Ganduje: Yadda aka Haifi Tinubu a Kano aka Raɗa Masa Suna Ashiru
- Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya gode wa ’yan Kannywood da suka nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu
- Ganduje ya bukaci ƙungiyar Triple-R ta tsaya kan adalci, gaskiya da haɗa kan al’umma yayin da take neman goyon bayan Tinubu a 2027
- Ya kuma yi kira da a ƙara zuba jari a masana’antar nishaɗin Najeriya ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da horar da matasa masu tasowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu haifaffen Kano ne, yayin da yake ganawa da tawagar ’yan Kannywood da ƙungiyar Triple-R.
Ganduje ya yi wannan bayani ne yayin wata ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da tawagar ’yan Kannywood da ke ƙarƙashin ƙungiyar Triple-R a Abuja.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanan da Abdullahi Ganduje ya yi ne a wani bidiyo da hadimin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya wallafa a X.
'Tinubu haifaffen Kano ne'
Rahoto ya nuna cewa Ganduje ya yaba wa ƙungiyar Rarara kan goyon bayan da take bai wa jam’iyyar APC da ’yan takararta a matakai daban-daban.
Yayin da yake jawabi ga tawagar, Ganduje ya ce:
“Tsaya ma dai a yi ta a kare, Asiwajun nan ai haifaffen Kano ne. Wannan Asiwajun da kuke ji Ashiru ne. Wannan Bola ɗin da kuke ji, Bala ne, wannan Ahmed kuma Amadu, wannan Tinubu kuma Tanimu ne.”
Tsohon gwamnan ya ce Triple-R na daga cikin ƙungiyoyin da suka fi nuna goyon bayan jam’iyyar APC a ƙasar nan.
Ya bukaci mambobinta su tsaya kan adalci, daidaito da haɗa kan al’umma yayin da suke gudanar da ayyukansu na siyasa.
Rarara ya goyi bayan Tinubu
Shugaban Triple-R, Dauda Kahutu Rarara, ya tabbatar da aniyar ƙungiyar ta goyi bayan sake zaɓen Tinubu da sauran ’yan takarar APC a Arewa a zaɓen 2027.
Rarara ya ce ƙwararrun masana’antar nishaɗi da ke Arewa sun mayar da hankali wajen haɗa kai domin tallafa wa Tinubu da ’yan takarar APC a yankin.
Ya ce goyon bayan ƙwararrun masana’antar fim da nishaɗi na Arewa ya samo asali ne daga abin da suka bayyana a matsayin ayyukan gwamnatin Tinubu.

Source: Facebook
Lawan Ahmad, da sakataren ƙungiyar, Ahmad Bifa, sun kuma bayyana aniyarsu ta yin aiki domin samun nasarar Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen da ke tafe.
Ga bayanin da Ganduje ya yi:
Tinubu ya yi watsi da tallafin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da yiwuwar komawa tsarin tallafin man fetur, yana mai cewa Najeriya ba za ta koma tsohon tsarin ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga ƴan Najeriya ranar Alhamis yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara tun shekarar 2023.
Shugaban ƙasar ya amince cewa sauye-sauyen sun yi wahala kuma tasirinsu ya kasance mai tsanani, amma ya ce janye su zai nufin komawa ga manufofin da ba su magance matsalolin tattalin arzikin Najeriya ba.
Asali: Legit.ng

