Zaben Osun: Aikin Davido da Abubuwa 5 da Suka Taimaki Adeleke Ya Sake Doke APC

Zaben Osun: Aikin Davido da Abubuwa 5 da Suka Taimaki Adeleke Ya Sake Doke APC

Osun - An gudanar da zaben gwamna a jihar Osun an kammala, duniya ta shaida da nasarar jam’iyyar hamayya ta Accord.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Gwamna Ademola Nurudeen Jackson Adeleke ya yi galaba kan Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji da sauran ‘yan takara 13.

Kamar yadda malamin zabe, Farfesa Joshua Ogunwole ya sanar, Adeleke ya samu kuri’u 511,067 sai APC ta zo ta biyu da 444,815.

Adeleke
Gwamna Ademola Adeleke yana kada kuri'a a zaben Osun Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abubuwan da suka taimaka wa Ademola Adeleke

Legit Hausa ta yi duba da abubuwan da suka taimaki Mai girma gwamnan zai zarce a ofis, ana sa ran zai kara yin wasu shekaru hudu.

1. Albashi da hakkokin ma’aikata

A shekarun baya, ma’aikatan gwamnati a Osun sun samu kan su cikin halin wayyo Allah sakamakon bashi da ya yi wa jihar nauyi.

Gwamnatin Ademola Adeleke ta dage wajen ganin ba a wasa da hakkoki. Albashi da fanshon ma’aikata suna shigowa aljihu ka wata.

Kara karanta wannan

Mutane 3 daga gidan Adeleke da suka shiga siyasa kuma suka shahara a tarihi

Masu nazari sun ce wannan ya ba jam’iyyar Accrod gudunmuwa sosai musamman a yankin tsakiyar Osun da ake da ma’aikata da yawa.

2. Ayyukan da Adeleke ya yi

Jaridar Vanguard ta ce baya ga hakkokin ma’aikata, Ademola Adeleke ya kawo abubuwan more rayuwa a shekarun da ya yi a ofis.

Duk da’yan adawa suna zargin gwamnatinsa ta karkata ayyukan ne a garin Ede inda gwamna ya fito, wannan ya sa ya iya tallata kan shi.

3. Cin dunduniyar jam’iyyar APC

Akwai wasu ‘ya ‘yan APC da suka yaki jam’iyyar ta cikin-gida, ana zargin wadannan mutane da yi wa Mai girma Adeleke aiki ta bayan-fage.

Ko da Iyiola Omisore bai sauya-sheka ba, mutanen shi sun sauya-sheka zuwa jam’iyyar Accord saboda hana sa shiga takara a APC.

Magoya bayansa sun yi bakin kokarinsu wajen karya APC musamman a Ife Watsi da irinsu Olagunsoye Oyinlola shi ma bai taimaki APC ba.

4. Kokarin Davido

Rahoton ya ce fitaccen mawakin nan David Adeleke wanda ake kira Davido ya yi amfani da farin jininsa wajen tallata ‘dan uwan mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Adeleke: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da wanda ya lashe zaben gwamnan Osun

Davido ya yi ta amfani da shafukan sada zumunta yana ankarar da matasa game da yiwuwar APC ta yi amfani da karfin gwamnatin tarayya.

Har ranar zabe an ga yadda mawakin ya rika sakin bayanai a shafukan sada zumunta da nufin ganin APC ba ta kai labari a Osun ba.

5. Tallata Bola Tinubu

Duk da gudumuwar da Gwamnan Osun ya ba Atiku Abubakar a zaben 2023, wannan karo ya fito ya nuna yana tare da Bola Tinubu.

Akwai masu ra’ayin cewa marawa shugaban kasa baya da Adeleke zai yi a zaben 2027 ta sa fadar shugaban kasa ba ta yaki takarar shi ba.

Shugabannin APC sun hana gwamnan shigo wa jam’iyyar da ya bar PDP, amma wannan bai sa Tinubu ya yi wa Bola Oyebamiji aiki sosai ba.

6. Karya kashin bayan ADC

Jam’iyyar ADC ba ta tabuka abin kwarai a zaben Osun ba, wannan ya ja hankalin mutane irinsu Ja’afar Ja’afar da ya yi tsokaci a Facebook.

Dauke jiga-jigan siyasa irinsu Alhaji Moshood Adeoti da gwamna Adeleke ya yi daga ADC ya yi wa jam’iyyar Accord tasiri a zaben na 2026.

Kara karanta wannan

Jerin wadanda suka yi nasara da wasu da suka tafka asara a zaben Osun

Tashin Adeoti ya raunata gidan Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan da yanzu shi ne sakataren ADC da ta tashi da kuri’a 17, 000 a duk jihar.

Davido
Mawakin da ya tallata jam'iyyar Accord a Osun, Davido wajen wani wasa da yake yi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Yan zuri’ar Adeleke da suka yi suna a siyasa

Kun ji labarin yadda Raji Ayoola Adeleke ya fara siyasa tun zamanin Shehu Shagari kafin ‘ya ‘yansa biyu su zama gwamnoni a jihohinsu.

Shi ma Isiaka Adetunji Adeleke ya shiga siyasa, sannan shi ne gwamnan farko da aka zaba a jihar Osun a shekarar 1992 bayan kirkirar jihar.

Kanin Isiaka Adeleke kuma gwamnan yanzu, wanda shi ma ya zama sanata sannan daga bisani ya zama gwamna bayan nasarar a zaben 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng