotimi Amaechi ya ce tsadar magunguna ta sa danginsa suka sha wahalar kula da mahaifiyarsa har ta rasu
- Yana zargin cire tallafin man fetur da tsadar rayuwa na jefa ‘yan Najeriya da yawa cikin matsalar samun lafiya
- Amaechi ya koka game da yadda magunguna suka yi tsada a yau sakamakon yawan shigo da su daga waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Rotimi Amaechi wanda ya yi minista a gwamnatin APC ya cigaba da koka wa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Abin har ya kai ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar na ADC yana alakanta manufofin gwamnati da rasa tsohuwarsa.

Source: UGC
Rotimi Amaechi ya yi maganar rasa gyatuma
Da aka yi hira da shi a tashar talabijin na Channels a ranar Juma’a, ya yi maganar abin da ya jawo mutuwar uwarsa.
Rotimi Amaechi ya yi kuka cewa magunguna sun yi tsada bayan shugaba Bola Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari a 2023.
Mista Amaechi yana ganin ba don tsadar da magunguna suka yi ba, da Dame Mary Odua Amaechi tana nan da rai yau.
Yana ganin manufofin gwamnati mai-ci suka hana marigayiya Mary Odua Amaechi ta yi tsawon rai, ta haura shekaru 90.
Ya ce wasu sun kai shekaru 90 ko 92 a duniya, bai ga dalilin da gyatumarsa ba za ta kai shekarun nan ba illa zuwan Tinubu.
Ya ce:
“Saboda tsare-tsare suna kashe mutane. Na rasa mahaifiya ta.”
Amaechi yana ce mutane suna kuka da Tinubu
‘Dan adawar ya ce abin bai tsaya a kan shi ba, mutane da yawa a Najeriya da kyar suke iya daukar dawainiyar asibiti.
An ji yadda magunguna suka kara kudi musamman bayan ficewar wasu manyan kamfanonin waje daga Najeriya bayan 2023.
‘Dan siyasar ya kafa hujja da alkuluman gwamnati, ya ce NBS sun tabbatar da yadda ake kawo magunguna daga ketare.
The Cable da ta saurari hirar, ta ji tsohon ministan yana cewa kafin Tinubu ya karbi mulkin kasar, lafiyar mahaifiyarsa kalau.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027
Amaechi ya ce lafiyar mahaifiyarsu kalau a da
Amaechi ya ce mahafiyar kalau ta ke, sai da aka yi canjin gwamnati a Najeriya ta fara rashin lafiya.
“Kafin Tinubu ya hau mulki, mahaifiyata tana cikin ƙoshin lafiya.
"Amma da Tinubu ya zo, sai aka samu matsalar sayen magungunan da take bukata. Na san da yawa daga cikinku ba za su yarda da wannan ba."
- Rotimi Amaechi
Ya cigaba da cewa:
“Amma abin da nake nufi shi ne, akwai mutane da dama da iyayensu suka mutu, su kuma yanzu suna cikin haɗarin rasa rayukansu, saboda manufofin Tinubu.
"Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce a zango na ƙarshe, mun kashe Naira biliyan 200 wajen shigo da magunguna. Kashi 40% na kayayyakin da ake amfani da su ana shigo da su ne daga ƙasashen waje.”

Source: Getty Images
'Alhaki yake bin El-Rufai a mulkin Tinubu'
A nan da aka samu labari cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani bai tausayin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Sanata Shehu Sani ya ce an rika yi wa doka rikon sakainar kashi ana watsi da umarnin kotu lokacin mulkin APC tsakanin 2015 da 2023 a Kaduna.
A cewar kwamred din, akwai malamai, ‘yan jarida, manyan mutane da El-Rufai a aka aika su kurkuku a Kaduna saboda sun yi adawa da shi kawai.
Asali: Legit.ng

