Atiku Ya Fusata Mutanen Tinubu, Sun Masa Raddi Mai Zafi

Atiku Ya Fusata Mutanen Tinubu, Sun Masa Raddi Mai Zafi

  • Kungiyar Tinubu Must Stay ta ce tana goyon bayan ci gaba da mulkin Shugaba Bola Tinubu, tana mai ambaton wasu bayanan tattalin arziki da shirye-shiryen gwamnati
  • Kungiyar ta kawo karuwar GDP, shirin rancen karatu na NELFUND da sauya motoci zuwa CNG cikin abubuwan da ta ce ya kamata a duba yayin muhawarar siyasar 2027
  • Hakan ya zo ne bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira da a kawo ƙarshen mulkin Tinubu a jawabinsa na ranar samun ’yancin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Tinubu Must Stay (TMS), wadda ta ce an kafa ta ne domin tallafa wa ci gaba da mulkin Shugaba Bola Tinubu, ta mayar da martani ga kiran wasu ’yan adawa na neman a sauya gwamnati a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Kungiyar ta lissafa wasu bayanan tattalin arziki da shirye-shiryen gwamnati da ta ce ya kamata a yi la’akari da su yayin tattaunawa kan tarihin gwamnatin Tinubu.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Facebook

A ranar Alhamis ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya kammala jawabinsa na ranar samun ’yancin kai da maimaita kalmar “Tinubu Must Go” sau uku.

Nasarorin da Tinubu ya kawo

Vanguard ta wallafa cewa jagoran kungiyar, brahim Uba ya ce ’yan ƙasa masu goyon bayan ci gaba da mulkin Tinubu da kuma son gabatar da hujjoji ne suka kafa kungiyar.

Kungiyar ta amince cewa sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur da sauye-sauyen kasuwar canjin kudi waje, sun jefa ƙarin nauyi kan jama'a.

Sai dai ta ce ya kamata a duba sakamakon da aka samu tare da matsalolin da har yanzu ba a warware su ba.

Ta ce tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaban kashi 4.43 cikin 100 a 2026, daga kashi 4.23 a 2025.

An ambaci NELFUND da 3MTT

TMS ta kuma ce zuwa watan Yuni, sama da ɗalibai miliyan 1.5 ne suka amfana da shirin rancen karatu na NELFUND, inda aka raba sama da Naira biliyan 282.

Kara karanta wannan

Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai

Bayanan NELFUND da aka fitar a watan Yuni sun nuna cewa ɗalibai daga cibiyoyin manyan makarantu 288 sun amfana da shirin.

Kungiyar ta kuma ambaci shirin 3MTT, inda ta ce sama da mutane 160,000 sun samu horo cikin rukuni uku, yayin da kusan miliyan 1.87 ke cikin wadanda suka yi rajista da jerin masu jiran shiga shirin.

A bangaren hauhawar farashin kayayyaki, kungiyar ta ce hauhawar farashin kaya ya tsaya kan kashi 15.39 cikin 100 a watan Agusta 2026, daga kashi 15.43 a watan Yuli.

Atiku Abubakar
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ma'aikata sun fara yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa ma’aikatan gwamnati sun shiga yajin aikin gargadi na kwana uku daga ranar 2 zuwa 4 ga Oktoba 2026.

Majalisar ta umarci shugabanninta na ƙasa da jihohi da su tattara ma’aikata domin shiga yajin aikin, wanda ya fara daga tsakar daren Juma’a zuwa Lahadi.

Hakan ya biyo bayan abin da majalisar ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin tarayya wajen magance buƙatun da ta gabatar wa Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng